'Yan Najeriya da ke son hadewar Kwankwaso da Peter Obi a inuwa daya

Asalin hoton, Other
'Yan Najeriya sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu kan batun hadewar dan takarar shugaban kasar a jam'iyyar NNPP Dr Rabi'u Musa Kwankwaso da na jam'iyyar Labour Peter Obi.
Muhawara kan batun hadewar tsofaffin gwamnonin na jihohin Kano da Anambra ta mamaye shafukan sada zumunta da muhawara a ranar Asabar.
Hakan ya faru ne bayan wata hira da BBC Hausa ta yi da Sanata Kwankwaso, inda ya bayyana cewa suna tattaunawa da takwaran nasa na Labour Party, LP, don yiwuwar hada gwiwa a zaben 2023.
A cewarsa "gaskiya muna magana da shi Peter Obi, ko kuma ma in ce kwamiti yana aiki domin ya duba dukkan abin da ya kamata (kan hada gwiwa da shi), kuma abokai da 'yan uwa suna zuwa suna yi mana magana kan batun.
Shafin Twitter ya dauki zafi da muhawara inda maudu'ai irin su #Kwankwaso da #PeterObi da #BBCHausa da #NNPP da kuma #LP suka dinga tashe sau dubbai.
A Facebook ma ba ta sauya zani ba, domin kuwa batun "majar" manyan 'yan siyasar biyu daga arewa da kudancin kasar ne ya mamaye muhawarar dandalin.
Wace wainar ake toyawa a soshiyal mediya?
Yawanci mutanen da suka fi yin tsokaci kan lamarin matasa ne, za a iya cewa daga 'yan shekara 18 har zuwa 50.
Sannan daga kowane bangare na kasar nan arewa da gabas da yamma da kudu kowa ya saka baki.
Mafi yawan mutane suna fatan wannan lamari ya kasance, don a ganinsu Kwankwaso da Obi ne gamayyar da ta fi dacewa da "ceto Najeriya daga halin da take ciki."
Sannan wasu na ganin su ne 'yan takarar da a yanzu suka fi tashe da farin jini da tsantsar gogewa, da sauran jini a jika da za su iya kai Najeriya ga ci idan har aka zabe su a shugaban kasa da mataimaki.
Amma hakan bai hana masu muhawarar kuma mayar da hankali ba kan idan har aka yi gamayyar to wace jam'iyyar za a yarda a hadu a karkashinta, kuma waye zai zama shugaba, waye zai yi mataimaki.
Mafi yawan 'yan arewa na ganin Dr Kwankwaso ne ya kamata ya zama shugaban kasar, Obi ka ya zama mataimakinsa, don a ganinsu ya fi shi tagomashi da karbuwa da kuma gogewa a fagen siyasa.
Masu irin wannan ra'ayin na dagewa cewa idan har Obi ya yarda da haka, to bayan sun kammala shekara takwas din da ake zatar musu sai shi kuma ya dare a matsayin shugaban kasa.
Sannan suna ganin Mista Obi ne ya kamata ya bar LP ya koma NNPP wajen Kwankwaso.
Jafar Jafar ya ce: "Kwankwaso ba zai taba barin jam'iyyar da ya gina daga wacce da ba a santa ba zuwa wacce ta karbu a kasa ta rushe ba, bayan yana da sanatoci da 'yan majalisa masu ci a arewacin kasar. Abu na biyu, komawa LP zai lalata kokarin duk 'yan takarar NNPP."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Shi ma wani mai suna @PoojaMedia cewa ya yi: "Kwankwaso gaba yake da Peter Obi a siyasance kuma dole ya yi duk mai yiwuwa don gamsar da shi a kammala wannan gamayyar da aka faro. Dalili shi ne don shi ya fara samun kwarin gwiwar bayyana hakan kafin jam'iyyar Labour."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Sai dai ga alama wannan dambarwa ita ce wacce ka iya kawo tarnaki a hadewar 'yan takarar waje daya.
Domin kuwa su ma 'yan yankin kudu na ganin Peter Obi ne ya fi cancanta da zama shugaban, alabashi idan shekarar 2031 ta zo sai "a taru a mara wa Kwankwason baya" shi ma ya zama shugaban kasar.
A ganin masu wannan ra'ayin, yanzu lokaci ne da ya kamata a ce mulkin kasar ya koma kudu, tun da dan arewa ne yake gab da kammala wa'adinsa ya sauka.
Kuma suna ganin ko a kudun ma, to kudu maso gabas wato yankin kabilar Ibo ne ya kamata a ce an bai wa, yankin da Mista Obi ya fito kenan.
@Chigoziealex ya ce "Bari na yi bayani sosai, da na ce mabiyan Kwankwaso su ba shi shawara ya zama mataimakin Peter Obi ba don na raina shi na ce hakan ba. Dole a mayar da mulki kudu saboda adalci. Ko gwamnonin arewa ma sun yarda da wannan tsarin."
Shi ma @mrsamie_ ya ce: "Kwankwaso muna rokonka ko ba don komai ba don a samu zaman lafiya da ci gaba a Najeriya da al'ummarta. Ka daure ka karbi rokonmu ka ji kukanmu ka zama mataimakin Obi. Ka ce kana wannan takara ce don farin cikinmu, to wannan abin muke bukata a yanzu mu yi farin ciki.
Cikin abin da ya kara wa masu irin wannan ra'ayi kwarin gwiwa har da kalaman da Kwankwaso ya yi a hirar tasa ta BBC Hausa.
Kwankwason ya ce hada gwiwarsu da Obi na da muhimmanci, musamman ganin cewa jam'iyyun APC da PDP ba su tsayar da dan takarar mataimakin shugaban kasa daga yankin kudu maso gabas ba - inda kabilar Igbo ta fi rinjaye.
Ra'ayi ya zo daya
A hannu guda kuma, akwai inda ra'ayoyin masu muhawarar suka zo daya, musamman ta inda suka dinga kambama cancantar mutanen biyu da irin azamar da suke ganin suna da ita wajen ciyar da Najeriya gaba.
An yi ta bayyana yadda Sanata Kwankwaso da Mista Obi suke da muradin bunkasa harkokin ilimi da tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa.
@UchePOkoyo ya ce "Idan har batun Peter Obi da Kwankwaso ya tabbata, fannin iliminmu zai farfado!
@FS_Yusuf_ ya ce "Idan har lamarin nan na majar Peter Obi da Kwankwaso ya kasance, to ku manta da yajin aikin ASUU. An daina kenan har abada. Ku je ku binciki ayyukansu a fannin Ilimi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
@thekaysie ya ce: "Peter Obi da Kwankwaso za su zamo wasu gagarabadau. Dukkansu sun hadu ta wajen inganta tattalin arziki kuma suna bayar da muhimmanci ga zuba jari da inganta ci gaban mutane. Idan wannan abu ya kasance, to lallai za su yi nasara."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4











