Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Filato: 'Na ga gawawwaki yashe a kan titi'
Akalla mutum 43 ne suka mutu cikin kwanaki biyu da aka shafe ana tashin hankali a ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar Filato a tsakiyar Najeriya, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC.
Sai dai rundunar yan sanda a jihar ta ce ta kama mutum tara da ake zargi da hannu a tashin hankalin da kashe-kashen na karamar hukumar Mangu.
Lamarin na zuwa ne bayan da sojojin Najeriya suka zargi makiyaya da kashe-kashe da satar shanu.
Kakakin hedikwatar tsaron Najeriya, Janar Edward Buba ya ce an tura sojoji na musamman zuwa yankunan da rikicin ya fi kazanta domin dakile bazuwar tashin hankalin.
Wata takaddama a kan shanu ce ta janyo tashin hankalin a Filato - yankin da ake yawan samun hatsaniya mai alaka da addini da kabilanci.
Wani mutum a garin Mangu ya fada wa BBC yadda aka kashe dan'uwansa mai shekara 63 a gidansa wanda daga baya aka cinna wa wuta.
"A yanzu da nake magana, yaransa shida suna kuka. Mun yi jana'izarsa tare da wasu gawawwaki 14," in ji shi.
Filato jiha ce da ke da cakuɗuwar al'umma musulmai da kuma mabiya addinin kirista.
Mazauna Mangu da ke da nisan kilomita 74 daga garin Jos, babban birnin jihar yanki ne da galibin mazaunansa Musulmai ne makiyaya da kirsitoci yan kabilar Mwagaful.
Wani bafulatani dan kasuwa Umar Haruna yana gida a lokacin da rikicin ya ɓarke ranar Talata, kamar yadda dan'uwansa Abdullahi Haruna ya ce.
Yana zaune a wata unguwa da ke garin da ke da mutane daga bangarorin biyu inda kuma aka kona gidaje 100, a cewarsa.
Haruna ya ce an kona masallatai bakwai da majami'u hudu.
Mai dakin Umar Haruna da yaransu ba sa gida lokacin da aka kai hari a gidan. Sun koma gidan ne a ranar Laraba.
"Lokacin da muka je gidan, mun ga gawarsa kone kamar dai yadda aka kone gidan. Ba mu samu yin wankan gawa ba saboda yadda gawar ta dagargaje," kamar yadda dan'uwansa ya bayyana.
Dagen Emmanuel Bello, daga kabilar Magwaful ya ce ya ga gawawwaki yashe a kan titi an kuma kona gidaje.
"Akwai wasu mutane da aka kashe aka kuma boye gawawwakinsu, muna ci gaba da kokarin nemo su," kamar yadda ya fada wa BBC.
Tashin hankalin ya soma ne bayan da wata saniya mallakin makiyaya ta tsere inda ta hau kan titi lamarin da ya fusata al'ummar Mwagaful.
An sa dokar hana fita - ba dare da rana amma matakin bai dakatar da tashin hankalin ba.
Mutane a yankin sun ce an tura sojoji zuwa Mangu amma sun tsaya a manyan tituna sannan kuma ba a ga keyarsu a yankunan da ake hare-haren ramuwar gayya ba.
Fiye da mutum 100 sun rasa rayukansu a hare-hare makamanta da suka faru a wani bangare na jihar ta Filato a jajiberin Kirsimeti.