'Babachir Lawan ba shi da hujjar sukar zaben Kashim Shettima a matsayin mataimakin Tinubu takarar Tinubu'
Zaben 2023: Babachir Lawan ba shi da hujjar sukar matakin zaben Kashim Shettima a matsayin mataimakin Tinubu

Asalin hoton, AFP
Wasu na hannun daman ɗan takarar shugaban ƙasa na jam`iyyar APC a Najeriya sun ce tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ba shi da hujjar sukar matakin ɗaukar Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakin Bola Ahmed Tinubu da aka yi.
Mista Babachir ya soki Bola Tinubu kan ɗaukar Kashim Shettima, yana cewa matakin na iya janyo wa jam’iyyar ta APC faɗuwa zaɓen 2023.
Sai dai wasu makusantan Tinubu sun ce Babachir Lawal na cikin kwamitin da ya zaɓo mutanen da aka gabatar wa tsohon gwamnan Jihar Legas din, inda ya ɗauki ɗaya a matsayin mataimakinsa, bayan sun yi la'akari da fa'idar da ke tattare da kowannensu.
Sanata Abu Ibrahim na cikin kwamitin, ya kuma shaida wa BBC cewa suna zaune tare da Babachir Lawan aka yanke shawarar a kan cewa ya kamata akai mukamin mataimakin shugaban kasar na Tinubu zuwa yankin arewa maso gabas.
Ya ce a tattaunawar da aka yi sai da aka tabo batun addini, to amma daga karshe aka ce a samo wanda zai sa a ci zabe kawai.
"Ba wai na ce Babachir ya yi ba daidai ba ne don ya yi magana, kawai dai ya kamata ya yarda da cewa ya san abin da ya faru," in ji Sanata Ibrahim.
Sanata Abu Ibrahim ya ce ya kamata ya kasance a cikin masu kashe wuta ba masu hura ta ba.
"Babachir zai iya kashe wutar da aka hura, ma’ana zai iya sanya baki komai ya lafa, saboda yana daga cikin manya a bangaren mabiya addinin Kirista, don haka idan har zai zauna ya yi musu bayanin komai dalla-dalla, to za su fahimta," a cewarsa.
Sanata Abu Ibrahim ya kara da cewa “Batun cewa ai za mu fadi zabe wanda Babachir Lawan yake muku, mu kam ba za mu fadi zabe ba saboda mutane da dama suna son Tinubu ganin cewa shi ya taimaka wa Shugaba Buhari ya ci zabe."
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriyar, Babachir Lawal, ya ce zabin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Bola Ahgmed Tinubu ya yi na Musulmi a matsayin mataimakinsa gagarumin kuskure ne.
Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, inda yake ganin illar hakan kasancewar Tinubun shi ma Musulmi ne.










