Maryam Sanda da sauran waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa bayan sake nazari

Asalin hoton, @aonanuga1956/X
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya rage yawan mutanen da ya yi wa afuwa a watan Okotoba daga 175 zuwa 116 ciki har da Maryam Sanda wadda take zaman jiran hukuncin kisa bisa laifin kisan maigidanta.
Wannan na ɗauke a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Tinubu kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar.
A farkon watan Oktoba nan ne dai shugaba Tinubu ya yi wa wasu mutum 175 afuwa da suka haɗa da matattu da masu rai.
Sai dai kuma shugaban ya fuskanci suka daga ɓangarori da dama na ƙasar, wani abun da ake ganin shi ya sa gwamnatin ta fito ta ce za ta sake waiwayar jerin sunayen.
To sai dai sabon jerin sunayen mutanen ya ƙunshi mutum 116, inda aka kasa su gida uku waɗanda aka yi wa afuwa da waɗanda aka yi wa sassauci da kuma waɗanda aka yi afuwa amma ba a wanke su ba.
Mutanen da aka yafe mawa tare da wanke su

Su ne mutum 15 da aka yafewa laifin da suka yi sannan kuma aka wanke su daga laifin wanda hakan ke nufin ba za a taɓa alaƙanta su da laifin ba sannan idan akwai wasu haƙƙoƙinsu da aka hana su sakamakon aikata laifin to yanzu za a ba su haƙƙoƙin nasu.
- Mrs Anastasia Daniel Nwaobia
- Barrister Hussaini Alhaji Umar
- Ayinla Saadu Alanamu
- Hon Farouk Lawan
- Herbert Macaulay
- Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa
- Ken Saro Wiwa
- Saturday Dobee
- Nordu Eawo
- Daniel Gbooko
- Paul Levera
- Felix Nuale
- Baribor Bera
- Barinem Kiobel
- John Kpuine
Mutanen da ake sauya wa hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai
- 1. Emmanuel Baba
- 2. Abubakar Usman
- 3. Khalifa Umar
- 4. Mohammed Umar
Waɗanda aka yafe mawa amma tabon zai bi su
- Oroka Michael Chibueze
- Adesanya Olufemi Paul
- Daniel Bodunwa
- Hamza Abubakar
- Buhari Sani
- Mohammed Musa
- Maharazu Abubakar
- Ibrahim Yusuf
- Saad Ahmed Madaki
- Kofur Michael Bawa
- Richard Ayuba
- Adam Abubakar
- Emmanuel Yusuf
- Chinedu Stanley
- Johny Ntheru Udor
Mutanen da aka yi wa sassauci
Sunan Maryam Sanda shi ne na 86 a cikin jerin sunayen mutanen da aka sassauta musu hukuncin da aka yi musu.
Maryam Sanda wadda aka yanke mata hukuncin kisa yanzu haka ta samu sassauci inda aka mayar mata da hukuncin zuwa zaman gidan kaso na shekaru 12.
Maryam wadda aka ɗaure ta a shekarar 2020 yanzu haka ta yi shekaru shida, inda ake sa ran nan da shekaru shida za ta shaƙi iskar ƴanci.
