Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
A wace jam'iyyar Peter Obi zai tsaya takara a 2027?
Kiraye-kiraye da zawarcin da jam'iyyun siyasar Najeriya ke yi wa tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi na ƙara jefa ƴan ƙasar cikin rashin tabbas dangane da haƙiƙanin jam'iyyar da ɗan siyasar zai yi takarar a cikinta a 2027.
Batun takarar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar, Peter Obi dai ba wani ɓoyayyen al'amari ba ne tunda ya furta da bakinsa, sai dai abin da har yanzu bai fito fili ba shi ne a wace jam'iyya zai yi takarar?
BBC ta yi duba dangane da jam'iyyun da ke zawarcin tsohon ɗantakarar shugaban ƙasar a 2023 a jam'iyyar LP, Peter Obi da kuma cece-kucen da ake yi.
Peter Obi bai yi rajista da ADC ba - Bolaji
Mai riƙon muƙamin sakataren watsa labaran jam'iyyar haɗaka ta ADC, Malam Bolaji Abdullahi ya ce har yanzu tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi bai yi rajista da jam'iyyar ba duk kuwa da cewa da shi ake yin komai.
Malam Bolaji wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba a shirin gidan talbjin na Channels mai suna 'Politics Today' ya ce har yanzu Peter Obi bai karɓi katin jam'iyyar ADC ba sakamakon damar da jagorancin jam'iyyar ya ba shi na kammala abubuwan da ya fara kan zaɓe a jam'iyyarsa ta LP.
"Babu matsala a ADC. Dalilin da ya sa Peter Obi bai yi rajista ba shi ne ya nemi izinin mu ba shi damar kammala ayyukan da ya fara a jam'iyyar Labour Party kasancewar yana da jama'a a jam'iyyar...," in ji Bolaji.
Ana dai ganin sanarwar ta ADC ba za ta rasa nasaba da zargin cewa jam'iyyar PDP tana zawarcin Peter Obi ba.
PDP na zawarcin Peter Obi?
A wata hira da BBC ta yi da, tsohon mataimakin Peter Obi a takarar neman shugabancin Najeriya a jam'iyyar LP a 2023, Datti Baba-Ahmed ya tabbatar da cewa jam'iyyar PDP na zawarcin Peter Obi.
"PDP ma na zawarcin Peter Obi. Ni dai ba zan bi shi jam'iyyar haɗaka ta ADC ba. Amma idan ya yi takara a LP to zan dafa masa.' In ji Datti Ahmed.
An kuma jiyo jigo a jam'iyyar ta PDP, tsohon ministan sadarwa na Najeriya, Farfesa Jerry Gana na cewa idan Peter Obi ya koma PDP to zai samu ƙuri'ar al'ummar arewacin ƙasar.
"Ni mai bincike ne, kuma ina binciken ra'ayoyin jama'a. A jihohin arewaci, idan Peter Obi ya yi takara a PDP zai buge duk wani ɗantakara saboda mutanenmu suna da buɗaɗɗiyar zuciya." In ji Farfesa Jerry Gana a gidan talbijin na Arise TV ranar Laraba.
Ita ma jam'iyyar ta PDP ba ta musanta ba, illa ma dai yin maraba da Peter Obin.
"Zancen gaskiya Peter Obi ɗan jam'iyyar PDP ne tun asali kuma idan ma akwai yiwuwar ya dawo jam'iyyar wanda muna fatan haka. Hakan bai kamata ya zama wata matsala ba," in ji Ibrahim Abdullahi, mataimakin sakataren watsa labarai na jam'iyyar PDP.
LP ta bai wa Peter Obi wa'adin sa'a 48
A farkon watan Yulin nan ne wani ɓari na jam'iyyar LP ya bai wa mutumin da ya yi mata takarar shugabancin ƙasar a 2023, Peter Obi, wa'adin sa'a 48 da, ko dai ya gaggauta ficewa daga jam'iyyar ko kuma ya bar jam'iyyar haɗaka ta ADC.
Ɓangaren Julius Abure na jam'iyyar Labour ne ya bai wa Peter Obi wa'adin a wata sanarwa:
"Jam'iyyar Labour Party ba ta cikin wannan tsari kuma ta nesanta kanta daga shirin haɗakar ADC," in ji mai magana da yawun ɓangaren na LP.
Sai dai kuma shugabancin jam'iyyar ƙarƙashin Nenadi Usman, ya yi watsi da wa'adin.
'Salon ɓadda-bami'
Malam Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano wato CAS, ya ce irin wannan saɓata-juyata abu ne da ƴan siyasa ke yi domin ɓadda-bami.
"Ƙoƙarin lissafi ne da dukkan ɓangarorin ke yi na ganin sun samu nasara ba tare da ƴan'uwansu jam'iyyu sun fahimci wurin da aka sa gaba ba."
Dangane kuma da jam'iyyar da Peter Obi zai tsaya a ciki Malam Kabiru Sufi ya ce har yanzu babu tabbas kan jam'iyyar da zai yi takarar.
"Har yanzu akwai buƙatar daidaita sahu ko kuma shirya yadda jam'iyyun hamayya za su tunkari jam'iyya mai mulki a kakar zaɓe mai zuwa saboda haka wannan sa-in-sa ɗin ya sa ba za ka iya cewa takamaimai ga wanda zai yi jagoranci a wannan jam'iyya ko waccan kuma hakan na ƙara nuna cewa ana ta lissafe-lissafe ne kuma duk inda aka ga akwai mafita to can ne za a karkata." In ji malam Kabiru Sufi.