Yadda tsadar rayuwa ta tilastawa likitocin Najeriya ficewa zuwa ƙasashen waje

Asalin hoton, Getty Images
Najeriya dai ta kasance ƙasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, sannan ta na shirin fara fitar da sabbin takardun kuɗi karon farko cikin sama da shekaru 20.
Matakin dai wani yunkuri ne na sake dawo da kwarin gwiwa a kan kuɗin naira, da ke fuskantar matsin lamba.
Yayin da hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 20, mutane na ta kokawa kan yanayin tsadar rayuwa.
Hakan kuma ya sanya kwararrun matasa da suka ƙware a bangarori da dama barin ƙasar a cikin shekarun nan.
"Ka yi tunanin zuwa sayar da kayayyaki wata rana, kwatsam sai ka samu komai ya ninka har sau uku, ya mutum zai yi? Kana da iyali a gida. Me za ka fasa saya?" Oroma Cookey ta faɗa min a tattaunawa ta intanet da muka yi.
Mai zanen kayan kwalliyar ta bar babban birnin Najeriya, Legas, tare da iyalanta shekara guda da ta wuce zuwa babban birnin Birtaniya, Landan.
Mijinta wanda kuma ya kasance abokin kasuwancinta mai suna Osione, wanda mai zane ne, an ba shi bizar kwararre ta duniya, wanda ke bai wa shugabanni a fannin ilimi, fasaha da al'adu, da fasahar dijital yin aiki a Birtaniya.
Ta ce akwai wahala matuka wajen samar wa iyalanta rayuwa mai inganci a Legas.
"Kuɗin mu na sayo mana ƙananan abubuwa, ba mu iya biyan kuɗaɗen mu, ba mu iya yin abubuwan da muka saba yi."
Oroma ta yi karatun a bangaren shari’a a Jami’ar Northumbria ta kasar Birtaniya, sannanta koma Najeriya kusan shekaru 20 da suka gabata, inda take da zimmar son yin amfani da karatunta wajen ci gaban ƙasarta.
Oroma tare da Osione, sun kirkiro da This Is Us, wani samfurin salo da salon rayuwa mai ɗorewa wanda ke amfani da kayan gida da masu sana'a, wanda ya kunshi auduga da ake nomawa da kuma rini a arewacin Najeriya.
Da farko, matsalar tsadar rayuwa ba ta shafe su ba.
"Saboda muna da abin da muka dogara da shi a Najeriya, abubuwa ba su yi mana muni ba kamar sauran mutane," in ji Oroma.
"Don haka lokacin da kowa ke ƙara farashinsa, mun tsallake karin saboda muna da ɗan abin dogaro."

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai kwastomominsu na Najeriya na wahala wajen sayan kayayyaki kamar sutura - musamman lokacin da abinci ya kai kashi 63 na abin da suke kashewa.
Wannan yana nufin lokacin da farashin abinci ya tashi, mutane na samun ƙarancin kuɗin shiga.
Oroma ta ce abin ba shi da ɗaɗi ga matasan Najeriya. “Ina magana da mahaifiyata, wani abu da na gane shi ne, lokacin da suke matasa, abubuwa sun yi musu sauƙi. Suna iya sayan gidaje da motoci.
"Koyaushe ina jin kamar: 'Me ke faruwa da ni?' Ina kasawa ne saboda ba zan iya yin duk abubuwan da mahaifiyata take yi ba, amma na gane cewa ƙasar ba ta yi min abin da ya kamata ba." Ba ita kaɗai ta ji haka ba. Najeriya na fuskantar ɗimbin masu hijira mafi muni cikin shekaru.
Yana da wuya a samu ƙididdiga mai inganci, amma adadin 'yan Najeriya da aka bai wa bizar aiki a Birtaniya ya ruɓanya sau huɗu tun daga 2019. Kuma an bai wa ɗaliban Najeriya ƙarin biza wanda ya kai kashi 700.
Akwai dogayen layuka a wajen cibiyoyin kula da shige da fice da kuma ofisoshin jakadanci a kullum, kuma kowa a nan ya san wanda zai tafi ko yana kokarin komawa kasar waje.
Kalmar “japa” wacce ke nufin “balaguro” a cikin harshen Yarbanci, ya zama abin da ya fi shahara da tattaunawa a Intanet da kuma a gidajen rediyo da talabijin.
Galibin waɗanda ke da damar barin ƙasar ta hanyar da bata dace ba, suna da ilimi sosai.
Sun haɗa da likitoci da ma'aikatan jinya da injiniyoyi da ƙwararrun 'yan fasaha. Hakan ya sa wasu ke kiran ficewar da “ƙwararru masu ficewa”.
Kungiyar likitocin Najeriya, ta ce akalla likitoci 50 ne ke barin Najeriya duk mako domin yin aiki a ƙasashen waje. Rashin yanayin aiki haɗe da rashin albashi da tsadar rayuwa sune manyan abubuwa da ya sa mutane ke ficewa daga ƙasar.
Kunle Ibisola, karamin likita ne wanda ya kasance yana aiki a Asibitin Kwalejin Jami’ar UCH, da ke kudu maso yammacin birnin Ibadan. Yanzu yana aiki da hukumar lafiya ta NHS a Scotland.

