'Yadda na ji bayan 'yan bindigar Zamfara sun saki 'ya'yana mata biyar'

Mahaifiyar 'yan matan nan biyar da 'yan bindiga suka sako a Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta bayyana irin mawuyacin halin da 'ya'yan nata suka shiga lokacin da suke tsare.
'Yan mata, wadanda suka kwashe wata biyar a hannun 'yan fashin daji, 'ya'ya ne ga wani tsohon Babban Akanta a jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Bello Furfuri.
Labarin sace su ya ja hankalin 'yan Najeriya, musamman a arewacin kasar, bayan da 'yan bindigar suka fitar da wani bidiyonsu rataye da manyan bindigogi da jigidar harsasai, inda suka yi barazanar ɓatar da su ko kuma su mayar da su mayaƙansu, matuƙar ba a kai kuɗin fansa ba.
A ranar Litinin ne aka sako 'yan matan bayan da wasu rahotanni suka nuna sau uku mahaifinsu yana biyan kuɗin fansa.
"Ba a keta haddinsu ba"

Asalin hoton, Gwamnatin Zamfara
Mahaifiyar 'yan matan, Hajiya Hadiza Abubakar, ta shaida wa BBC cewa sun yi matukar murna da aka sako 'ya'yan nata.
"Na yi farin ciki sosai [bisa sakinsu], na yi wa Allah godiya. Sai dai akwai wasu 'yan wahalhalu da ke damunsu.
"Farin cikin da na yi shi ne da suka tabbatar mini cewa ba a keta haddinsu ba na 'ya mace.
"Sai dai cije-cijen sauro da sauran wahalhalu da suka dame su," in ji ta.
End of Wasu labaran da za ku so karantawa
Ta kara da cewa babban abin da ya fi tayar musu da hankali bayan kama 'ya'yanta shi ne yadda aka nuna su a bidiyo rataye da manyan bindigogi, tana mai cewa "na yi baƙin ciki sosai na miƙa wa Allah kukana."
Hajiya Hadiza ta ce tana haɗuwa da 'ya'yanta suka rungume juna suna koke-koke ba tare da cewa uffan ba, ko da yake daga bisani "an ce gwamna [Mohammed Matawalle] yana nemansu" don haka ta kyale su, su tafi wurinsa.
Sai dai ta ce sun shaida mata cewa sau biyar kawai aka bar su, suka yi wanka cikin wata biyar, "shi ma ba tare da sabulu ba."
"Sun shaida mini cewa abin da ya fi tayar musu da hankali shi ne barazanar da 'yan fashin dajin suka riƙa yi musu cewa ba za su dawo gida ba - za su rike su a hannunsu matsawar ba a kara kawo musu kuɗi.
Babu wanda ya ba mu ko sisi, mu muka sayar da kaddarorin mai gidana da 'yan uwa da abokan arziki har Allah ya sa aka karbo su", a cewar Hajiya Hadiza.











