Mece ce lalurar tsananin rashin mayar da hankali ta 'ADHD' wadda mata suka fi fama da ita?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Merve Kara Kaska and Anya Dorodeyko
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 7
"Ina da kokari a makaranta, amma na fita daban daga cikin kawayena. Ina matukar wahala wajen mayar da hankali a lokacin daukan darrusa kuma ina shan wahala wajen gane tambayoyin jarrabawa," a cewar Ayse, 'yar shekara 38 daga Turkiyya, wadda wahalar da ta sha a rayuwa ya sa ta fahimci tana da lalurar rashin nastuwa da ake kira ADHD a Turance.
Ta na daya daga cikin mata da dama a duniya da aka gano sun sake kamuwa da wannan lalurar bayan girma.
Ayse na karatun digirin digirgir a fannin raya birane a wata jami'a da ke Burtaniya, lokacin da ta fahimci ba ta iya mayar da hankali, sannan tana jin matukar gajiya da yanayin nata."
"Na sha fitowa a makare, ko na saba alkawari, ko na manta ranar dana waye gari ko na manta inda na ajiye jakata ko makulin gida," a cewarta.
Yanayin da ta tsinci kanta ya kai ga ta rasa gurbin karatun da gwamnati ta dauki nauyin karatunta a Burtanita, haka nan ta koma Turkiyya da dimbin basuka. Sai dai fahimtar cewa tana fama da larurar rashin natsuwa ya taimaki rayuwarta.
"A karo na farko a rayuwata, Ina ji na a matsayin babba da ke iya yanke hukunci ko tafiyar da rayuwata da tunani," a cewar Ayse idan ta tuna baya.
Mece ce cutar ADHD?
Lalurar tsananin rashin mayar da hankali da ake kira ADHD a Turance, lalura ce da ke da alaka da ƙwaƙwalwa. Alamominta sun hada da kirinki da rashin samun natsuwa. Wata alama kuma ta ADHD, ta hada da tsananin rashin daukan abu ko ana wa mutum magana amma hankalinsa ya gushe.
Milyoyin mutane na dauke da wannan larura, amma ba su sani ba.
Tana daga cikin lalurori da yara ke fama da ita a duniya kuma tana da alaka da kiriniyar yara maza, sai dai sake fahimtar masu dauke da larurar na sake fitowa a kowanne rukuni na shekaru da jinsi.
Kwararru na cewa ana samun karin manyan mutane da ke fahimtar suna fama da wannan matsala, musamman mata, irin su Ayse, da ba a taba kai su wurin likita ba har suka girma.
Dr Ulrich Muller-Sedgwick, kwararre ne a lalurar ADHD da ke asibitin koyarwa na kwalajen Royal da ke Burtaniya daga sashen masu lalurar kwakwalwa, ya ce gano wannan matsala tun da wuri na taimakawa wajen saita rayuwar mutum.
"Na sha ganin iyaye mata da ake kai su Kotu ana raba su da 'ya'yansu saboda ba sa iya bai wa yaran kulawa. Galibi idan aka bincika ana fahimtar suna dauke da wannan lalura ta ADHD, sai ka ga an ba su kulawa kuma su zauna da yaransu lfy," a cewarsa.
Mene ne alamomin lalurar ADHD a manya?
Alamomin lalurar ADHD a manyan ya bambanta da wanda ake gani a yara. Bayanan da cibiyar kula da lafiyar kwakwalwa ta Amurka ta fitar, na cewa a galibin lokuta alamomin ADHD a manyan sun kunshi:
- Yawan gushewar hankali
- Rashin kimtsa kai da tunanin abin da babu shi
- Rashin mutunta ko aiki da lokaci
- Manta abubuwa ko ayyuka da ya kamata a aiwatar a rana
- Katse mutane ko takura musu da hirarraki
- Matsala wajen mayar da hankali a kan ayyuka ko kammalasu
- Rashin fahimta ko sabawa da wani yanayi
- Yanke hukunci nan take ba tare da dogon nazari ba
Ga manya da ke da wannan alamomin larurar ADHD ya kan yi tsanani, sannan yana shafar harkokinsu na rayuwar yau da kullum.
Ya girmar lalurar ta fannin jinsi?
An kiyasta cewa a duk maza hudu ana samun mace guda da ke fama da wannan lalura, sannan a ciki manya ana samun raguwa.
Chiara Servili, jami'ar lafiyar kwakwalwa a hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce ana samun karuwar hujojji da ke nuna gano lalurar ya bambanta, saboda kowanne alama kan bambanta da na juna tsakanin mata".