"Labari na shine labarin yawancin likitocin Najeriya," in ji shi ta wayar tarho. “Ban taba son barin Najeriya ba, niyyata ita ce in fara zama a can, in zama kwararre sannan in dawo don yi wa ƙasata aiki.
“Babban dalilin da ya sa na tafi shi ne albashi da kuma tsadar rayuwa. A ƙasar Birtaniya idan na yi aikin sa’o’i shida zuwa takwas sannan na mayar da kuɗin zuwa naira, zai yi daidai da albashin da nake karba a Najeriya duk wata. Kuma wannan bai ma haɗa da babban albashina na Birtaniya."
Ya ce shekara guda da ta wuce asibitinsa da ke Najeriya ya fara wahalar da likitoci.
“Wasu likitocin ba a biyan su albashi na watanni shida zuwa tara ba, saboda akwai matsala da batun tsarin biya na gwamnatin tarayya. Wasu manyan abokan aikinsu ba sa iya tuka mota zuwa aiki ko tura ‘ya’yansu makaranta. hakan ya abin darasi ga mutane da yawa."
Matarsa da 'ya'yansa suna shirin tafiya tare da shi zuwa Scotland nan ba da jimawa ba. Lokacin da na tambaye shi me yake ganin makomar Najeriya, sai ya kara fushi.
"Idan na yi tunanin abin da yawa, yana da takaici saboda ko da mutanen da ke makarantar likitanci a halin yanzu duk suna shirin fita. Idan ba ka shirin fita ba, mutane suna tunanin cewa ba ka damu ba ko kuma ba ka da kuɗi."
Na yi magana da likitoci guda shida, duk suna da irin wannan labari. Ga aiki mai yawa da kuma rashin biyan albashi, duk sun yanke shawarar ƙaura a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Ga waɗanda aka bari a baya, matsin lamba yana da yawa.
Cheta Nwanze, wani manazarci kan tattalin arziki a cibiyar bincike na SBM Intelligence, ya ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya a halin yanzu ya samo asali ne sakamakon ƙarancin abinci.
“SBM tana da abubuwan bincike na duba hauhawar farashin abinci musamman ma Jollof,” in ji shi, yayin da yake magana kan shinkafar tumatur, wadda ta shahara a faɗin yammacin Afirka.
“Muna lissafin matsakaicin kuɗin da ake kashewa wajen girka shinkafar jollof ga iyali mai mutane biyar, bai kai naira 4,000 ba a farkon shekarar 2016, amma yanzu ya kai kusan naira 10,000 – don haka ya ninka fiye da sau biyu cikin shekaru biyar.

