Waiwaye: Kashe sojojin Najeriya 17 a jihar Neja, da sabbin dokokin haraji

Lokacin karatu: Minti 6

Kamar kowane mako, wannan maƙala ta yi waiwaye kan muhiman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata.

Kashe sojojin Najeriya 17 a jihar Neja

Janar Christoper Musa

Asalin hoton, Nigerian Army

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana fara zaman makoki na kwanaki uku domin girmama sojoji 17 da suka rasa rayukansu a yayin wani harin da aka kai musu a Kwana Dutse, ƙaramar hukumar da ke jihar Neja.

Wannan zaman makoki zai gudana ne daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Yuni, 2025, a matsayin alamar juyayi da girmamawa ga sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare martabar ƙasa.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X, an umurci dukkan cibiyoyi da ma'aikatan soji a faɗin ƙasar da su yi ƙasa-ƙsa da tutocin sojin Najeriya a wannan lokacin.

Rundunar ta ce wannan mataki na nuni da yadda take ɗaukar rayuwar jami'anta da muhimmanci tare da nuna alhini ga iyalai da ƴan'uwa na waɗanda suka mutu.

Rundunar Sojin Najeriya dai ta tabbatar da mutuwar sojojin ne sakamakon hare-haren da wasu ƴan bindiga suka kai kan sansanonin soji da ke jihohin Neja da Kaduna.

Abdullahi Ganduje ya sauka daga shugabancin jam'iyar APC

Abdullahi Ganduje

Asalin hoton, Kano State Govenment

Shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga muƙaminsa bayan kwashe ƙasa da shekara biyu yana jagorancin jam'iyyar.

Wasu majiyoyi daga fadar shugaban Najeriya sun tabbatar wa BBC cewa Ganduje ya ajiye muƙamin ne bayan da fadar shugaban ƙasa ta umarce shi da yin hakan.

"Da gaske ne Ganduje ya sauka tun jiya (Alhamis) aka ba shi umarnin ya rubuta takardar murabus, a yau da safe (juma'a) ya miƙa takardar," in ji majiyar.

Hakan na zuwa ne bayan wani rudani da aka samu kimanin mako ɗaya da ya gabata a lokacin taron jam'iyyar ta APC na arewa maso gabashin ƙasar.

Karanta ƙarin bayani a wannan labarin na ƙasa:

Tinubu ya saka wa sabbin dokokin haraji hannu

Bola Tinubu

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan sababbin dokokin haraji huɗu a wani mataki na sauya fasalin tsarin karɓa da tattara haraji na ƙasar.

Gwamnatin ta ce sabbin dokokin za su sauƙaƙa tsarin, da rage wahalhalun haraji kan ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni, da kuma taimakawa wajen inganta karɓar haraji.

"Sauye-sauyen za su taimaki masu ƙaramin ƙarfi tare da tallafa wa ma'aikata ta hanyar ƙara yawan abin da suke samu,'' kamar yadda Shugaba Tinubu ya bayyana a watan da ya gabata lokacin bikin cika shekara biyu a kan mulki.

Ya ƙara da cewa: "Sauye-sauyen sun cire muhimmman abubuwa kamar abinci da ilimi da kula da lafiya daga tsarin biyan harajin VAT. Haka nan, sabon tsarin ya keɓe karɓar rance da sufuri da makamashin da ba ya gurɓata muhalli, duka wadannan ba za su biya harajin VAT ba, kuma duk wannan an yi ne domin sauƙaƙa wa magidanta''.

Karanta cikakken labarin a nan:

Mun kashe yaran Bello Turji a gidansa - Hukumomin jihar Zamfara

Jami'an tsaro na Zamfara

Asalin hoton, Zamfara State Government

Haɗin gwiwar jami'an sa-kai a jihar Zamfara sun yi wa riƙaƙƙen ɗan fashin dajin nan mai ƙaurin suna, Bello Turji ƙofar rago a wata maɓoyarsa tare da gwabza ƙazamin faɗa.

Hukumomin jihar sun ce jami'an sa-kai sun yi nasarar kashe mayaƙan Bello Turji fiye da 100 a farkon wannan mako.

Sun ƙaddamar da harin ne da gudunmawar wani tubabben ɗan bindiga, Bashari Maniya wanda ya jagoranci kai farmakin a kusa da ƙauyen Cida na ƙaramar hukumar Shinkafi.

Mataimaki na musamman kan harkokin tsaro ga Gwamnan Zamfara, Alhaji Ahmad Manga ya ce "an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya".

'Yan sa-kan CPG na Zamfara sun kuma samu goyon bayan dakarun Civilian JTF na jihar Borno, inda suka ƙaddamar da harin a-yi-ta-ta-ƙare na bazata ga maɓoyar ta Bello Turji.

Karanta cikakken labarin a nan:

Wasu baƙin ƴanbindiga sun tayar da ƙauyuka da dama a Zamfara

Wasu 'yanbindiga

Asalin hoton, @DanKatsina50

Al'ummar yankin Bukkuyum a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce wasu baƙin ƴanbindiga sun tarwatsa ƙauyuka da dama a yankin.

