Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fitattun mawaƙa a Kannywood da Youtube ya ɗaga likkafarsu
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Mawaƙan Hausa da dama sun fara ƙirga ribar da suke samu a sanadiyar ɗora waƙoƙinsu a YouTube, kafar da take ba manya da ƙananan mawaƙa damar baje-kolin fasaharsu cikin sauƙi.
Yawancin mawaƙan Hausa na dauri, sun samu ɗaukaka ne a sanadiyar sanya waƙoƙinsu a gidajen rediyo, da kuma tarukan bukukuwa da suke halarta, ko kuma tarukan kalankuwa da mawaƙan suke shiryawa.
Amma yawancin mawakan Hausa na zamani sun samu ɗaukaka ne a sanadiyar waƙoƙin fina-finai da suke yi, inda a zamanin baya ma jaruman da suka hau waƙoƙin suke shuhura sama da mawaƙan.
Daga baya mawaƙan Kannywood sun fara shirya albam na waƙoki a faye-fayen CD suna sayarwa kamar yadda ake yin fina-finai, lamarin da ya kawo wani sauyi a ɓangaren waƙokin Hausa.
Mawaƙa irin su Abubakar Sani da Adam A. Zango da Sadi Sidi Sharifai da Nazifi Asnanics ne suka shige gaba a wannan zamanin, inda kundin waƙokinsu suka ci kasuwa sosai, kuma suka ƙara samun ɗaukaka bayan an daɗe ana jin muryoyinsu a fina-finai.
Sai dai yanzu zamani ya sauya, inda mawaƙan Hausa da dama suna sabunta salon fitar da waƙoƙinsu, inda suka koma ɗorawa a YouTube suna samun kuɗin, lamarin da ya fitar da sababbin mawaƙa da muryoyinsu ke amo a yanzu.
Ga wasu mawaƙan waɗanda a sanadiyar YouTube ne likafarsu ta ɗaga.
Hamisu Breaker
A ranar 30 ga Mayun 2020 ce mawaƙi Hamisu Sa'id Yusuf Ɗorayi, wanda aka fi sani da Hamisu Breaker ya ɗora waƙar 'Jaruma' a tasharsa ta YouTube.
Kafin ya fitar da bidiyon, waƙar ta riga ta fara tashe bayan an yi gasar waƙar kai wa maza abinci da ita a lokacin da ake kullen cutar kurona.
Jaruma Momee Gombe ce ta taka rawa a waƙar, wadda darakta Sanusi Oscar 442 ya ba da umarni.
Zuwa yanzu, waƙar ta samu masu kallo a YouTube sama da miliyan 14 a tashar tasa mai mabiya dubu 507, wadda aka buɗe a ranar 6 ga Yulin 2018.
Waƙarsa ta biyu da aka fi kallo ita ce 'Ƙarshen ƙauna' wadda ya yi tare da jaruma Rakiya Mousa, wadda ta samu masu kallo sama da miliyan takwas daga ranar 27 ga Yulin 2019 da aka ɗora ta, sai kuma waƙar 'Na yi sa'a, wadda ta samu masu kallo sama da miliyan bakwai daga ranar 19 ga Janairun 2019 da aka fitar da ita.
Fresh Emir
Adam Abdullahi Emir, ko kuma Fresh Emir mawaƙi ne da ya fara fice a sanadiyar waƙoƙinsa na fafutikar neman kawo sauyi a YouTube, tun daga jerin kundinsa na farko mai suna 'Aku mai bakin magana' a tasharsa ta YouTube da ya fara ɗora waƙa a ranar 23 ga Janairun 2019.
Ya yi zango biyu ne na jerin gwanon waƙoki mai suna 'A yau' zango na ɗaya da na biyu da na uku.
Waƙarsa da ta fi tashe ita ce 'Illar zina' a zango na biyu na waƙoƙin 'A yau' wadda ta samu masu kallo 707,099 daga 28 ga Afrilun 2012 daga aka ɗora ta.
Waƙoƙin kundin 'A yau' zango na ɗaya na 'Fyaɗe' da 'Almajirai' ne suka fara ɗaga tauroron mawaƙin.
Sadiq Saleh
Sadiq Saleh matashin mawaƙi ne, wanda ya fara tashe tun daga waƙarsa ta 'Abin ya motsa', wadda ta samo masu kallo sama da miliyan huɗu daga ranar 6 ga Agustan 2022 da aka ɗora ta.
Sai waƙar 'Darasul Auwal', wadda aka ɗora a ranar 4 ga Agustan 2023, wadda ta samu masu kallo sama da miliyan 3,462,130.
Garzali Miko
Garzali Miko jarumi ne, wanda yake haɗa fim da waƙoƙi, musamman a tashar YouTube.
Waƙarsa ta 'Mai sona' wadda aka ɗora a ranar 7 ga Maris na 2021 ta samu masu kallo 3,793,520. Sai waƙar 'Baby' wadda ta samu kallo miliyan 3.2.
Daga baya da ya fara fitar da bidiyo a YouTube aka gane cewa yana waƙa, duk da cewa an fara jin muryarsa tun kafin lokacin.
Kawu Ɗan Sarki
Muhammad Khalid Yunus, wanda aka fi sani da Kawu Ɗan Sarki wani matashin mawaƙi ne da yake tashe a YouTube.
Waƙarsa ta 'Ingallo' ita ce wadda ta fi tashe, inda ta samu masu kallo guda miliyan 6,006,405 daga ranar 1 ga Maris ɗin 1, 2022.
Hauwa ƴar Fulani
Hauwa ƴar Fulani, mawaƙiya ce da ta daɗe a masana'antar, amma YouTube ne ya ƙara haskaka ta, ta ƙara suna.
Waƙar da ta yi tare da Adam A. Zango ta 'War-war Pullo' da aka ɗora a ranar 16 ga Yunin 2022 ta samu masu kallo 3,048,731. Sannan tana fitowa a waƙoƙin siyasa tare da manyan mawaƙa maza.
Auta MG Boy
Abdurrahman Muhammad Garba wanda aka fi sani da Auta MG Boy fitaccen mawaƙi da ya fara tashe daga YouTube.
Waƙarsa da ta fara tashe ita ce 'A yi mini aure' amma waƙarsa ta 'Soyayya ce ta haɗa mu' ita ce ta fi tashe, inda ta samu masu kallo 6,656,182 daga ranar 17 ga Nuwamban 2021 da aka ɗora.
Sauran mawaƙan da YouTube ya ɗaga tauraronsu sun haɗa da Isah Ayagi, da Salim Smart da Ɗan Musa new prince da Sani Liyaliya da Sabon Oji da sauransu.