APC: Shugaban jam'iyyar Abdullahi Adamu ya ce ya ɗauki alhakin matsalolin da ta shiga

.

Asalin hoton, OTHERS

Shugaban jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ya ɗauki alhakin duk matsalolin da jam'iyyar tasu ta shiga musamman game da zabukan fitar da gwani da aka kammala a farkon watan Yuni.

Shugaban na mayar da martani ne kan matakin da jam`iyyarsu ta ɗauka na miƙa sunan Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ga hukumar zaɓe a matsayin ɗantakarar sanata mai wakiltar Mazaɓar Yobe ta Arewa maimakon Bashir Machina, wanda ya ci zaɓen fitar da gwani na mazaɓar.

Cikin wata hira ta musamman da BBC Hausa, Sanata Adamu ya ce "ni a matsayina na shugaba, duk abin da ya faru tun daga lokacin da Allah ya ba ni shugabancin APC, na ɗauki laifi".

Ya ƙara da cewa: "Idan ban ɗauki laifi ba wa za zan ɗora wa laifin? Ni ne shugaba, kuma ai wuta ake so a kashe."

To ko waɗanne matsaloli ne APC ke ciki?

Zan kai APC kotu - Bashir Machina

Ahmed Lawan da Bashir Machina
Bayanan hoto, Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan (hagu ) da Bashir Machina

Daga cikin manyan matsalolin da APC ke ciki a yanzu har da batun karɓe tikitin takarar sanata daga hannun Bashir Machina, wanda shi kuma ya lashi takobin bin kadin lamarin a gaban kotu.

Da wakilin BBC Ibrahim Isa ya tambayi Abdullahi Adamu game da lamarin, sanatan ya yi kakkausan gargaɗi ga Machina cewa ya yi hattara saboda "maganganun da yake fadi sun fara neman su yi yawa".

A cewarsa: "Ni a matsayina na shugaba na san babu wata doka da jam'iyya ta karya, domin babu wata doka da ta ce idan ka shiga wata takara ba za ka shiga wata ba. Don haka ba dokar da ta hana shi ko ta hana kowa ma.

"Shi fa ɓarawo idan ba ka iya kama shi ba sai ya kama ka. Machina, ya yi hattara zuwa yanzu."

Tun farko Abdullahi Adamu ya yi iƙirarin cewa Ahmad Lawan ya sayi fom kuma ya shiga zaɓen fitar da gwani na sanatan Yobe ta Arewa. Sai dai Bashir Machina na cewa shi kaɗai ya tsaya takara a zaɓen.

Tun bayan rashin nasara da ya yi a zaben fitar da gwani na takarar shugaban ƙasa a APC, aka fara dambarwa kan Sanata Ahmad Lawan kan yiwuwar kasa komawa majalisar bayan ya shafe fiye da shekara 20 yana wakiltar al'ummarsa a Majalisar Wakilai da ta Dajjitai.

Zaɓen ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa

Bola Tinubu da Kabiru Masari

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto, Bola Tinubu (dama) ya zaɓi Kabiru Masari a matsayin abokin takararsa na shugaban ƙasa, duk da wasu na cewa "na riƙo" ne

APC na ci gaba da shan suka game da yadda jam'iyyar ta kasa ɗaukar mataimakin ɗan takararta na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda sai a ranar da wa'adi ke cika sannan ta miƙa sunan Kabiru Masari.

Sai dai rahotanni da kuma masu sharhi na ganin cewa ɗan takarar "na riƙo" ne yayin da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ke ci gaba da tattaunawa don sauya sunan mataimakin a nan gaba kamar yadda hukumar zaɓe INEC ta ba su dama.

"Babu wata doka da ta ce dole a kawo mataimaki [na ɗan takarar shugaban ƙasa] na take, to mece ce damuwar?

"Don an kai wani lokaci ba mu fitar da ɗan takara ba iyawa ce, don mu daddale, mu fito da mutumin da zai karɓu a wajen al'ummar da za a nemi ƙuri'unsu."

Sauran jam'iyyu kamar NNPP ta Rabiu Kwankwaso da LP ta Peter Obi duk sun miƙa sunayen mataimakan ne na riƙo yayin da suke ci gaba da tattaunawa don yin "maja" kafin babban zaɓen na 2023.

Bashir Machina ya ce ya wallafa takarda a shafukan intanet wadda ya ce ya aike wa APC kan tuntuɓar da aka yi masa ko yana nan kan takararsa, inda ya amsa da cewa bai janye ba kuma yana kan takararsa.

Ya ƙara da cewa Ahmad Lawan bai tuntuɓe shi ba baki da baki ba, don haka yana nan kan bakansa kamar yadda jama'a suka zaɓe shi.

Ficewar 'yan siyasa daga APC

Wata matsala da jam'iyyar ke ciki ita ce ta ficewar wasu 'yan siyasa daga cikinta zuwa jam'iyyun adawa, abin da shugaban jam'iyyar ya ce ba abin mamaki ba ne saboda "mana cikin matsala".

A Kano misali, jam'iyyar NNPP ta tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ta kwashi 'yan APC da yawa, cikinsu har da jiga-jigai kamar Kawu Sumaila da Abdulmumini Jibrin.

"In na ce babu wanda ya bar APC na yi ƙarya...ba shakka akwai waɗanda suka shiga zaɓe ba su samu ba kuma sun ce za su bar jam'iyyar," a cewar Abdullahi Adamu.

Sai dai ya ce yawan waɗanda suka bar APC ba su kai yawan mutanen da 'yan jarida ke faɗa ba.

Presentational grey line