Ko ƙarin farashi zai sa man fetur ya wadata a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Ba a kauce hanya ba idan aka ce ƙarin kuɗin man fetur ya zama jini da tsokar 'yan Najeriya, amma abin da ya fi ɗaure wa mutane kai shi ne ana ƙara kuɗin amma man yana ƙara wahalar samuwa.
Daga shekarar 2000 zuwa 2020, gwamnatocin da suka mulki ƙasar sun ƙara kuɗin litar man fetur sau 11 a wannan tsakanin.
Sai dai ƙarin da kamfanin mai na gwamnatin ƙasar NNPC Limited ya yi a yanzu - daga naira 617 zuwa naira 897 - na musamman ne saboda shi ne aka yi shi a daidai lokacin da kamfanin ya ce yana fama da ƙarancin kuɗi.
Rahotanni sun nuna cewa tuni NNPCL ya sanar da gwamnatin Najeriya cewa ba zai samu damar biyan wasu haraje-haraje ba saboda kuɗin da yake kashewa wajen sauƙaƙa farashin man ga 'yan ƙasa - wato tallafin mai a taƙaice.
A madadin haka, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta amince wa kamfanin ya yi amfani da kason da ya kamata a ba ta na ribar da aka samu wajen sayar da man a rabin farashinsa da NNPCL ɗin ya kamata ya sayar wa 'yan ƙasa.
Duk da rashin alfanu da aka saba gani a baya na ƙarin kuɗin wajen rage ƙarancin fetur, ko na yanzu zai taimaka wajen rage wahalar samunsa a ƙasa baki ɗaya?
Wannan ita ce tambayar da muka yi wa masana biyu a ɓangaren makamashi domin jin amsarta.
'Dole ne sai NNPCL ya ƙara farashi ko da babu cigaba'

Asalin hoton, Getty Images
Tun daga ranar Lahadi da NNPCL ya fitar da sanarwar cewa "babban bashin" da 'yankasuwa da ke shigo da mai ke bin sa yana takura masa sosai wajen gudanar da aikinsa, wasu masu sharhi suka fara hasashen ƙarin kuɗin man fetur.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Wannan bashi ya jawo takura sosai a kan kamfanin kuma yana yin barazana ga cigaba da samar da man a faɗin ƙasa," in ji kakakin NNPCL Olufemi Soneye cikin wata sanarwa.
Kafofin yaɗa labarai a ƙasar sun ce bashin ya kai dala biliyan shida.
Sanarwar ta zo ne mako biyu kacal da kamfanin ya sanar da samun gagarumar riba ta shekara ɗaya wadda ita ce mafi yawa a tarihinsa ta naira tiriliyan 3.297 ya zuwa Disamban 2023.
Masanin harkar makamashi Injiniya Yabagi Sani ya ce ya zamar wa kamfanin wajibi ya ƙara kuɗi domin samun damar gudanar da harkokinsa saboda sabuwar dokar man fetur ta 2022.
"Cire tallafi da shugaban ƙasa ya yi, da sauya tsarin canjin kuɗi, da kuma shigowa da ɗanyen man fetur daga waje sun sa dole kashe kuɗi a ɓangaren NNPCL ya ƙaru," in ji shi.
"Ka ga ke nan idan za a shigo da mai sai NNPCL ya nemi dalar Amurka, kuma yanzu dala ta kai N1,600. Kazalika, ka san sabuwar dokar man fetur ta PIA ta sauya alƙiblar kamfanin daga na gwamnati zuwa na 'yankasuwa.
"A taƙaiace dai dole ne sai NNPCL ya ƙara kuɗi tun da an daina biyan tallafi. Sannan kuma jihohin arewaci da ma dole ne su sayi man da tsada saboda jigilarsa da ake yi daga kudanci."
'Hanyoyi biyar da za su sa mai ya wadata saboda ƙarin farashin'

A gefe guda kuma, Dr Ahmed Adamu - masani kan tattalin arzikin man fetur kuma malami a Jami'ar Nile da ke Abuja - na ganin ƙarin kuɗin man da aka yi a yanzu zai sa ya wadata saboda wasu dalilai kamar haka:
Na farko, masanin na ganin cewa 'yankasuwa da dillalan da ke ɓoye man saboda tunanin za a ƙara kuɗinsa nan gaba yanzu za su fito da shi.
"Sannan waɗanda ba su son sayo shi saboda ribar ta yi musu kaɗan, yanzu za su sayo shi saboda an ƙara kuɗinsa," a cewarsa.
"Shi kan sa NNPCL, nauyin da yake kan sa na samar da shi a farashi mai sauƙi zai ragu wanda hakan zai ba shi ƙwarin gwiwar shigo da fetur ɗin mai yawa sama da yadda yake yi a baya.
"Haka nan, yawan buƙatar man za ta ragu a faɗin ƙasa baki ɗaya saboda farashin sa zai yi wa wasu tsada.
"Sannan hakan zai rage wa masu fasa-ƙwaurin man zuwa ƙasashen ƙetare ƙwarin gwiwa saboda yanzu ba za su samu riba ba sosai."
Ko matatar Dangote za ta taimaka?
Da gwamnatin Najeriya ba ta biyan tallafin man fetur da farashinsa tuni ya zarta naira 1,000.
A makon nan kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa NNPCL ya cim ma yarjejeniya da matatar Dangote kan shi ne zai dinga saye baki ɗayan man da za ta fara samarwa nan gaba kaɗan.
"Yanzu matatar za ta fara samar da tataccen mai lita miliyan 25 kullum a watan Satumba, inda daga baya za ta rika samar da miliyan 30 daga watan Oktoban 2024," kamar yadda hukumar kula da cinikayyar fetrur NMDPRA ta bayyana cikin wata sanarwa.
Ahmed Adamu na ganin hakan zai taimaka wa Najeriya ta ɓangarori da dama, ba man fetur kawai ba.
"Wannan zai rage wa Najeriya tsadar shigowa da mai daga ƙasashen waje, musamman jigilarsa a jirgin ruwa.
"Sannan da naira za a sayar wa matatar ɗanyen mai kuma ita ma da naira za ta sayar wa 'yankasuwa tataccen a cikin gida. Wannan zai ƙara wa naira daraja kuma zai ƙara haɓaka tattalin arzikin ƙasar."
Yayin taron manema labarai da ya gudanar ranar Talata, Aliko Dangote ya ce wannan matakin zai taimaka wa Najeriya wajen rage dogaro kan dalar Amurka da kashi 40 cikin 100.
Sai dai kuma, Yabagi na ganin ko da matatar Dangote ta fara aiki akwai sauran matsalolin da ke buƙatar gyara kafin man ya wadata.
"Ai matatar Dangote a Legas za ta samar da man, kenan sai an yi jigilarsa zuwa jihohi masu nisa kamar Borno da Kano. Sai an biya kuɗin jigila, sannan kuma yana ɗaya daga cikin dalilan da NNPCL ke bayarwa na ƙaranci fetur a yanzu."