Ɗanmajalisar jiha da ke wakiltar yankin ya ce wasu baƙin ɓarayi ne daga kasashen waje suke kaddamar da sababbin hare-haren a sassan yankunan kananan hukumomin Bukkuyum da Anka na jihar Zamfara.

Honarabul Hamisu A. Faru Nasarawa Burƙullu, mai wakiltar Bukkuyum ta Kudu a majalisar dokokin jihar Zamfara ya ce ƴanbindigar sun kashe sama da mutum 20.

Ya ce al'amarin ya kai maƙura, har yana neman hana gudanar da harkokin noma a daminar bana a yankunan da abin ya shafa.

Karanta cikakken labarin a nan:

Waɗanda suka tsira daga kisan Filato sun bayyana yadda sojoji suka cece su

'Yanbindiga

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasu daga cikin waɗanda suka tsira daga kisan da aka yi wa wasu da za su je biki a Filato sun bayyana wa jaridar Daily Trust yadda aka kai musu hari a lokacin da suke tafiya zuwa bikin aure.

Ibrahim Umar, ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, ya ce suna kan hanyarsu ne daga Zariya zuwa Qua'an Pan domin bikin ɗan uwansa. A cikin motar akwai mahaifin ango, kawunsa da kuma ƙaninsa. Duk da cewa sun bayyana wa maharan cewa ba 'yan yankin ba ne, kuma suna ɗauke da goro da kyaututtukan biki, sai ya ce, "ba su saurare mu ba – suka kashe ƴanuwanmu."

Ya bayyana cewa mahaifi da ƙanin ango da kuma kawunsa duk an kashe su a harin.

Angon, wanda asalinsa daga Zariya ne kuma malami ne a wata makaranta a yankin, ya hadu da matar da zai aura a lokacin da yake koyarwa, sannan suka amince su yi aure. Ibrahim ya ce sun bayyana wa maharan cewa ba mazauna yankin ba ne, daga Jihar Kaduna suka taho domin halartar biki, amma ba su yarda ba "Dukkanmu dangin juna ne, daga ƙauye ɗaya muka fito," in ji shi.

Ibrahim ya ce da ba don sojojin da ke kusa da inda lamarin ya faru sun hanzarta zuwa ba, da abin zai fi muni. "Sojojin sun iso da wuri kuma suka cece mu. In ba don hakan ba, da labarin zai canza," in ji shi.

Wani, wanda shi ma ya tsira daga harin, Sa'adu Abdullahi, ya bayyana cewa sun yi ɓatan hanya ne suka shiga wani ƙauye ba da gangan ba. Bayan sun tsaya domin tambayar hanya, sai kwatsam aka fara kai musu hari.

Duk da cewa sun shaida wa mutanen cewa suna kan hanyar zuwa biki ne, hakan bai sa aka kyale su ba.

Kashe 'yan Kano a jihar Binuwai

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kakkausar suka tare da yin Allah-wadarai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasa biyu 'yan jihar a garin Makurɗi, babban birnin jihar Binuwai.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce, a jiya Litinin ne da misalin ƙarfe 11:00 da dare wasu da ba a gano ko su waye ba har yanzu suka far ma matasan biyu - Barhama Suleiman da Jamilu Ahmad, inda suka yi musu kisan-gilla, haka kawai.

A sanarwar gwamnan ya bayyana harin a matsayin na dabbanci da rashin imani da hankali, wanda ba za a lamunta da shi ba.

A yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya ga 'yan uwa da iyalan mamatan Abba Kabir ya jajanta wa fitaccen malamin nan na addinin Musulunci Sheikh Ibrahim Khalil wanda shi ne tamkar mahaifi a garesu.

Sannan ya roƙi jama'ar jihar ta Kano da su kwantar da hankalinsu, inda ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya wajaba don ganin an yi bincike a kan lamarin tare da hukunta waɗanda suka yi kisan.

Wannan ya faru ne kuwa yayin da ake ci gaba da alhinin kisan-gillar da aka yi wa wasu 'yan jihar Kaduna, 12 a garin Mangu na jihar Filato.

NNPCL ya ƙara farashin litar man fetur

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin litar mai daga naira 910 zuwa naira 945 a gidajen mansa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

Haka kuma kamfanin ya ƙara farashin litar mai a gidajen mansa da ke Legas daga naira 870 zuwa 915, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Wannan ƙarin ya nuna an ƙara naira 35 a kowace lita a Abuja, da kuma ƙarin naira 45 a Legas.

Jaridar Daily Trust mai zaman kanta ta ruwaito cewa tuni wasu gidajen man suka fara sayar da fetur ɗin a sabon farahi, inda ta ruwaito gidan man NNPCL da ke babbar hanyar Fin Niger Badagry ya fara sayar da man a naira 915.

Haka kuma a gidan man kamfanin NNPCL da ke yankin Kubwa na Abuja, tuni aka fara sayar da man a naira 945.