Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙarin hauhawar farashin da aka daɗe ba a gani ba na gigita ƴan Najeriya
Tashin farashi a Najeriya ya tursasawa ɗumbin 'yan ƙasar, rungumar nau'o'in abincin da ake kira ci-kar-ka-mutu, a wasu lokutan har wasu kan kwana da yunwa.
'Yan ƙasar na fama da ƙarin farashi babu ƙaƙƙautawa, wanda a iya cewa matasa 'yan ƙasa da shekara 30, ba su taɓa ganin irinsa ba a rayuwarsu.
"Farashi kam gaskiya... ba ya taɓuwa a kasuwa. In dai farashi ake tambaya, ba ya taɓuwa a kasuwa, more especially ma a Adamawa," in ji wata matar aure mai suna Fatima Aliyu.
Tsadar kayayyaki, ta kai abin da ake kira farashin yau daban, na gobe kuma daban, ga magidanta masu zuwa cefane.
Alƙaluman Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasar sun ce hauhawar farashin ya yi ta ƙaruwa cikin wata 12 a jere inda ya kai zuwa kashi 28.92 daga kashi 28.20 a watan Nuwamba.
Tsadar ta kai matsayi mafi tsananin da aka taɓa gani a cikin sama da shekara 27 a watan Disamban bara.
Hukumar ƙididdiga ta ce hakan ta faru ne, sanadin tsadar farashin abinci, lamarin da kuma ya ta'azzara tsadar rayuwa da ƙarin matsin lamba a kan babban bankin Najeriya wajen ƙara kuɗin ruwa.
Wani magidanci a Gusau babban birnin jihar Zamfara, ya ce a baya-bayan nan ya riski shinkafar da yake saya kwano ɗaya naira 2,400 amma an yi mata ƙarin 300. Haka zalika, burodin da yake saya 800, "Da na je saya ranar Litinin, ya koma 1,100. Can A baya naira 400 nake sayen shi."
Fatima Aliyu mazauniyar Adamawa ta ce ledar maggi a yanzu ta kai naira 800-900, yayin da mudun shinkafa wadda ita ce jigo, in ji ta, ya kai naira 1,500-1,600.
"A da za ka iya ka je kasuwa, da ɗan dubunka uku. Ka sayi shinkafanka. Ka sayi magginka, ka sayi ɗan nama ko kifi, ka ɗan ƙawata miyanka, kai har da kayan ƙamshi, in ji ta.
"To yanzu kam ana ƙoƙari ne ta yaya za a yi rayu ne ba wai a samu balancediet ba. Ba maganar balance diet a binci kawai ka ci ne kar ka mutu."
Rahotanni sun ce tun cikin 1996, rabon da a ga hauhawar farashi mai tsanani irin na watan Disamba a ƙasar mafi girman tattalin arziƙi ta Afirka.
Alƙaluman sun ce hauhawar farashin kayan abinci, wanda shi ne kaso mafi yawa na tsadar kayan masarufin a Najeriya, ya tashi daga kashi 33.93 a watan Disamba daga kashi 32.84 a Nuwamba.
Kayan abincin da farashinsu ya fi tashi sun haɗar da burodi da dangin hatsi da man girki da kifi da nama da kayan marmari da ƙwai.
Abinci yana wahala, in ji Fatima.
"Kuma hakan yana shafar rayuwar aiyali." Ta ce tsada ta sanya kusan kowa ya koyi rowa a gidansa. Dole hakan ya shafi iyali in ji Fatima.
Masharhanta a ƙasar suna alaƙanta tashin farashin ne da ƙaruwar kuɗin man fetur da kuma durƙushewar darajar naira.
Ta ce lamarin ya jefa ƙunci da ɓacin rai tsakanin ma'aurata.
"Maigida zai fita, ya tafi nema. Zai dawo ka gan shi kamar an masa duka. Ka tambaye shi ya ce maka babu, ka ci gaba da tambaya, ya fara ɓata rai. Ba maigidan da zai so, ya fita bai samu abin da iyalansa za su ci ba, sannan ya dawo cikin farin ciki. Babu shi!"
Yaro Mai bindin Kantin Daji a garin Gusau ya ce yanzu ba abu ne mai yiwuwa ba, ka iya hasashen farashin wani kaya. Farko abin da ya fara tayar min da hankali shi ne farashin burodi. Ya ce suna bai wa iyalansu haƙuri ne kawai saboda al'amura sun fi ƙarfi talaka kamarsa.
Masharhanta irinsu David Omojomolo na cibiyar Caital Economics sun yi hasashen cewa hauhawar farashi a Najeriya za ta iya kai wa har kashi 30 nan da ƙarshen wata uku na farko
A cikin watan Mayu ne Shugaba Bola Ahmed Tunubu ya bijiro da gyare-gyare mafi ƙarfin hali a cikin shekaru gomma bayan ya yi watsi da manufar cire tallafin man fetur, darajar kuɗin Najeriya kuma ta karye a ƙoƙin farfaɗo da bunƙasar tattalin arziƙi. Sai dai har yanzu ba a fara ganin bunƙasar ba, yayin da hauhawar farashi ke daɗa muni.