'Kyautata wa kaina ya zame min babban ƙalubale'

Michelle Obama ta bayyana cewa ta sha wahala matuka da yawaita tunani mara kyau kafin iya gamsar da kanta kan yanayin halittarta da kuma tsoron da ke cike da zuciyarta, amma dole wannan matar ta "koyi nuna wa kanta soyayya, ta kuma so kanta yadda take."
A sabon littafinta, Matar tsohon shugaban Amurka ta bayyana cewa "ta tsani yadda take a ko-da-yaushe".Amma kuma sai ta ɓullo da hanyoyin daɗa wa kanta, kamar yadda ta shaida wa BBC a shirinsu na 'BBC Breakfast.'
Ta ce: 'Har yanzu ina kan sama wa kaina cigaba da fuskantar kai na kullum da safe wadda a wasu lokutan hakan kalubale ne,’
Ta ci gaba da cewa: 'A kullum ina kokari, kamar yadda na shaida a littafina, ina yi wa kaina kirari da kalamai masu daɗi.
yi mana ba.
"Ina ganin hakan shi ne jigon wasu damuwa da rashin farinciki, saboda idan ba ki koyi yadda za ki so kanki ba, yadda kike, to zai yi wuya ki iya nusar da sauran mutane kan hakan.
"Don haka a kullum ina aiki a kanwannan a ko-da-yaushe."

Asalin hoton, Reuters
Misis Obama, mai shekara 58 a duniya, ta yi zaman fadar White House tare da mijinta a lokacin mulkinsa tsakanin 2009 zuwa 2017.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A hirar da aka yi da ita a Burtaniya kan littafinta, The Light We Carry, ta faɗa wa Naga Munchetty ta BBC cewa: "Ana maka kallon wani gida mai karfin gaske.
"Ana miki kallon macen da ta yarda da kanta, macen da ta ginu, mace mai hazaka…Idan kina jin haka, to wani fata ne ya rage ga sauran mata?"
Misis Obama ta mayar da martani: "Ina ganin amfanin fitowa a tattauna kenan.
"Dukkaninmu tattare muke da irin wannan tunani, irin wasu tunani marasa kyau da muke dauke da su tsawon shekaru, musamman a matsayinki na mace, mace bakar fata, inda ba a ganinmu a matsayin abin alfahari a cikin al’umma.
"Ina ganin muna kan hanyar dacewa, amma daga cikin abubuwan da ake magana a kai shi ne, yadda rayuwa take a lokacin da mutum ke girma, ba wai kawai batun mace bakar-fata ba.
Aamma a matsayin doguwar mace bakar-fata, kafin zamanin Serena da Venus [Williams], kafin a kirkiri kungiyar kwallon kwando ta mata, da kuma rashin wanda za ka yi koyi da shi baya ga masu wasannin tsalle-tsalle.
"Yana da kyau mu fahimci irin mutanen da za mu iya zama saboda mu samu karsashi da farin ciki kan yanayinmu."
'Yanayi na Tsoro'
Ta kuma yi Magana kan muhimmanci yadda za ka yaki ‘tsoro da ke tattare da kai ko ke wanda ke taso wa mutum lokaci zuwa lokaci’.
"Idan kana iya fahimtar kanka, ya kasance abin da ke ba ka tsoro shi ne abun da zai jefa ka cikin hadari – sannan ya kasance akwai wani bangare naka da ke ba ka kwarin gwiwar yakar wannan tsoron.
"Ina iya cewa yanayin da na tsinci kaina a yau, saboda irin takura kaina da tursasa wa kaina yin abubuwan da suka zarta tunanina, cire wannan tsoron a raina, da rungumar sabbin kalubale da babu mamaki suna iya rike ni ko datse ni daga cimma burikana."
A littafin, Misis Obama ta ce yanayi na fargaba da ta tsinci kanta a rayuwa shi ne lokacin da mijinta ya fadamata cewa yana son ya gwada takarar shugaban kasa.
"Ban taba tunanin za a zo gabar da zan yi wannan zama domin bayar da tarihina ba ganin fargabar da ke tattare da ni a lokacin, a cewarta .

Asalin hoton, Getty Images
"Na kasance wacce ta samar da martaba ga rayuwar mutane da dama, musamman Amurkawa bakakken fata, da kakannina, wadanda rayuwarsu ta fuskanci iyaka saboda fargabar wani abu na daban," a cewarta.
Kakanninta sun taso a lokacin da bakar-fata ba shi da sukunin iya fitowa ko a cikin makwabta, ko fargabar lokacin fita ko wajen zama, lalubo hanyoyin kaucewa kuskure saboda guje wa mutuwa, a cewarta.
"Don haka yayin da shekaru ke wucewa, ina ganin kamar duniyar kakannina ta kasance yar karama kuma tsukakkiya ganin an kai gabar da ba su yarda da kowa ba, babu wanda suka sani ko likitoci ba su yarda da su ba.
Kuma wannan dalili ya sa, daya daga cikin kakannin nawa ya kamu da kansar huhu ba tare da ya sani ba.
"Ina amfani da wannan domin bayar da misalin irin yanayi mai tsanani da aka kulle mu a ciki, fargabar haduwa da mutane ko fahimtar da mutumin da ba ya sonmu, ko yake ganin ya fi mu, ko aminta da ra'ayinmu.
Wannan ya sa duniyarmu ta kasance kalilan 'yar karama kuma ya sa ana yada labaran karya da jita-jita da ake kalubalantarmu da su.
"Mun soma tsoron duk wani wanda ba ya cikinmu. Wannan ba rayuwa ba ce mai inganci.
Don haka ina son mutane musamman matasa su yi la'akari da haka, irin tsoron da muka sha fama, domin iya ganewa ko tantace tsoro da kuma sama wa kai tsaro, da fargabar da za ta datsesu wuri guda a duniyarsu."
'Shin mun bar baya da kura ne?'
Ta shaida cewa akwai mutane da dama da ke ganin ba a damu da su a wannan duniya ba', kuma suna 'takaicin har yanzu' cewa Donald Trump ya gaji Barack Obama.
"A wannan lokaci dole za ka tambayi kanka, shin ya cancanci wannan kujera? A cewarta.
"Shin mun yi wani tasiri ne? Abin damuwa ne? Idan ina cikin yanayi na mafi muni, wurin da ba na tattare da farin ciki, ina iya cewa, to, watakila ba hakan ba ne. Watakila kwarewar tamu ba ta kai wani mataki ba.
"Amma inda na kewaya, sannan kuma idan komai ya fito fili, lokacin da nake iya sake baje wadannan tunani da nazari mai zurfi a kansu, sai na ce, wai.., akwai matasa da dama a duniya da ke da tunani iri daban-daban kan yanayinsu saboda aikin da muka yi.
"Shin mun iya maganace komai cikin shekaru 8 na mulkinmu? Gaskiya ba mu yi ba. Ba hakan sauyi ke samuwa ba. Amma dai mun bar tambarinmu a kasa.
Mun dan tura motar gaba kadan. Amma shi cigaba ba lokaci guda yake samuwa ba.
Akwai fadi tashi da tsayawa cak wuri guda a wasu lokutan. Sauyi na tattare da wadannan kalubale.
"Kuma shi ya sa muke aikin da muke yi a yau domin taimaka wa masu tasowa gaba.
Ma’auratan a yanzu na tafiyar da gidauniyar da suka samar ta Obama Foundation, wanda aikinsu shi ne zaburarwa da agazawa da hada kan mutane da za su kawo sauyi a duniya."











