Ƴan Kannywood takwas da suka samu muƙamin gwamnati

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 3

Ƴan Kannywood da dama sun rabauta da muƙaman siyasa a wannan gwamnatin tun daga matakin tarayya da wasu jihohi, lamarin da wasu ke murna, wasu kuma suke nuna rashin daɗi, suna masu cewa ana ba ƴan fim muƙamai.

An dai ga yadda ƴan masana'antar suka shiga aka dama da su dumu-dumu a harkokin yaƙin neman zaɓe a kowane ɓangare na siyasa, inda kusan kowane ɓangare na jam'iyya da ƴantakara suke da masu tallata su daga masana'antar.

Ga wasu waɗanda suka samu muƙaman gwamnati.

Ali Nuhu - Shugaban Hukumar Finafinai ta Najeriya

Gwamnatin Najeriya a ƙarƙashin Bola Tinubu ce ta naɗa fitaccen jarumi kuma darakta, Ali Nuhu a matsayin shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya.

Tuni Ali Nuhu ya fara aiki a hukumar, wadda take ƙarƙashin ma'aikatar al'adu.

Rahama Sadau - Kwamitin iDICE

Rahama Sadau kuma ta samu shiga cikin kwamitin bunƙasa zuba jari ta hanyar amfani da fasahar zamani wato Technical Committee of the Investment in Digital and Creative Enterprise programme (iDICE) wanda yake ƙarƙashin ofishin mataimakin shugaban ƙasa.

Kwamitin yana zama ne a ƙarƙashin mai ba shugaban ƙas shawara kan tattalin arziki a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Tope Kolade.

A watan Afrilu ne aka sanar da naɗin, inda ta bayyana a shafinta na X tana bayyana godiyarta ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da mataimakinsa Kashin Shettima bisa wannan damar.

Bashir Datti - Kwamishina a jihar Filato

Bashir Lawandi Datti jarumi ne kuma furodusa a masana'antar Kannywood.

Ya yi takarar kujerar majalisar jihar Filato sau biyu a shekarar 2019 da 2024, amma bai samu nasara.

Sai dai gwamnan jihar Filato na yanzu ya naɗa shi kwamishinan matasa da wasanni, sannan daga bisani aka sauya masa ma'aikata zuwa ma'aikatar albarkatun ruwa da makamashi.

Duk da cewa ba sanadiyar fim ɗin aka naɗa shi ba, jarumin ya taka rawa a fina-finai irin su 'Kallon Gajimare' da 'Gori', sannan ya yi a bayan fage a 'Sai wata rana' da 'Halacci' da 'Ƴa daga Allah' sannan shi ne furodusan fim ɗin 'Gidan Aure' da sauransu.

Abba El-Mustapha - Hukumar Tace Fina-finai ta Kano

Abba El-Mutapha shi ne shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, matsayin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa shi bayan sun samu nasara.

Tuni ya fara aiki a hukumar, duk da ɗarewarsa muƙamin ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ƴan ɓangarensu na siyasa.

Sunusi Oscar 44 - Mai ba gwamnan Kano shawara kan Kannywood

Shi ma fitaccen darakta a Kannywood, Sunusi Hafiz, wanda aka fi sani da Sanusi Oscar 442 ya rabauta da muƙamin bai ba gwamnan Kano shawara na musamman a kan harkokin Kannywood.

Tijjani Gandu - Mai ba gwamnan Kano shawara kan mawallafa

Shi ma fitaccen mawaƙin siyasa, wanda ya fi fice da waƙarsa ta Abba gida-gida wato Tijjani Hussaini Gandu ya samu muƙamin mai ba gwamnan Kano shawar na musamman kan harkokin mawallafa.

A kwanakin baya an ga mawaƙin yana ba wasu jaruman Kannywood motoci da kuɗin mai da ya ce daga gwamna ne domin godiya a kan gudunmuwar da suka bayar.

Maryam Jankunne - Mai ba gwamnan Kano shawara kan matan karkara

Hakazalika an naɗa tsohuwar ƴar Kannywood, Maryam Abubakar Jankunne a matsayin babbar mai ba gwamnan Kano shawara kan matan karkara.

Rabiatu Sulaiman Kurfi - Mai taimaka wa gwamnan Katsina kan kafofin sadarwa na zamani

Rabiatu Sulaiman Kurfi ita ce mai ba gwamnan Katsina, Dokta Dikko Raɗɗa shawara a kan kafofin sadarwa na zamani.

Ita ce jarumar da ta maye gurbin Aishatu Aliyu Tsamiya a fim ɗin 'Manyan Mata' mai dogon zango na furodusa Abdul Amart Maikwashewa da Kwana Casa'in da sauransu.