Man Utd na sa ran kammala cinikin Onana daga Inter Milan

Manchester United na sa ran kammala kula yarjejeniya da golan Inter Milan, Andre Onana.

Kocin United, Erik ten Hag na shirin warware matsalar da ke tattare da makomar golansu David de Gea.

Yarjejeniyar De Gea a Old Trafford ta kare ne a watan da ya wuce, kuma har yanzu kungiyar ba ta kulla sabuwar yarjejeniya ba da tsohon dan kwallon Sifaniya.

Onana mai shekaru 27, ya buga wasa takwas a cikin 24 da ba zura kwallo a ragarsa ba a kakar wasa mai zuwa a Italiya.

Dan Kamarun kuma ya fi kowanne mai tsaron raga haskakawa a gasar zakarun Turai a kakar wasan da ta wuce.

Ten Hag ne kocin Onana a kungiyar Ajax kafin dan kasar Holland din ya koma United.