Asalin hoton, Getty Images
Ya ce duk da cewa Najeriya ma ta fuskanci abubuwa na hauhawarar farashin kayayyaki kamar wasu wurare a faɗin duniya, musamman ma ƴaƙin Ukraine da annobar korona a shekarar 2020, akwai ƙarin wasu da suka shafi Najeriya.
Ya ce manoma da dama a arewacin Najeriya, inda ƙasar take samun yawancin abincinta, basu samu damar yin noma ba a ‘yan shekarun nan saboda hare-haren masu iƙirarin jihadi da kuma masu garkuwa da mutane.
"Idan ka haɗa wannan duka da kuma tsare-tsaren gwamnati na hana shigo da abinci da kuma ƙaruwar al’umma, na nufin cewa abinci ba zai wadatu ga kowa ba, wanda kuma zai sanya hauhawar farashi.’’
An ga tasirin hakan a kasuwannin ƙasar. A Ajah, wata ƙaramar kasuwar sayar da abinci da ke jihar Legas, mutane ƙadan ne ke zuwa idan aka kwatanta da baya.
Omowunmi Ajekigbe, wata ‘yar kasuwa ce da ke sayar da kuɓewa. “Kayayyaki basu yi tsada kamar yanzu ba a shekara da ta gabata,’’ in ji ta, “amma a wannan shekara, abubuwa sun tashi. Kana iya ganin kwastomomi na ta rububin zuwa saye, amma yanzu...da wuya ka ga wani.
A kusa da wani kanti, Cordelia Fidelis, na cinikin ganyayyaki tare da mai kantin. Ita ma tana da kantin sayar da abinci, tana zuwa kasuwa saye a kullu yaumin.
"Hauhawar farashin kayayyaki abin damuwa ne – a cikin watanni biyu, farashin doya ya ninka har sau biyu. Abin ba ya misaltuwa, komai ya yi tsada. Kwandon kwai ya yi tsada, nama ta yi tsada sannan manja ma farashinta ya yi sama.’’

Mutane da dama dai sun fara ɗaukar matakai don takaita yawan kuɗaɗen da suke kashewa.
Angela Chukwulozie, wata malamar makaranta ce da ta yi ritaya, inda yanzu ta koma sayar da takalma da aka buga a Italiya."Tun da farashin kayayyaki ya tashi, na yanke shawarar rage yawan abincin da ni da iyalaina ke ci a kowace rana. Maimakon cin abinci sau uku a rana, yanzu mun koma ci sau biyu.”
Bangaren tattalin arzikin shi ne babban damuwa ga ‘yan ƙasar gabanin gudanar da babban zaɓe a watan Febrairu. Duk da kasancewarta Najeriya a matsayin mafi girman tattalin arziki a nahiyar Afirka, mutum huɗu cikin goma na ‘yan ƙasar na rayuwa ne cikin talauci a cewar Bankin Duniya.
Dukkan ‘yan takara da ke son shugabancin ƙasar, sun yi alkawarin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar idan aka zaɓe su. Sai dai, akwai shakkun cewa ko za su iya cika alkawarin nasu.
Babban bankin ƙasar ya ce sauya fasalin kuɗin ƙasar, wanda zai kuma sanya a daina amfani da tsofaffin takardun kuɗi a ranar 10 ga watan Febrairu, zai taimaka wajen dawo da kuɗaɗen da ke hannun jama’a da kamfanoni zuwa bankuna.
Ya ce kashi 80 na kuɗaɗen da ake amfani da su a yanzu na a hannun jama’a. Babban bankin na fatan sauyin zai ba shi damar sanin hakikanin kuɗaɗen da ke yawo cikin ƙasar saboda ta samu damar magance hauhawarar farashi. Ko hakan zai yu ko ba zai yu shi ne abin da ‘yan ƙasar ke ta muhawara a kai.
A can Landan kuwa, Oroma na da fata mai kyau, duk da irin tsadar rayuwa da ƙasarta ke fuskanta.
"Babu wani wuri da ya fi gida. Ina komawa Najeriya a duk bayan kowane wata uku, saboda idan ban je ba, ina jin kamar zan mutu.
"Ina ganin kamar Najeriya cikin matsayin da, idan za mu canza a yanzu, lokaci bai kure ba. Mayar da hankali za mu yi: ya kamata mutane su samu ilimi da wutar lantarki da kuma hanyoyi. Idan za mu samu waɗannan abubuwa guda uku da inganta yanayin tsaro, ina ganin Najeriya za ta gyaru saboda irin kwararru da ke cikinta.”











