'Yan Najeriya na jinjina wa mace tilo da ta yi nasara a zaben fitar da gwani na gwamnoni

Binani Facebook

Asalin hoton, Binani Facebook

Lokacin karatu: Minti 3

Cikin wannan makon ne jam'iyyun siyasa a Najeriya suka gudanar da zabukan fitar da gwani na wadanda za su kara da sauran takwarorinsu na sauran jam'iyyu a zaɓukan 2023.

Manyan jam'iyyun kasar na APC mai mulki da babbar jam'iyyar adawa ta PDP suna daga cikin waɗanda nasu zabukan fitar da gwanin suka ja hankali a ƙasar.

Wani abun birgewa a zabukan shi ne yadda mace daya tilo ta samu nasarar takarar kujerar gwamna. a cikin duka jam'iyyun babu wata mace da ta samu nasara bayanta.

Sanata Aisha Dahiru Ahmed Binani wadda ta fito daga jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, ta samu nasarar ne a karkashin inuwar jam'iyyar APC da ke mulki.

Shugaban kwamitin zaben Malam Gambo ne ya sanar da nasarar da ta samu a Yola inda aka yi zaben, ta kuma yi nasara da ƙuri'a 430.

Abin da ya girgiza mutanen Najeriya ya kuma mayar da nasarar da ta samu ta musamman shi ne, yadda ta kayar da manyan ƙusoshin siyasa da suka yi suna a jihar ko ma a ƙasar.

Ta kara da gwamnan da ya fadi zabe a 2019 wanda ya yi wa'adi guda na shugabancin kasar Muhammadu Jibrilla Bindow wanda shi ne ya yi na uku a takarar da ƙuri'a 103.

Ta fafata da tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Nuhu Ribado wanda ya yi na biyu da ƙuri'a 288.

Wannan ya sa 'yan Najeriya da dama suka riƙa jinjina mata a kafafen sada zumunta na kasar kama daga Facebook zuwa Twitter.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Halimah wadda aka fi sani da @NextDoorDoctor daya ce daga cikin masu wadanda suka bayyana ra'ayinsu kan nasraar ta Binani, ta ce "Ina taya Sanata Aisha Binani murnar lashe zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC da aka yi.

"Hakika ina fatan za ta zama mace ta farko da za ta zama gwamna a Najeriya."

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Arabi M.Bello cewa ya yi, "Yayin da kake yi wa mutanenka abin arziki, su ma za su biya ka a ranar ramuwa. Ina taya ki murna Sanata Aisha Binani tare da tawagar yakin neman zabenki."

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Mr Kermit wato @O_ssai ya ce, "Yankin arewa shi ne a baya, suna dakile yunkurin mata na fafatawa da su... amma yankin arewacin ne kadai ya yi kokarin kawar da shingen hana mata dama."

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Alli-Balogun H.Lekan wanda ake kira @allibaloo ya tofa albarka cin bakinsa inda ya ce "Nasarar da Aisha Binani ta yi kan Bindow da Nuhu ta kara dawo da muhawara kan tasiri da kuma rawar da wakilan jam'iyya ke takawa.

"Abu ne mai wuya ka kashe kudi sama da gwamnan da aka kayar kasa da shekara hudu, don haka ba maganar kudi ba ce ko wakilan jam'iyya."

Wannan layi ne

Wace ce Aishatu Binani?

An haifi Aishatu Dahiru Ahmed a shekarar 1971. Kuma sanata ce a majalisar dattijan Najeriya a yanzu haka.

Ta taɓa zama ƴar majalisar wakilai da ke wakiltar Yola ta Arewa da Yola ta Kudu da Girei a ƙarƙashin jam'iyyar PDP daga 2011 zuwa 2015.

Ta yi karatunta a Najeriya da Ingila. Ita ce shugabar kwamitin Muradun Ci gaba Mai ɗorewa ta majalisar dattijan.

Binani tana da aure tsawon shekara 15, kuma mijinta shi ne tsohon shugaban hukumar kula da ilimi a matakin farko Ahmed Modibbo Mohammed. Tana da ƴaƴa biyu.

Binani wadda ita kadai ce mace yar takara gwamna, ta zama mace ta farko da ta fara samun tikitin takarar gwamna a wata babbar jam'iyya a jihar Adamawa.

A 2014, Sanata Aisha Alhasan wadda aka fi sani da Mama Taraba, ta samu irin wannan nasara a jam'iyyar APC a jihar Taraba, sai dai ta yi rashin nasarar a hannun abokin karawarta Gwamna Darius Ishaku a babban zabe.

Kungiyoyin cikin gida da waje na ta kiraye-kirayen yadda za a rika bai wa mata a Najeriya damar damawa da su a duka matakan gwamnatocin kasar, sai dai za a iya cewa har yanzu wannan hakar ba ta cimma ruwa ba.

Wannan layi ne