Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin Datti Baba-Ahmed ya juya wa Peter Obi baya ne?
A ranar Litinin ne Datti Baba-Ahmed ya kai wa ɓangaren shugabancin Julius Abure na jam'iyyar Labour ziyara a Abuja.
Datti wanda ya yi ya jam'iyyar ta LP takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen shugaban Najeriya na 2023, ya ce zai jagoranci tattaunawar sasanci tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasar jam'iyyar a 2023, Peter Obi da kuma wasu masu ruwa da tsaki, da nufin sake haɗa kan jam'iyyar gabanin zaɓen 2027.
"Labour ba jam'iyya ba ce da mutum zai fice daga cikinta," in ji Datti yayin da ya gana da manema labarai bayan ziyarar da ya kai wa Abure.
Julius Abure shi ke jagorantar wani ɓangare na jam'iyyar LP da ke iƙirarin zama sahihin shugabancin jam'iyyar, wanda kuma ke takun tsaka da ɓangarensu su Peter Obi.
Peter Obi ya fi karkata ne ga ɓangaren shugabanci Nenadi Esther Usman, waɗanda suka bayyana cewa wa'adin shugabancin Abure ya ƙare, a saboda haka ne suka yi iƙirarin yin zaɓen shugabannin a farkon makon da uke ciki.
Sai dai an yi mamakin ganin Datti yana alaƙanta kansa da ɓangaren Abure, wanda a makonnin da suka gabata suka bai wa Peter Obi wa'adin ficewa daga jam'iyyar sanadiyyar alaƙarsa da sabuwar gamayyar ƴan hamayya.
A lokacin ziyarar, Datti ya gargaɗi ƴan jam'iyyar ta LP kan shiga jam'iyyar haɗaka waɗanda aƙidunsu ba su irin ɗaya da Labour ba.
Martanin ɓangaren Peter Obi
Ɓangaren na Peter Obi dai ya ce ba shi da masaniya kan ziyarar da Datti Baba-Ahmed ya kai wa Julius Abure.
Wani na kusa da Obi, Ibrahim Abdulkarim ya shaida wa BBC cewa Datti ya mallaki hankalin kansa wanda kuma haka zai sa ya shiga tsakani idan ya ga an samu matsala don samar da mafita.
"Shi Datti Baba-Ahmed ya sha faɗa wa Peter Obi cewa yana son a samu sulhu a wannan jam'iyya kuma ba ya son a rasa irin yawan ƙuri'un da ta samu a zaɓen da ya gabata a zaɓe mai zuwa," in ji Abdulkarim.
Da BBC ta tambaye shi kan yanda suke kallon ziyarar Datti Baba-Ahmed, ya ce: "Baba-Ahmed yana ƙoƙarin ganin an gyara matsalar da aka samu ne, yiwuwarta ko rashin yiwuwar gyarar abu ne na Allah. Mu a ɓangarenmu muna ganin abu ne da za a sa ido a gani don duk wanda yake neman sulhu dole ne mu ba shi goyon baya wajen yin gyara," in ji shi.
Jam'iyyar ta Labour dai ta shiga cikin rikici wanda ya ƙara ta'zzara a watan Afrilun wannan shekara, inda mambobin jam'iyyar uku suka ayyana kansu a matsayin shugabannin jam'iyyar.
Wannan kuma ya zo bayan da Kotun Koli ya yi watsi da shugabancin Julius Abure, wanda hukumar zaɓen Najeriya ta amince a matsayin shugaban jam'iyyar.
Rikicin ya ƙara ta'zzara ne bayan da Lamidi Apapa ya ce shi ne ya kamata ya jagoranci jam'iyyar a matsayinsa na babban jami'in kwamitin zartaswa.
Shin Obi zai amince a yi sulhu?
Ibrahim Abdulkarim ya ce abu ne mai sauki a wajen Peter Obi wurin amincewa da yin sulhu da ɓangaren Julius Abure.
Ya ce Obi mutum ne mai son zaman lafiya da kuma yin sulhu a kodayaushe.
"Kullum yana cewa yana yin abu ne don jama'a ba kansa kaɗai ba. Ya sha magana da Abure da mutanensa da kuma waɗanda ke zuga shi domin ganin an zo an dunƙule wuri ɗaya don gyara Najeriya".
Ya ce hakan ne ya sa shi ma Datti yake son ganin ya ba da gudummawa wajen samar da sulhu a jam'iyyarsu ta Labour.
Sai dai a baya-bayan nan Peter Obi tare da wasu manyan jiga-jigan adawa a Najeriya sun shiga jam'iyyar haɗaka ta ADC, wadda suka ce a cikinta za su kalubalanci jam'iyya mai mulki ta APC a zaɓen 2027.
Haɗakar ƴan siyasar dai ta tayar da ƙura, inda masana da ƴan ƙasar ke hasashen cewa za ta iya yin tasiri a babban zaɓen ƙasar mai zuwa.
Me Peter Obi yake nema?
Duk da cewa Obi bai bayyana ficewarsa daga jam'iyyar Labour ba, amma ya tabbatar da cewa zai yi takarar shugaban ƙasa, inda ya yi watsi da yiwuwar zama mataimakin Atiku Abubakar.
Obi ya bayyana hakan ne a gidan talbijin na Channels a makonnin baya-bayan nan.
"Zan tsaya takarar shugaban ƙasar jamhuriyar Najeriya, kuma na yi imani ina da cancantar yin hakan." In ji Obi.
"...Babu wanda ya taɓa tattauna batun (kasancewa mataimakin Atiku Abubakar). Mutane suna hasashen abubuwa da yawa. Babu mutumin da ya taɓa magana da ni a kan wannan cewa ko zan zama kaza ko kaza," in ji shi.