Ƙungiyar Miyetti-Allah ta ce an mamaye wa makiyaya wuraren kiwo a Abuja

Hoton Shanu
Bayanan hoto, Hoton shanu
Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin Najeriya da mai alfarma Sarkin Musulmi, hadin gwiwa da kungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah sun yi wani zaman tattaunawa domin lalubo bakin zaren irin matsalolin da Fulani makiyaya suka ce suna fuskanta a babban birnin kasar, Abuja.

Makiyayan sun bayyana cewa an mamaye galibin wuraren da suke kiwo a birnin, sannan an watsar da su, inda ba su da makarantu da sauran abubuwan more rayuwa.

Gwamnatin Najeriyar dai ta yi wannan hadin gwiwar ne da shugabannin makiyayan inda suka tattauna yanayi ko halin da makiyayan suka samu kansu a manyan biranen Najeriya.

Galibin makiyayan sun bayyana cewa wuraren kiwon dabbobi na ci gaba da kankancewa, sakamakon yadda ayyukan gina gidaje da kamfanoni suka mamaye wuraren da ya dace su zama wurin kiwo ko burtali.

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar na daga cikin wadanda suka jagoranci zaman tattaunawar.

Kuma ya shaida wa mahalarta taron cewa za su tsaya tsayin-daka wajen ganin an samu nasarar zaman lafiya.

Sannan ya ce zai tattauna da ministan babban birnin Najeriyar don shaida masa matsalolin makiyayan.

''Fatanmu shi ne a kira shi minista, kuma a kira ku, a ji matsalolinku, kuma idan Allah Ya yarda za a shawo kan matsalar,'' in ji shi.

A nasa bangaren shugaban kungiyar Miyetti-Allah ta Najeriya Baba Usman Nganzarma, ya ce magance wannan matsala ta makiyaya a Abuja, zai share masu hawayensu, ba ma a Abuja kadai ba, har ma da sassan kasar baki daya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shi ma ministan ma'aikatar kula da kiwo ta Najeriyar Dakta Mukhtar Idi Maiha, ya ce matsalar da ake samu ita ce akwai wasu mutane da ba makiyaya ba da suka mamaye wuraren da makiyayan ke kiwo musamman a Kawu, da Karshi da sauransu.

Kuma suna zaune, don haka za a samar da jami'an tsaro da za su zauna a wurin don a kare masu dukiyarsu.

A cewarsa: ''Za mu gina masu asibitoci, da burtsatse da kududdufai ta yadda za a iya yin noman rani.

Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin fito da taswirar da za ta yi amfani da ita wajen samar da mafita.

Kazalika, makiyayan na korafin yadda yaransu ba sa samun ilimi kamar sauran takwarorinsu.

Kuma suna korafin cewa gwamnati ta watsar da su ba tare da samar musu abubuwan more rayuwa ba - kamar wutar lantarki da asibitoci da ruwan sha da sauransu.

Wasu daga cikin shugabannin makiyayan sun bayyana gamsuwa tare da cewa taron na da muhimmanci domin a duba halin da suke ciki.

Ana ganin wannan tattaunawa da ta hada bangarorin sarakuna da gwamnatin Najeriyar da su kansu makiyaya na iya zama zakaran-gwajin-dafi wajen magance damuwarsu.

Wakilan gwamnatin kasar da Mai Alfarma Sarkin Musulmi sun dauki alkawarin isar da sakon ga gwamnatin Najeriya domin duba bukatun makiyayan.