Jerin waɗanda aka yi wa sassaucin su ne:
- Yusuf Owolabi - ɗaurin rai da rai zuwa ɗaurin shekara 15
- Ifeanyi Eze - ɗaurin rai da rai zuwa ɗaurin shekara 15
- Malam Ibrahim Sulaiman - ɗaurin rai da rai zuwa ɗaurin shekara 15
- Patrick Mensah - ɗaurin shekara 17 zuwa ɗaurin shekara 13
- Obi Edwin Chukwu - ɗaurin shekara 15 zuwa ɗaurin shekara 12
- Tunde Balogun - ɗaurin shekara 15 zuwa ɗaurin shekara 12
- Lima Pereira Erick Diego - ɗaurin shekara 15 zuwa ɗaurin shekara 12
- Uchegbu Emeka Michael - ɗaurin shekara 15 zuwa ɗaurin shekara 12
- Salawu Adebayo Samsudeen - ɗaurin shekara 15 zuwa ɗaurin shekara 12
- Napolo Osariemen - ɗaurin shekara 15 zuwa ɗaurin shekara 12
- Odeyemi Omolara - ɗaurin shekara 25 zuwa ɗaurin shekara 18
- Dias Santos Marela Christian- ɗaurin shekara 15 zuwa ɗaurin shekara 12
- Alhaji Ibrahim Hameed- ɗaurin shekara 7 zuwa ɗaurin shekara
- Isaac Joshua - ɗaurin shekara 10 zuwa ɗaurin shekara 7
- Aishat Kehinde - ɗaurin shekara 5 zuwa ɗaurin shekara 4
- Helen Solomon- ɗaurin shekara 5 zuwa ɗaurin shekara 3
- Okoye Tochukwu - ɗaurin shekara 6 zuwa ɗaurin shekara 3
- Ugwueze Paul - ɗaurin shekara 6 zuwa ɗaurin shekara 3
- Mustapha Ahmed - ɗaurin shekara 7 zuwa ɗaurin shekara 5
- Abubakar Mamman - ɗaurin shekara 10 zuwa ɗaurin shekara 7
- Muhammed Bello Musa - ɗaurin shekara 10 zuwa ɗaurin shekara 7
- Nnamdi Anene- ɗaurin rai da rai zuwa ɗaurin shekara 20
- Alhaji Abubakar Tanko- ɗaurin shekara 30 zuwa ɗaurin shekara 20
- Innocent Brown Idiong- ɗaurin shekara 10 zuwa ɗaurin shekara 6
- Iniobong Imaeyen Nuikidem - ɗaurin shekara 7 zuwa ɗaurin shekara 5
- Ada Audu - ɗaurin shekara 7 zuwa ɗaurin shekara 4
- Buka Adamu - ɗaurin shekara 20 zuwa ɗaurin shekara 9
- Chukwukelu Sunday Calistus- ɗaurin rai da rai zuwa ɗaurin shekara 20
- Markus Yusuf - ɗaurin shekara 13 zuwa ɗaurin shekara 8
- Samson Ajayi - ɗaurin shekara 15 zuwa ɗaurin shekara 10
- Rakiya Beida - ɗaurin shekara 7 zuwa ɗaurin shekara 5
- Umanah Ekaette Umanah - ɗaurin shekara 10 zuwa ɗaurin shekara 7
- Utom Obong Thompson Udoaka - ɗaurin shekara 7 zuwa ɗaurin shekara 6
- Jude Saka Ebaragha - ɗaurin shekara 12 zuwa ɗaurin shekara 8
- Frank InsortAbaka - ɗaurin shekara 12 zuwa ɗaurin shekara 8
- Sluna Alolo- ɗaurin shekara 12 zuwa ɗaurin shekara 8
- David Akinseye - ɗaurin shekara 12 zuwa ɗaurin shekara 8
Dalilin lashe amai
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sanarwar da Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ta ce shugaba Tinubu ya sake waiwayar jerin sunayen mutanen da aka yi wa afuwar ne sakamakon tuntuɓar Majalsiar Ƙasa da kuma ra'ayoyin ƴan Najeriya kan batun.
"Shugaban ƙasa ya yi umarnin a sake bibiyar da waiwayen jerin sunayen waɗanda aka yi wa afuwar da farko...inda aka goge sunayen mutanen da suka aikata manyan laifuka kamar garkuwa da mutane da safarar ƙwaya da safarar bil'adama da damfara da mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba....sannan kuma aka rage hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai ga wasu waɗanda aka yafewa a farko."
Sanarwar ta ƙara da cewa ɗaukar matakin ya zama dole ne bisa la'akari da girman laifukan da alaƙarsu da matsalar tsaro da ƙasar ke ciki da kuma nuna damuwa da halin da ƴan uwa da iyalan wadanda masu laifin suka saɓawa.
"Shi adalci abu ne mai fuska uku - Wanda ya aikata laifi da wanda aka yi wa laifin da kuma ƙasa ko kuma al'umma saboda haka ne ma aka yi wani waiwayen," in ji sanarwar.










