Ibrahim Masari: Zan yarda a sauya sunana da wanda ya fi ni cancanta

Bayanan bidiyo, Bidiyon hira da Ibrahim Masari

Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Ibrahim Masari ya shaida wa BBC cewa a shirye yake a sauya sunansa da wani wanda ya fi shi cancanta idan Bola Ahmed Tinubu da kuma shugaba Muhammadu Buhari suka ga akwai bukatar haka.

Mataimakin Tinubun ya ce ya zuwa yanzu "ta tabbata jam'iyyar APC ta tsaida 'yan takara Musulmi da Musulmi ke nan a matsayin shugaban kasa da mataimaki".

Ya ce "ba na tsammanin akwai irin wannan banbancin addini kamar yadda ku 'yan Jarida ku ke zuzuta shi".

Da yake magana kan zaben shekara ta 2023 kuma, Ibrahim Masari ya ce ba ya shakkar APC za ta kayar da babbar jam'iyar adawa ta PDP.