Yadda ƙarin takunkuman Trump kan Rasha za su shafi tattalin arziƙin duniya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Jonathan Josephs
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 5
Duk da kasancewarta ƙasar da aka fi sanya wa takunkumi a duniya, Rasha na ci gaba da amfani da arzikin makamashinta mai tarin yawa don ɗaukar nauyin yaƙin Ukraine.
To amma shugaban Amuka, Donald Trump na fatan sauya hakan, bayan ya bayyana aniyar sanya wa ƙasar ƙarin takunkuman da za su yi tasiri a hada-hadar kasuwancinta, idan har ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Ukraine ranar Juma'a, 8 ga watan Agusta.
Ƙarin takunkuman sun kunshi sanya wa kayayyakin ƙasashen da ke hulda kasuwanci da Rasha haraji kashi 100 idan aka shigar da su Amurka.
Man fetur da iskar gas ne manyan abubuwan da Rasha ta fi fitarwa, kuma ƙasashen ke suka fi sayen kayayyakin ƙasar sun haɗa da China da India da kuma Turkiyya.
"Nakan yi amfani da kasuwanci ta hanyoyi da dama, amma ya fi amfani wajen sasanta yaƙi'', kamar yadda Trump ya bayyana a makon da ya gabata.
Wannan ba shi ne karon farko da gwamnatin Trump ke sanya ƙarin haraji ba, inda a baya ya sanya shi domin hukunta masu sayen man fetur na Venezuela.
To sai dai amfani da su kan Rasha ka iya yin tasiri ga attalin arzikin duniya.
Rasha ce ƙasa ta uku mafi samar da man fetur a duniya, baya ga Saudiyya da Amurka. To sai dai mujallar Bloomberg ta ce an samu raguwar fitar da man ƙasar a wannan shekara.

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Ƙaruwar farashin makamashi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Hanya ta farko da ƙarin harajin da za a sanya da kayayaykin ƙasashen da ke sayen makamashin Rasha shi tashin farashin makamashi a duniya,'' in ji Kieran Tompkins ta cibiyar tuntuɓa kan tattalin arziki.
Idan har ƙarin harajin ya fara aiki, zai rage shigar da man fetur da isakar gas ɗin Rasha zuwa kasuwannin duniya.
Kuma idan aka samu raguwar makamashina a kasuwannin duniya dole farashinsa ta tashi, kamar yadda ya faru a 2022 lokacin da Rasha ta ƙaddamar da mamaya kan Ukraine.
Hakan kuma zai haifar da hauhawar farashin kayayyaki a faɗin duniya. Shugaba Trump ya ce bai damu da hakan ba saboda yawan man da Amurka ke samarwa.
Rasha dai ta yi ƙoƙarin samar da wani tsarin da za ta kauce wa takunkuman da aka sanya mata, wanda hakan kuma ya taimaka wa ƙasashen da ke huldar ciniki da ita su kauce wa barazanar harajin Trump.
"Ta samar da tsarin ne domin kauce wa illolin takunkuman da aka sanya mata'', in ji Richard Nephew, masanin takunkuman Amurka a Jami'ar Columbia

Asalin hoton, Ashish Vaishnav/SOPA Images/LightRocket via Getty Images
Tashin farashin wayoyin iPhone
Tun bayan mamayar Ukraine a 2022, Indiya ta kasance ta biyu mafi yawan sayen man Rasha, a cewar cibiyar binciken makamashi ta duniya.
"Su ke bayar da gudunmowar yaƙin. Kuma idan za su yi haka, ba zan ji daɗi ba,'' kamar yadda Shugaba Trump ya bayyana wa kafar yaɗa labaran Amurka ta CNBC a ranar Talata.
Idan ƙarin takunkuman suka fara aiki, kamfanonin Amurka da ke sayen kayyakin Indiya za su riƙa biyan harajin kashi 100.
Hakan zai sa irin waɗannan kayayyaki su yi tsada a Amurka ta yadda masu saye za su karkata ga wasu kamfanonin domin sayensu da sauƙi, lamarin da zai janyo wa Indiya gagarumar asara.
Ɗaya daga cikin hanyoyin da matakin zai yi tasiri shi ne tashin farashin wayoyin iphone da Amurkawa ke saya da Indiya.
Hakan tilasta wa Indiya dakatar da sayen man fetur daga Rasha.
Idan Rasha ta kasa sayar da man nata saboda irin wannan mataki da Amurka ta ɗauka kan ƙasashen da ke hulda da ita, zai sa ta kasa sayar da man nata, wani abu da zai sa ƙasar ta rasa kuɗin da za ta ɗauki nauyin yaƙin na Ukraine.
