Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me mulkin wa'adi ɗaya da Peter Obi ke iƙirari ke nufi?
A ranar Lahadi ne tsohon ɗantakarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar LP a 2023, Peter Obi ya sake nanata aniyarsa na yin wa'adi ɗaya na shekaru huɗu a matsayin shugaban Najeriya idan aka zaɓe shi a 2027.
Peter Obi ya yi martani ne ga kalaman gwamnan jihar Anambra na yanzu, farfesa Charles Soludo wanda ya ce duk mutumin da ya ce wa'adi ɗaya kawai zai yi a kan mulki to ya kamata "a duba lafiyar ƙwaƙwalwarsa".
Ko a baya ma an sha jiyo Peter Obi na nuni da cewa idan ƴan Najeriya za su zaɓe shi to wa'adi ɗaya kawai zai yi wani abun da ke nuni da irin imanin da ɗantakarar yake da shi na cewa dole ne mulki ya koma kudanci.
Kalaman Peter Obi
A shafinsa na X, Peter Obi ya ce idan ya samu nasarar zama shugaban ƙasar, wa'adi ɗaya na shekara huɗu kawai zai yi kamar yadda ya yi alƙawari.
"Ko tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln wa'adi ɗaya ya yi na shekara huɗu, sannan John F. Kennedy bai ma ƙarasa wa'adi ɗaya ba, amma ana ci gaba da tunawa da su a matsayin shugabanni masu adalci."
Ya ce ko a Afirka, Nelson Mandela ya zama abin koyi a duniya wajen shugabanci na adalci, "amma wa'adi ɗaya kawai ya yi. Ba daɗewa a ofis ba ne ke alamta nasara, irin ayyukan da shugaba ya yi ne za a riƙa tunawa."
Ya ƙara da cewa ya san ƴan Najeriya ba su cika yarda da maganar ƴan siyasa ba, "amma duk da haka akwai masu cika alƙawari."
Obi ya ce duk da wasu ƴan Najeriya na da hujjar ƙin amincewa da alƙawarin ƴansiyasa amma a cewarsa, yana da tarihi mai kyau wajen cika alƙawari tun daga lokacin da ya fara siyasa a Anambra, inda ya ce wata 48 sun isa duk wani shugaba da ya shirya mulki ya yi abin da ya dace.
"Idan na zama shugaban Najeriya a wa'adi ɗaya zan magance matsalar tsaro, zan yaƙi da talauci in inganta aikin gwamnati, sannan zan fifita ɓangaren ilimi da kiwon lafiya, sannan in yaƙi cin hanci da rashawa. Sannan uwa-uba zan inganta ɓangaren noma ta hanyar amfani da kimiyya da fasaha domin Najeriya ta zama ƙasa mai ciyar da kanta da wasu ƙasashen." In ji tsohon gwamnan jihar Anambra.
'Sabon salon siyasa' ne
Malam Kabiru Sufi malami a kwalejin share fagen shiga jami'a kuma masanin kimiyyar siyasa ya ce abin da Peter Obi ke faɗi wani sabon salon siyasa ne.
"Maganar da Peter Obi ta saɓa da ɗabi'ar ƴan siyasa. Wataƙila yana nema ya yi amfani da wannan ne domin ya nuna shi ya sha banban da sauran ƴan siyasa da suka zo a baya da wataƙila ma kwata-kwata ba sa tattauna irin wannan batun. Wannan zai nuna cewa shi ne ya fara fito da wannan batu wataƙila domin ya samu karɓuwa." In ji malam Kabiru Sufi.
To sai dai Malam Kabiru ya ce duk da waɗannan kalaman na Peter Obi akwai yiwuwar fuskantar matsin lamba ko kuma shi da kansa ya sauya ra'ayi.
"Soja ma an zo masa da buƙatar ya zarce ballanta ma ɗansiyasa? Shi ya sa wasu ke kallon kalaman na siyasa ne."
"Zawarcin ƴan arewa"
Masana na ganin cewa Peter Obi na son ya yi amfani da ragowar wa'adi guda ɗaya da ya ragewa Kudancin ƙasar bitsa la'akari da tsarin karɓa-karɓa.
A 2027, wa'adin farko na shugaba Tinubu zai ƙare bayan karɓa mulki daga hannun Muhammadu Buhari, ɗan Arewaci da ya yi wa'adi guda biyu na shekara huɗu-huɗu.
Peter Obi na yin amfani da wannan dama wajen jan hankalin ƴan arewa domin nuna musu cewa idan ya samu nasarar kayar da Tinubu to wa'adi ɗaya zai yi wato ya kammala zangon kudanci.
"Abin ya yi kama da siyasa domin neman yardar masu zaɓe (mutanen Arewa)." In ji Malam Kabiru Sufi.
Ba dai waɗannan ne kalaman farko ba daga Peter Obi na neman karɓuwa ga ƴan arewacin ƙasar, inda ko a watan da ya gabata sai da ɗan siyasar ya faɗi cewa marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ba shi amanar ƴan ƙasar.