Ohaneze na son shugabancin Najeriya ya koma tsarin karba-karba

Al'ummar Ibo

Asalin hoton, Other

A Najeriya, kungiyar kare muradun al'ummar Igbo zalla ta ''Ohanaeze Ndigbo'', ta nemi a sa tsarin karba-karba na shugabancin kasar zuwa shiyyoyi 6 na kasar a kundin tsarin mulki, maimakon yadda wasu jam'iyyun ke karba-karbar tsakanin Kudu da Arewa.

Kungiyar al'ummar Igbon na ganin ta haka ne kawai za a tabbatar da dai-daito, wajen ganin kowanne sashe na kasar ya samar da shugaban kasa.

Mukaddashin shugaban sashen matasa na kungiyar ya shaida wa BBC cewa, wannan shawara ce da ta yi daidai da muradunsu na ganin cewa Najeriya ta ci gaba da kasancewa dunkulalliyar kasa guda.

Ya ce," Idan har ba a sa irin wannan tsari na karba-karbar shugabancin Najeriya a kundin tsarin mulki ba, za mu iya karewa da wani tsari irin na wanda ya fi kudi ya kasance da iko a kodayaushe."

Mukaddashin shugaban sashen matasan kungiyar ta Ohaneze, ya ce yana ganin yin hakan ba zai yi kyau ga hadin kansu a matsayin al'umma ba.

To sai dai kuma a nasu bangaren, wasu dattawan arewacin Najeriya na ganin wannan wata shawara ce da ya kamata al'ummar Igbon su gabatar da ita ga sauran 'yan Najeriya ta hanyar da ta dace.

Dakta Hakim Baba Ahmed, shi ne kakakin kungiyar dattawan arewacin Najeriya, wanda ya shaida wa BBC cewa matakin kungiyar ta Ohaneze a kan hanya yake, amma kuma ya kamata su je majalisar wakilai da ta dattawan kasa su kai kokensu kan wannan batu.

Ya ce," Shi batun karba-karba an yi shi ne a lokacin da kasar ke cikin babbar matsala, to yanzu wannan lokacin ya wuce, to amma idan har suna da hujja mai karfi to sai su kai inda ake gyara."

Dakta Baba Ahmed, ya ce batun karba-karba na da fa'ida da kuma rashin fa'ida, fa'dar ita ce ya yi amfanin a wani lokacin da kasa ke cikin matsala sosai, ana ta hayaniya Abiola ya ci zabe ba a ba shi ba da dai sauransu, to a nan ne aka ce a raba batun karbar mulki a kasar inda idan kudu ta yi sai arewa ta karba.

Ya ce kuma wannan mataki ba wai an sanya shi a cikin tsarin mulki na kasa ba ne, shi tsarin mulkin kasa ya ce duk abin da za a tafiyar da shi na hakkin jama'a to a tabbatar kowa na da kashi a ciki in ji shi.

Dakta Baba Ahmed, ya ce " A bari 'yan Najeriya su zabi wanda suke ganin shi ra'ayinsu ya fi raja'a a kai, sannan a bari kowa ya fito ya nema, idan Igbo na son ya yi mulkin Najeriya, to ya fito ya yi damara kamar yadda kowa ke yi."

Al'ummar Igbo a Najeriya dai sun jima suna kiran da a sanya tsarin karba-karbar shugabancin kasar tsakanin shiyyoyi shida na kasar cikin tsarin mulki.