Yaya maganin rage teɓa ke aiki a jikin ɗan'adam kuma ta yaya zai sauya alaƙarmu da abinci?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, James Gallagher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Lafiya
- Lokacin karatu: Minti 4
Yanzu mun ci kanmu a zamanin da ake shan ƙwayar magani domin a rage ƙiba.
Matakan da ake ɗauka kan yadda za a yi amfani da waɗannan ƙwayoyi, da alama su ne za su fayyace yadda rayuwarmu ta gaba za ta kasance.
Kuma dai, yayin da masu bincike ke ci gaba da ƙoƙari, tun sun fara kawar da maganar cewa marasa jajircewa ne kawai ke yin teɓa.
Sabuwar gwamnatin Labour a Ingila ta ce irin waɗannan ƙwayoyi za su iya taimaka wa masu teɓa wajen komawa wuraren ayyukansu, ta yadda ba sai gwamnati ta ci gaba da tallafa musu ba.
Ga wasu tambayoyi za mu so ku amsa su:
Shin teɓa abu ne da mutane ke haifar wa kansu saboda ba su iya zaɓa wa kansu abubuwan da suka dace ba? Ko kuwa matsalar ta kowa da kowa ce kawai dai mutane na buƙatar a yi dokoki ne game da abincin da suka kamata mu dinga ci?
Ko ƙwayoyin rage ƙiba ne suka fi dacewa idan ana maganar teɓa mai yawa? Shin ana amfani da ƙwayoyin ne wajen katange babbar matsalar da ta sa mutane ke yin ƙibar fiye da kima tun da farko?
Ba za mu iya ba ku duka waɗannan amsoshi ba - sun danganta ne da ra'ayoyinku game da ƙiba fiye da kima da kuma nau'in ƙasar da kuke zaune. Amma akwai wasu abubuwa kuma da suka kamata a yi tunani a kai.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Teɓa abu ne da ake gani ƙarara, ba kamar larurori ba kamar ƙarancin ƙarfin jini a jiki, kuma aka daɗe ana tsangwamar masu ita. Rudanci (yawan cin abinci) na cikin abin da addinin Kiristanci ya yi hani da shi.
Bari mu duba ƙwayar Semaglutide da ake sayarwa da sunan kamfanin Wegovy domin rage ƙiba. Tana kwaikwayon sinadarin aika saƙo a jiki ne da ake samu idan muka ci abinci waɗanda ke yaudarar ƙwaƙwalwarmu cewa a ƙoshe muke, saboda haka za mu rage cin abinci.
Abin da hakan ke nufi shi ne, sauya sanadari ɗaya "ya sa kun sauya alaƙarku da abinci", a cewar Farfesa Giles Yeo, wani ƙwararre kan teɓa a Jami'ar Cambridge.
Haka nan, dukkan masu ƙiba fiye da kima na da "ƙarancin wasu sinadarai, ko kuma dai ba su aiki sosai", in ji farfesan, abin da ke yawan saka su jin yunwa idan aka kwatanta da sirara.
Ba lallai hakan ta yiwu ba a shekara 100 da suka wuce lokacin da babu abinci mai yawa - inda mutane kan ci abinci mai yawa saboda ba lallai su same shi ba gobe.
Ƙwayoyin gadonmu ba su sauya ba tsawon ƙarni guda, amma yanzu muna zaune a duniyar da ta ba mu damar sayen abinci mai ɗauke da ma'aunin kuzari mai yawa.
Irin waɗannan sauye-sauyen sun samu ne a shekaru 50 na ƙarshen ƙarni na 20, abin da ya sa masana kimiyya ke kiran sa “obesogenic environment” - wato ƙarnin da ke ingiza mutane cin abinci maras cikakken inganci kuma ba su son motsa jiki.

Asalin hoton, Getty Images
Bincike ya nuna cewa duk mutum ɗaya cikin huɗu a Birtaniya na da ƙiba fiye da kima.
Ƙwayar Wegovy na taimaka wa mutum rage kashi 15 na ƙibar da ta ƙaru a jikinsa.
Rage ƙibar na da amfani wajen rage haɗarin kamuwa da bugun zuciya, da ciwon siga aji na 2, da katsewar numfashi yayin barci.
Sai dai Dr Margaret McCartney, wata likita a birnin Glasgow, ta yi gargaɗi: "Idan muka ci gaba da ba su ƙarfin gwiwar samun teɓa, to fa za mu ci gaba da neman waɗannan ƙwayoyin magani,"
Hujjoji sun nuna cewa idan aka daina yi wa mutum allurar zai ci gaba da jin yunwar sannan kuma ƙibar za ta dawo.
Mun san cewa ana fara tara teɓa ne tun daga yarinta. Duk yaro ɗaya cikin biyar kan tara teɓa fiye da kima tun kafin ya fara zuwa makaranta a Birtaniya.
To kuna ganin ya kamata mu shawo daƙile matsalar zamantakewarmu da ke jawo ƙibar ko kuma kawai a dinga bai wa masu ƙibar magani idan ta fara zama matsala? Ko ya kamata gwamnati ta ƙara matsa ƙaimi kan kamfanonin abinci da kuma abin da muke ci?
Ko ya kamata mu koma irin Japan (ƙasa mai arziki da ba a yin teɓa sosai) don mu dinga cin abinci kaɗan? Ko kuma mu dinga ƙayyade yawan ma'aunin kuzarin da muke ci?
Farfesa Yeo ya ce idan muna son sauyi to "dole sai mun haƙura da wani abin, sai mun sallama wani ɓangare na 'yancinmu," amma "ba na jin mutane sun amince da hakan tukunna".
A Ingila, akwai tsarin yaƙi da teɓa - 14 daga cikinsu a cikin shekara 30, amma kuma babu wani kyakkyawan sakamako.
Cikinsu akwai rukunin wayar da kai har sau biyar a rana domin neman a dinga cin 'ya'yan itatuwa da kayan marmari, da saka lissafi a jikin kayayyakin abinci na ma'aunin kuzari wato colorie, da hana tallata abincin da ba su da inganci ga lafiyar yara sosai.
"Kamfanonin abinci na cin riba, kuma abin da suke nema kenan - babban fatana shi ne ƙwayoyin rage ƙiba su taimaka wa mutane daina cin abinci marasa inganci ga lafiya," kamar yadda Farfesa Naveed Sattar ya bayyana na Jami'ar Glasgow.
A yanzu dai muna ta fata ne kawai. Babu ƙwayoyin da yawa a duniya saboda tsadarsu.
Amma ana sa ran za a samu sauyi sosai cikin shekara 10 masu zuwa. Sababbin magani kamar tirzepatide na kan hanya kuma za a samu damar samar da maganin daga wasu kamfanoni da za su fi sauƙi.
An shiga irin wannan yanayi lokacin da aka fito da ƙwayoyin saukar da jini, inda suka yi tsada kuma ake bai wa mutane 'yan ƙalilan.











