Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya haddasa zanga-zangar da ta kai ga ƙona fadar hakimi a Filato
Waɗansu mata da suka yi da zanga-zanga a garin Bokkos da ke jihar Filaton Najeriya sun banka wa fadar hakimin garin na Bokkos wuta, sakamakon harzuƙa a kan kamen da jami'an tsaro ke yi a yankin, bayan wasu hare-hare da suka auku kwanan baya.
Sai dai bayanan da muka samu sun ce wani ɓangare ne na fadar aka ƙona, kuma ba a yi asarar rai ba sakamakon wutar.
Hukumomi a Najeriya sun tura ɗumbin jami'an tsaro zuwa yankunan da aka kai miyagun hare-haren jajiberen Kirsimeti waɗanda suka haddasa kisan kusan mutum 200.
Mata masu zanga-zanga a ranar Juma'a dai na zargin cewa sojoji sun shiga yankin suna tattara matasa, ba tare da wani dalili ba.
Wata shugabar matan yankin da lamarin ya auku a idonta, Laraba Lekshak, ta ce matan da suka tayar da hankalin sun tunkari fadar ne yayin da wasu shugabannin matan yankin ke ziyarar hakimin domin tattaunawa a kan hare-haren da suka auku a ranar jajiberin Kirsimeti.
'Mun shiga kenan za mu zauna sai muka ji ana ruwan duwatsu, ana fasa tagogi, da muka fita muka haɗu da matan sai muka fara ba su hakuri, amma ba su saurare mu ba. Ana cikin haka sai suka fito da fetur suka ƙona fadar, suka ƙona motoci, mu ma da ƙyar muka fita daga wurin,' in ji ta.
Ta ƙara da cewa shugabannin matan yankin sun yi Allah-wadai da abin da matan suka aikata kuma ba su goyin bayan matakin da matan suka ɗauka ba.
A cewarta 'idan abu ya lalace ba da faɗa ake magance shi ba ya kamata a zauna ne a teburin sasantawa.'
Shugabar matan ta yi kira da a nemi hanyyoyin da za a iya warware duk wata matsala cikin kwanciyar hankali ba tare da an tayar da jijiyar wuya ba.
Wani mai riƙe da mukami a garin na Bokkos, Chief Gabriel Loms ya ce ɓangaren ofisoshin fadar ne wutar ta shafa kuma ba a sami asarar rai ba. Ya kuma bayyana cewa sun ɗauki wannan lamari da matuƙar muhimmanci.
'Mu yanzu muna ba su hakuri ne, mu waɗanda ke riƙe da sarauta za mu zauna da sarki, mu kira matan domin mu tattauna, saboda mu ji shawarwarinsu na nemo hanyoyin da za a warware matsalolin.'
Ya ce akwai buƙatar mutanen yankin su ƙara hakuri saboda gwamnati ta fara ɗaukar matakai bayan hare-haren da aka kai kuma za a yi nazari domin tabbatar da hakan bai sake faruwa ba.
BBC ta yi yunƙurin ji ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar amma bai amsa kiran da aka yi masa ta waya ba.
Bayanai da aka samu sun nuna cewa an ƙara yawan jami'an tsaro da ke fadar hakimin na Bokkos da kuma sauran sassan yankin domin tabbatar da zaman lafiya.