Zaben 2023: Yadda ‘ya’yan gwamnoni da wasu manyan ‘yan siyasa ke fafutikar gadar iyayensu a Najeriya

..

Yayin da babban zaben Najeriya yake karatowa, 'yan siyasa da jam'iyyu daban-daban suna ci gaba da daura damarar yadda za su karbu a wajen masu kada kuri'a.

Tun kafin hukumar zaben kasar, INEC, ta fitar da jadawalin zabukan shekarar 2023, 'yan siyasa suka soma kamun-kafa da gagganawa da zummar samun magoya baya a siyasance domin tunkarar zabukan da ke tafe.

Tuni dai shugabannin da ke kan mulki (wadanda tsarin mulkin Najeriya ya ba su damar sake tsayawa takara) da tsoffin 'yan siyasa da ma sabbin-shiga suka soma gudanar da taruka da tattanawa da masu ruwa da tsaki da abokan harkokinsu na siyasa, da ma 'yan wasu jam'iyyu a yunkurin samun nasara a zabuka masu zuwa.

Sai dai wasu daga cikin mutanen da suka ja hankalin 'yan kasar a wannan fafutika su ne 'ya'yan gwamnoni da wasu manyan 'yan siyasa da su ma suka yunkuro domin tsayawa takara a zabukan 2013.

Ko da yake a baya wasu 'ya'yan gwamnoni da ma shahararrun 'yan siyasa sun nuna sha'awarsu ta tsayawa takara, amma a wannan karon adadinsu ya karu, abin da masana harkokin siyasa ke kallo a matsayin yunkuri na gadar iyayensu.

Wasu daga cikin 'ya'yan gwamnoni da aka ga fastocinsu na tsayawa takara sun hada da Bello Elrufai, dan gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir Elrufai da ke neman takarar dan majalisar dokokin tarayya a jam'iyyar APC.

Akwai Mustapha Sule Lamido, dan tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, da ke son tsayawa takarar gwamna jihar tasu duk da a baya yayin wata hira da BBC, Sule Lamido ya ce ba laifi bane idan ya goyi bayan ɗansa ya tsaya takara inda ya ce duk wani mahaifi yana son ɗansa.

Sannan da Abba Ahmad Sani Yariman Bakura, dan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, shi ma yana son tsayawa takarar dan takarar majalisar tarayya.

Kazalika akwai Usman Mamuda Shinkafi, dan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Mamuda Aliyu Shinkafi da ke neman takarar dan majalisar dokokin jihar ta Zamfara da kuma Idris Abolaji Abiola-Ajimobi, dan tsohon gwamnan Oyo, Abiola-Ajimobi .

Baya ga wadannan kuma a baya-bayan nan aka jiyo James Ibori tsohon gwamnan Delta yana rokon delegets na jihar da cewa su mara wa 'yarsa baya a neman kujerar 'yar majalisar wakilai da take yi.

Masana harkokin siyasa dai na ganin irin wannan mataki da 'ya'ya da kuma dangin gwamnoni da manyan 'yan siyasa suke dauka na fitowa takara a matsayin maras alfanu ga dimokuradiyya.

Dr Tukur Abdulkadir, Malami a Tsangayar Koyar da Harkokin Siyasa ta Jami'ar Jihar Kaduna, ya shaida wa BBC cewa wadannan 'yan siyasa suna amfani da 'ya'yansu su domin ci gaba da zama masu muhimmanci a fannin siyasa da mulki ko da bayan sun sauka daga mukamansu ne.

A cewarsa, hakan yana nuna tabarbarewar shugabanci da kuma tasirin kudi a fannin siyasa.

"Wannan al'amari ne da ke nuna tasirin masu fada a ji, irin su gwamnoni da karfin kudi a fannin siyasa. Galibin wadannan 'yan siyasa suna so su ci gaba da tasiri ne kawai ba don kashin kansu ba domin ci gaban al'umma ba.

"Sau da dama za ka ga 'ya'yan da ake so su tsaya takara ba su da wani tagomashi da kwarjini, hasalima ba su san al'ummar da suke son wakilta ba saboda yawancinsu ba a Najeriya suka yi karatu ba, amma su ne suke zakewa wajen ganin sun gaji mahaifansu," a cewarsa.

Dr Abdulkadir ya kara da cewa a baya ba a san irin wannan dabi'a ta 'yan siyasa ba amma yanzu son kai ya sa wasu manyan 'yan siyasa suna yin duk abin da za su iya wajen ganin 'ya'yansu sun gaje su.

A hannu guda kuma, wani nazari da BBC Hausa ta yi ya gano cewa ba manyan 'yan siyasa ba kadai, hatta kananan 'yan siyasa a matakin kananan hukumomi sun fara bin irin wannan al'ada ta son dora 'ya'yansu a takara.

Misali akwai shugabannin jam'iyya dq mqsu ruwa da tsaki na kananan hukomomi da 'ya'yansu suka fito ko dai takarar 'yan majalisar jiha ko tarayya.

Dr Tukur ya kara da cewa: "Idan ka lura za ka ga cewa tsoffin shugabanni irin su Alhaji Shehu Shagari da Abdulkadir Balarabe Musa da Abubakar Rimi ba su dauki irin wannan mataki ba, duk da yake suna da 'ya'ya.

"Amma yanzu akwai wadanda ake tuhuma da lafin cin hanci su da 'ya'yansu amma su ne suke so a bai wa 'ya'yan nasu damar mulkar jama'a," in ji shi.

Ya kara da cewa akwai bukatar masu zabe su tashi tsaye su yi fatali da duk dan wani dan siyasa da ba shi da tarihin bautawa jama'a idan ya nemi wakiltarsu.

Babban abin tambayar shi ne ko idan Najeriya ta mayar da shugabanci irin na siyasar gado, za a samar da shugabannin da taimakon talaka ne a ransu ko kuwa cimma bukatar rayukansu ne a gabansu?