Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa PDP da LP ke ɓaɓatu kan shigar Atiku da Obi ADC?
Hankalin jam'iyyun hamayya na PDP da LP a Najeriya ya yi matuƙar tashi inda jam'iyyun suka ɓara dangane da shiga haɗakar ADC da Atiku Abubakar da Peter Obi suka yi.
Atiku Abubakar ya yi takarar neman shugaban ƙasa har karo biyu a jam'iyyar PDP a 2019 da kuma 2023 ba tare da samun nasara ba.
Shi kuma Peter Obi ya yi takara a karon farko a jam'iyyar LP a 2023, inda ya kara da shugaba Tinubu na APC da Atiku Abubakar na PDP da kuma Rabi'u Kwankwaso na NNPP.
Duk da cewa dai ba a san maci tuwo ba har sai miya ta ƙare amm ana kyautata tsammanin cewa Atiku da Peter Obi ka iya yin takara a ƙarƙashin haɗaka ta jam'iyyar ADC da suka shiga a makon nan.
To sai dai jam'iyyun da fitattun ƴan siyasar biyu wato PDP da LP na nuna rashin jin daɗinsu dangane da haɗakar da ƴaƴan nasu suka shiga.
PDP ta gargaɗi Atiku da muƙarrabansa
Tun dai bayan sanar da dunƙulewar da Atiku da wasu ƴan siyasa suka yi a ƙarƙashin jam'iyyar ADC, jam'iyyar hamayya ta PDP ta nuna cewa ba ta lamunta da tsarin ba, kasancewar Atikun bai sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ba.
A wata tattaunawa da BBC, shugaban jam'iyyar PDP na riƙo, Umar Damagum ya ce jam'iyya za ta hukunta duk wadda ya tafi zuwa haɗaka.
"AI mutanen da ke alƙanta kansu da ADC ɗin dama can su ne matsalar PDP, kuma lallai ne su futo su zaɓi ko PDP ko kuma ADC. Babu yadda za a yi mu bar su su zamar mana ƙadangaren bakin tulu," kamar yadda Ibrahim Abdullahi ,mataimakin mai magana da yawun jam'iyyar ta PDP a Najeirya ya shaida wa BBC.
Da aka tambaye shi ko me zai ce dangane da yadda ministan Abuja, Nyesom Wike yake jam'iyyar PDP kuma a lokaci guda yana aiki ga jam'iyyar APC, sai ya ce:
"Ai su ne sanadiyyar tunzura Wike duk abubuwan da yake yi a jam'iyyar su ne ummul-aba-isi."
Shi ma gwamnan jihar Bauchi Bala Muhamamd a tattaunawarsa da BBC, ya ce "ba zan bi sakarci ba" na bar jam'iyyar PDP na koma wata adda."
Baya ga Atiku Abubakar, akwai ƙarin wasu jiga-jigan jam'iyyar ta PDP kamar Alhaji Sule Lamiɗo da Amabasada Aminu Wali da sanata Abdul Ningi da suka hallara a wurin taron haɗakar ba tare da ficewa daga jam'iyyarsu ta PDP ba.
LP ta bai wa Peter Obi wa'adin sa'a 48
Ita kuwa jam'iyyar LP ta bai wa mutumin da ya yi mata takarar shugaban ƙasa a 2023 Peter Obi, wa'adin sa'a 48 da kodai ya gaggauta ficewa daga jam'iyyar ko kuma ya bar jam'iyyar haɗaka ta ADC.
Ɓangaren Julius Abure na jam'iyyar Labour ya bai wa Peter Obi wa'adin sa'o'i 48 da ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ta LP bisa haɗakar ADC da ya shiga.
A wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar ta ce:
"Jam'iyyar Labour Party ba ta cikin wannan tsari kuma ta nesanta kanta daga shirin haɗakar ADC," in ji mai magana da yawun ɓangaren na LP.
Sai dai kuma shugabancin jam'iyyar ƙarƙashin Nenadi Usman, ya yi watsi da wa'adin.
Abin da ya sa jam'iyyu za su ji haushin ADC - Masani
Dangane da dalilin da ya sa jam'iyyun PDP da LP ke takaicin ficewar mambobin nasu zuwa haɗaka, Malam Kabiru Sufi masanin siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a kano wato CAS ya ce saɓanin haɗakar da aka saba gani wannan haɗakar ta ADC ta zo da wani sabon salo wanda bai zama lallai ya yi wa jam'iyyun da aka bari daɗi ba.
"A wannan karon ƴan jam'iyyun ne suka fito daga jam'iyyunsu suka shiga jam'iyyar da take da rijista, inda wasu ma ba su sanar da fita daga jam'iyyun nasu ba. Misali ƴan jam'iyyar PDP da dama an gan su a taron haɗakar kuma ba tare da sanar da ficewarsu daga jam'iyyar tasu ba."
Masanin ya ƙara da cewa a baya an yi haɗaka iri-iri masu kama da wannan.
"Ko a jamhuriya ta biyu mun ga yadda jam'iyyu kan yi haɗaka domin ƙalubalantar jam'iyya mai mulki, inda ƴan jam'iyya kan shiga haɗakar ba tare da barin jam'iyyunsu ba. Misali za ka ga a tarayya ana haɗaka amma kuma a jihohi kowa na jam'iyyarsa."