Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba zan bi Obi haɗakar ADC ba - Datti Baba-Ahmed
Tsohon mataimakin ɗantakarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a Najeriya, Dakta Yusuf Datti Baba-Ahmed ya nuna shakku kan manufar jam'iyyar hadaka ta ADC, gabanin zaɓen da za a yi a 2027.
Dansiyasar wanda ya yi takara a matsayin mataimakin Peter Obi a zaben shugaban kasa na 2023 da ya gabata, ya ce matsawar Obin ya koma ADC, to za su raba gari, don kuwa shi zai yi zamansa a jam'iyyar Labour.
Ita ma kanta Labour din ya ce idan ta sake ba Obi takara sai ya yi shawara ya ga ko zai sake yarda ya yi masa mataimaki.
A hirarsa da BBC, tsohon sanatan wanda ya wakilci mazabar Kaduna ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya a 2011, ya ce ita ma jama'iyyar PDP na neman Obi don ba shi takara.
Dattin yana yi wa jama'iyyar hadakar ta ADC kallon wadda ba ta cancanci ya shig ta ba, saboda wadanda ya ce su ne jiga-jigan tafiyar.
''Magana ta farko wadanda suke hada hadakar sune suka yi ta da. Idan da ba su ba ne suka yi ta da. To amma su ne suka yi.
''Sannan su din nan dukkansu daga ina suka fito? Daga hadaka ko daga jam'iyyar APC? Me ya sa suka fito?''
Ya kara da cewa : ''Daya an kada shi, daya sai da ya je majalisar dattawa aka yi mai tambayoyi sannan ya fito aka hana shi minista. Na uku shi kuma yana jira har yau - Allah ina shugabancin da nake jira Ka ba ni?''
Dansiyasar wanda shi ne mai jami'ar nan mai zaman kanta ta Baze da ke Abuja, ya ce ba wai kayar da gwamnati ba ne ke da wuya - ''Ni abin da nake gudu a ka da gwamnati a sake komawa gidan jiya.
Datti wanda ya kuma taba wakiltar mazabar Zaria a majalisar wakilan Najeriya daga 2003 zuwa 2007, ya ce yana jiran masu hadakar su nuna masa cewa don talaka suke yi, kafin ya shiga hadakar.
Abin da ya ce ba za su iya nunawa ba.
''Wace ce ADC ? Me ya sa zan saki reshe in kama ganye? Su wane ne shugabannin hadakar ?
''Me ya sa zan biye wa wanda yau a jihata ta Kaduna yanzu haka majalisar dokokin jihar ta Kaduna akwai kwamiti a kanshi.
''Sannan ba da dadewa ba kwamishinanshi ya fito daga gidan yari. Irin wadannan shugabannin za ka zo ka biye ma?''
Dangane da yadda yake nuna kin hadakar ta ADC, ya kara bayani da cewa : ''Ba na cikin wadanda ke biye wa mutane, a rufe ido a rufe tunani a yi ta hauka. Ba na cikinsu, ba na irin wannan abin ko kadan a rayuwata, balle kuma a siyasata.''
Ya ce, muhimmancin fitar da shugabanni ya wuce yanda kawai za a zo a yi maka yarfe ka ce ka dauka.