Asalin hoton, Getty Images
Kwararru da dama sun ce alamomin ADHD sun fi nunawa ga iyaye da malamai a maza kan mata.
"Yara mata da ke dauke da ADHD ba su fiya hayaniya a aji ba, kuma baa saurin ganosu. Amma yara maza da ke da wannan larura ba sa zama wuri guda, suna yawaita guje-guje da rigima da haifar da matsaloli, don haka a makaranta ana saurin gane su da sanar da iyayansu, a cewar Dakta Muller-Sedgwick.
"Ina ganin mata da yara mata na da wani yanayi na boye abu - wanda fahimtar halayensu ko yanayi na da dan wahala," a cewarsa.
Yanayin al'umma da al'adu da bambanci jinsu na taka rawa wajen jinkiri ko saurin fahimtar 'ya'ya mata, a cewa Chiara Servili ta WHO.
Ta kuma kara da cewa ana bukatar a sake bincike kan kwayoyin halitta, sinadaran jiki da balaga wajen fahimta ire-iren alamomin lalurar ADHD.
Me ya sa sai mata sun girma ake gane suna dauke da lalurar?
Bincike da dama sun nuna cewa a rukunnin manya gano larurar ADHD a kowanne jinsu akwai kamanceceniya.
Wani babban dalili shi ne mata sun fi zuwa asibiti domin duba lafiyarsu idan aka kwatanta da maza, a cewar Dakta Ali Kandeger, likitan kwakwala a Turkiyya, inda mutane da dama ke fama da wannan larura, har ake cewa tafi yawa a kasar idan aka kwatanta da sauran kasashen duniya.
Dr Didem Suculluoglu Dikici, ita ma a Turkiyya, ta ce a shekarun baya-bayanan ta samu adadi mai yawa na mata da ke dauke da wannan larura.
Ta ce mutane na zuwa wurinta neman taimako saboda matsaloli na damuwa da yawan gajiya ba tare da sun fahimci larurar da ke damunsu ba. A cikinsu akwai mata, "da ke manyan ayyuka, wadanda ke da kwarewa kuma ke da karfin iko".
Amma saboda su kai wani mataki a rayuwa na cigaba suna yawaita neman taimako da amfani da dabaru da na'urori wajen cimma burinsu, a cewarta.

Asalin hoton, Getty Images
Ta yi bayyanin cewa cikin matan da take dubawa akwai rukunnin matan da suke cikin shekarunsu na 40, da ke fama da matsala na daukewar jinin al'ada ko rashin daidaitar al'ada.
"Alamomin ba wai sun tsaya kan bangare guda ba ne ko yawaita zafin jiki, wasu lokutan sukan bijiro da abubuwan da baa yi tsanmani ba," a cewarta.
Lalurar ADHD na karuwa?
Adadin mutanen da ake ganowa na fama da wannan lalura na karuwa a kasashe da dama a shekarun baya-bayanan.
A misali, a Ingila adadin mutanen da ake bai wa magunguna ADHD sun karu a shekaru 10 da suka gabata.
A Amurka, alkaluma sun nuna a 2022 an samu karin yara miliyan daya 'yan shekara 3 zuwa 17 da a wani yanayi na rayuwarsu sun yi fama da wannan larura, idan aka kwatanta da 2016.
Wani bincike da aka gudanar a 2023 ya nuna raguwa sannan aka samu karuwar yawan mutanen da ake bai wa magunguna ADHD a lokacin annobar korona.
ADHD na da alaka da kallon waya ko talabijin?
Yayin da ake samun karuwar fasahohin zamani da kallace-kallace da yara da manya ke yi a kafofin intanet, mutane na yawan diga ayar tambaya kan alaka tsakanin kallon sikirin da ADHD.
"Akwai binciken da aka yi kan yara da ke kallon sikirin, masu lalurar da marasa lalura, kuma an gano cewa masu lalurar ADHD sun fi bata lokaci wajen kalle-kalle na wayoyi da sauran na'urori ko kwamfutar da ake kallo," a cewar Dr Muller-Sedgwick.

Asalin hoton, Getty Images
Kafofin sada zumunta da wasannin da ake yi na bidiyo a kamfutoci na dauke da 'dopamine flashes' wanda masu laurar ADHD ke tsananin bukata, saboda 'dopamine' na taimakawa kwakwalwa a wajen aiki, a cewarsa.
Bincike ya nuna cewa bata lokaci sosai a kan wayoyi ko sikirin na kara ta'azzara matsalar ga yara masu dauke da ADHD, sai dai kuma fahimtar ko shi kansa sikirin din na haifar da ADHD abu ne da har yanzu babu hujja, a cewar Dakta Muller-Sedgwick.
Ya ake warkar da ADHD?
Kafin gane mutum na dauke da ADHD, dole sai an nazarci rayuwar mara lafiya daki-daki, sannan likitoci za su kokarin fahimtar wasu alamomi tun daga yaranta.
Misali, a Burtaniya likitoci na bada shawarar sauya wasu dabi'u ko abubuwa na rayuwa ko muhalli, kafin a kai ga soma bada magunguna.
Magunguna dama sun handa da stimulants, da amphetamines ko methylphenidates, da ke rage alamomin ADHD ta hanyar kara yawan sinadarai da kwakwalwa ke bukata. Sai dai magunguna na zame wa mutane kullum sai an sha muddin ba a yi amfani da su yadda ya kamata ba.

Asalin hoton, Getty Images
Ga wadanda ba sa son magunguna likita da akwai tsarin duba lafiyar da ake musu amfani da shi, da suka hada da nazartar lalurar sosai da nacewa wasu tsare-tsare da ake ganin za su takaita larurar.
Dr Kandeger ya kuma ce akwai wasu yanayi na motsa jiki da abubuwan da ke taimakwa jiki da lafiyar da ake son a mayar da hankali.
"Misali, idan mutum zai ci abinci, sai ya yi kokari ya ajiye komai ya kauracewa kallo. Ko kuma idan mutum na kallo, sai ya yi kallon kadai. Sannan wani lokaci mutum ya dan tattaka, wasu lokutan kuma a huta kada a yi komai", a cewarsa.











