Abin da ƴan Najeriya ke cewa game da daliget a shafukan sada zumunta

Tun bayan da aka fara zaben fitar da gwani a jam'iyyun Najeriya, kasuwar daligets ta buɗe inda suke ta cin karensu babu babbaka.
A irin waɗannan lokuta daligets kan samu kuɗaɗe daga wajen ƴan takara, wanda wasu ke cewa harka ce ta "daga bana sai baɗi", amma a zahiri ana nufin daga wannan shekarar sai kuma bayan wasu shekaru hudun.
Sannan a wannan kakar zaɓen fitar da gwanin na 2022 gabanin zaɓukan 2023, ba aljihun daligets ba ne kawai suka cika, har da sake samun suna da yin tashe a cikin al'umma, wataƙila saboda tasirin kafofin sada zumunta.
Tun daga farkon wannan makon ake ta tattauna batun daliget a shafuka daban-daban, wanda hakan yana daga cikin abin da ya ƙara fito da su da ayyukansu a idon duniya.
Yayin da wasu ke ta yi wa daliget wasa da raha da tsokanarsu da nuna yadda lokacin ƙarfin ikonsu ya zo, wasu kuma zagin su da zargin su da "kwaɗayin abin duniya suna ƙin zaɓar waɗanda suka dace suke yi."
Me ake cewa a shafukan sada zumunta?
Kalmar #deligates na daga cikin wacce aka fi ambatarta sosai a shafukan sada zumunta a Najeriya a baki ɗayan wannan makon.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
@AishaYesufu ta rubuta cewa: "Idan daligets ba su zaɓar muku ƴan takarar da kuke so ba, to ku rama ta hanyar ƙin zaɓar jam'iyyarsu a manyan zaɓuka. Ku gaya wa jam'iyyun cewa ba za ku zaɓe su ba!
Idan kuka ci gaba da cewa dole Jam'iyya kaza da kaza ce za su yi nasara, to waɗannan daligets ɗinza su ci gaba da zaɓar muku da ƴan takarar da ba kwa so."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
@SavvyRinu ya ce: Babu wata dimokradiyya da ake bi a tsarin wakilan jam'iyyu. Daligets ba za su taɓa yin biyayya ga Najeriya da al'ummarta ba.
Biyayyarsu ga masu hannu da shuni ne da shugabannin da suka naɗa su a matsayin daliget tun farko."
Ga sauran kamar haka:
Oke Umurhohwo @OkeStalyf ya ce: "Ka ji tsoron daliget kamar yadda za ka ji tsoron Delilah 😂."
MUSTAPHA @angry_ustaaz ya ce: "A da dai bai wa daliget cin hancin nan a ɓoye ake yi, amma abin da ban tsoro ganin yadda ba a ma ɓoye shi a yanzu.
"Wato a taƙaice dai ba maganar ɗan takara nagari ko mugu ake yi ba, magana ce ta wanda ya fi ba da kuɗi, me zai hana su yi ta sace kuɗaɗen al'umma?
Wani ɗan Najeriya mai sharhi kan al'amuran yau da kullum kuma malamin wata jami'a a Amurka, Farooq Kperogi ya rubuta a Facebook cewa:
"Zaɓen fitar da gwani da ake yi a faɗin Najeriya wanda daliget-daliget ke sayar da ƙuri'unsu a bayyane ga wanda ya fi ba su kuɗi mai yawa, shi ne yanayi mafi ƙasƙanci a siyasar Najeriya.
"Ban taɓa ganin wani abu makamancin haka ba. Kenan dai a 2023 za mu samu shugabannin da suka sayi daliget ba ko kunya don samun muƙamansu. Me zai faru sakamakon hakan?"

Wasu ƴan takara sun karɓo kuɗaɗensu bayan shan kaye
Wasu rahotanni sun ce tuni wasu ƴan takarar da suka sha kaye a zaɓukan fitar da gwanin suka karɓo kuɗaɗensu a wajen daliget din.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ɗan tsohon matakimakin shugaban Najeriya Namadi Sambo, ya bi daliget ɗin har gida ya karɓo kuɗaɗen da ya ba su, bayan da mafi rinjaye su azaɓi abokin karawarsa.
Adam Namadi wanda ke takarar ɗan majlisar wakilai a ƙaranmar hukumar Kaduna ta Arewa, ya nemi daliget din su mayar masa da naira miliyan bibbiyun da ya ba su kafin zaɓen.
Shi mutumin da ya so yi wa jam'iyar PDP takarar gwamna a Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya a zaben 2023, Sanata Shehu Sani, ya ce daliget biyu ne suka zabe shi, kuma ko sisi bai ba su ba.
Sanata Sani ya bayyana haka ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Alhamis.
A cewarsa, bai san wadanda suka zabe shi ba, yana mai cewa daliget kusan 300 ne suka kira shi suna masu bayyana masa cewa suna cikin mutum biyun da suka zabe shi.
Ya taya Honorabul Isah Ashiru, mutumin da ya lashe zaben.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3

Wane ne daliget?
Daliget shi ne mai kaɗa ƙuri'a a zaɓen fitar da gwani na jam'iyya.
Ƴaƴan jam'iyya a matakan mazaɓu na ƙanana hukumomi su ne suke zaɓar daliget daga tsakanin su.
Sai dai ana ganin duk jihar da ake da gwamna a jam'iyya mai ci, to ana zargin gwamna shi ke da ruwa da tsaki na zaɓar daliget ɗin.
Daliget biyar-biyar kawai ake zaɓa daga kowace mazaɓa don yin zaɓukan fitar da gwani a zaɓen gwamnoni da ƴan majalisar dattijai da ƴan majalisar wakilai da ƴan majalisar dokoki ga jam'iyyar APC.
Amma ga jam'iyyar PDP, mutum uku ake zaɓa daga kowace mazaɓa.