Rikicin kasuwanci da China
China ce ke sayen mafi yawan man fetur da Rasha ke fitarwa, kuma matakin na Trump zai zama cike da ƙalubalen aiwatarwa.
Dalili kuwa shi ne kayan da Amurka ke saya da China sun zarta waɗanda take saya daga Indiya da kusan ninki biyar. Kuma mafi yawan waɗannan kayyaki na amfanin yau da kullum ne kamar tufafi da kayan laturoni da kayan wasan yara.
Sanya ƙarin harajin kan China zai iya wargaza yarjejeniyar kasuwanci tsakanin manyan asashen biyu mafiya ƙarfin tattalin arziki da Trump ke muradi tun wa'adin mulkinsa na farko.
"Wannan mataki kuwa harzuƙa al'amura ne kawai domin China ba za ta lamunta ba,'' a cewar Farfesa Simon Evenett na cibiyar nazarin kasuwanci ta IMD.
Ya ƙara da cewa abu ne ''mai wahala'' a iya janye China daga hulda da Rasha ba tare da ƙwaƙƙwaran dalili ba, saboda yadda kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin shugabannin ƙasashen biyu a baya-bayan nan.
''Baya ga haka a duk lokacin da Amurka ta yi yunƙurin ƙaƙaba wa China ƙarin haraji ba ta jin daɗin haka a cikin gida''.
Kuma hakan zai haifar da hauhawar farashin kayyaki a Amurka, wani abu da Trump ya daɗe yana fatan magancewa.
A gefe guda kuma matakin zai haifar da asarar ayyuka a China, a daidai lokacin da tattalin arzikinta ke fama da matsaloli.
Gurgurta kasuwanci tsakanin Amurka da EU
Wani sharhi da cibiyar nazarin kasuwanci da ke Finland ta yi na nuna cewa ƙasashen EU ta Turkiyya na daga cikin manyan masu sayen makamashin Rasha.
Kafin 2022, Ƙasashen EU ne kan gaba wajen sayen makamashin Rasha, kodyake akan ya ragu tun bayan mamayar Ukraine.
A baya-bayan nan Belgium ta amince da sayen makamashi mai yawa daga Amurka, amma har yazu wasu na saye daga Rasha.
A watan Yuni, Shugabar Hukumar Gunadarwar EU, Ursula von der Leyen, ta amince da matsalolin, tana mai cewa ''Rasha ma ci gaba da ƙoƙarin ɓata mana suna ta hanyar mayar da makamashinta makamin yaƙi, inda ta alƙawarta kawo ƙarshen sayen man Rasha nan da ƙarshen 2027.
Dangantakar kasuwanci tsakanin Amurka ta EU ce mafi girma a duniya, kuma a baya-bayan nan ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniyoyin kasuwanci tsakaninsu, lamarin da ya sa Amurka ta sanya wa kayayyakin EU harajin kashi 15.
To amma yanzu da wannan ƙarin harajin da Trump ke barazanar sanyawa, hakan zai shafi EU.
Ƙara harajin kashi 100 ga kayyakin ƙasashen da ke sayan man Rasha zai rage yawan kayyakin EU da ake shigar da su Amurka.
Yiwuwar durƙushewar Rasha
Tattalin arzikin Rasha ya nua jajircewa tun bayan mamayar Ukraine, inda ko a shekarar da ta gabata ya samu haɓaka da kashi 4.3.
To sai dai, Ministan tattalin arzikin ƙasar, Maxim Reshetnikov a baya-bayan nan ya yi gargaɗin cewa ƙasar ta kama hanyar durƙushewa.
Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, IMF na hasashen cewa tattalin arzikin ƙasar zai bunƙasa da kashi 0.9 a wannan shekara.
Idan har sabbin takunkuman suka yi nasarar rage buƙatar kayyakin Rasha a kasuwannin duniya, to ba shakka hakan zai sa ƙasar ta kusanci durƙushewa.
Sai dai ba lallai ne a son haƙiƙanin tasirin da matakin zai yi kan tattalin arzikin Rasha ba, saboda ƙasar na hana wallafa alƙaluman tattalin arzikinta tun bayan mamayar Ukraine, ciki har da na man fetur da gas.
Kashi ɗaya bisa uku na kuɗaɗen da gwamnatin Rasha ke kashewa tana samunsu ne daga man fetur da iskar gas, to amma ana samun raguwar fitar da shi.
Haka kuma a baya-bayan nan Shugaba Putin na kashe mafi yawan kuɗin gwamnati kan tsaro fiye da kowane lokaci a baya.
Saɓanin Ukraine a ke kashe kashi 26 cikin 100 na kuɗinta a fannin tattalin arziki maimakon yaƙi.











