'Yadda matata ta haihu a wajen masu satar mutane a Zamfara'

Mata mai juna biyu ta haihu a hannun 'yan bindiga

Wani magidanci da matsarsa ta haihu a hannun ƴan bindiga ya ce babu abin da zai ce sai addu'ar Allah ya kuɓutar da ita, domin a yanzu ƙaddara kawai suka runguma.

Magidancin mai suna Kwamared Sanusi Isa, mazaunin wajen Gusau ne babban birnin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

Ya ce matarsa mai juna biyu da aka sace a farkon makon nan ta haifi ‘ya mace a hannun masu garkuwa da ita.

Kwamared Sanusi Isa Gusau ya shaida wa BBC cewa matar ta haihu ne kasa da kwana daya da sace ta kuma har yanzu ita da jaririyar da ta haifa na hannu masu garkuwar da su.

Yadda al'amarin ya faru

Kwamared Sanusi mazaunin birnin Zamfara ya ce a daren ranar Litinin wasu mutane suka je gidansa, ya jiyo suna ta bugun kofa har suka ɓallata bayan shafe minti 30.

Kafin Allah ya ba su ikon shiga gidan sai ya yi sauri ya ɓuya a cikin banɗaki, da suka shigo gidan sai suka iske matarsa kawai mai tsohon ciki, wadda ba ta iya ɓuya ba saboda yanayin da take ciki, a cewarsa.

Wannan ya ba su sa'ar tafiya da ita, kuma ba su sake jin wani labari ba, har sai zuwa yammacin Talata da ta kira su da wayarta da aka sace ta, take sanar da cewa ta haifi ɗiya mace, in ji Sunusi.

Mijin ya ce tun sannan dai ba su sake jin komai ba, sai dai ya ce duk da cewa har yanzu babu wani labari, jami'an tsaro na iya ƙoƙarinsu domin ganin sun ceto ta.

Sannan ya ce ɓangaren masu garkuwa da ita ba su kira sun nemi wani abu ba.

Sace-sacen mutane a Najeriya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yanayin da Kwamared Sanusi ya tsinci kansa kusan iri guda ne da wanda ake yawaita samun iyalai da 'yan uwa a ciki da ke koke da roƙon gwamnati ta taimaka wajen sako mutanensu da ke hannun 'yan bindiga.

Matar Kwarade Sanusi na ɗaya daga cikin ire-iren mata da galibi ake wayar gari da labarin garkuwa da su ko a gidajensu ko hanyar balaguro ko zuwa wajen neman abincinsu.

Ɗaruruwan 'yan Najeriya sun tsinci kansu a wannan yanayi tun daga lokacin da satar mutane domin neman kuɗin fansa ya zama ruwan dare musamman a yankunan arewacin ƙasar, ba ga birnin ba ko ƙauyuka.

A galibin lokuta gwamnati ko jami'an tsaro kan kuɓutar da wasu, wasu kuma 'yan uwa a iyalai ke biya musu kuɗin fansa.

Akwai kuma waɗanda ke rasa rayukansu da waɗanda har yanzu ba a sake jin duriyarsu ba.

Gwamnatin Najeriya na cewa tana ɗaukar matakai domin ganin an daƙile wannan matsalar tsaro, sai dai da alama a ko da yaushe hannun agogo na sake komawa baya.

Garkuwa da mutane na baya-bayan nan da ya girgiza 'yan kasa kuma ake kan jimami ita ce ta fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna da har yanzu akwai sauran mutane sama da 50 a hannun 'yan bindiga.

Sannan akwai ɗaliban makarantu da su ma ake dakon ganin ranar da sa su shaƙi iskar numfashi.