A biya wadda aka buga hotunan tsiraicinta kusan naira biliyan 900 - Kotu

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Nadine Yousif
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Wata kotun jihar Texas da ke Amurka ta umarci wani mutum ya biya tsohuwar budurwarsa tarar dala biliyan 1.2 kwatankwacin naira biliyan 900, bayan ya wallafa hotunan tsiraicinta a shafukan intanet.
Matar - wadda da aka ambaci sunanta da inkiyar DL (harrufan farko na sunayenta) a takardun kotu - ta shigar da tsohon saurayin nata ƙara ne bisa zargin cin zarafi a shekara ta 2022.
Ta zargi tsohon saurayin da wallafa hotunanta na batsa a shafukan intanet, bayan sun rabu, domin kawai kunyata ta a matsayin ramuwar gayya.
Lauyoyin matar sun ce hukuncin, wata nasara ce ga wadda suke karewar.
"Haƙiƙa hukuncin ya yi mana daɗi, domin kuwa hakan zai wanke ta daga ɓatancin da ya yi mata", in ji Bradford Gilde, jagoran lauyoyin DL a wata sanarwa.
Tun farko, lauyoyinta sun buƙaci kotun ta tilasta wa mutumin ya biya tarar dala miliyan 100.
"Muna fatan wannan maƙudan kuɗi na tara zai zama izina ga masu hali irin nasa, tare da koyar da darasi ga masu irin wannan mummunar ɗabi'a," in ji Mista Gilde.
Daga bayanan da aka gabatar wa kotun , DL ta fara soyayya da saurayin nata ne a 2016.
Inda ta riƙa tura masa hotunan tsiraicinta a lokacin da suke ganiyar shan zumar soyayya.
Bayan sun rabu ne a 2021, aka zarge shi da yaɗa hotunan a shafukan sada zumunta da na intanet, ba tare da saninta ba.
An zargi tsohon saurayin da tura wa ƙawayenta da 'yan uwanta adireshin shafin da ya wallafa hotunan, domin su kalli hatunan .
An kuma zarge shi da yin kutse a shafukanta na sada zumunta da adireshinta na Email, wajen yi mata leƙen asiri.
Haka kuma an zargi tsohon saurayin nata da tura mata saƙon razanarwar da ke cewa "Na tabbata za ki ƙare rayuwarki, kina ƙoƙari a banza don maido da mutuncinki da ya zube a shafukan Intanet.
Duk mutumin da kika haɗu da shi, zai riƙa kallonki da wannan tabon. Ina taya ki murnar shiga wannan fagen gwagwarmaya.
Lauyoyin matar sun yi iƙirarin cewa tsohon saurayin nata ya wallafa hotunan ne domin cin zarafi da wulakanta ta a idon duniya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mutumin dai bai halarci zaman kotun ba, kuma babu wani lauya da ya wakilce shi a shari'ar kamar yadda kafofin yaɗa labaran Amurka suka ruwaito.
Kotun ta umarce shi ya biya matar tarar dala miliyan 200 kan damuwar da za ta shiga, sannan kuma da dala biliyan ɗaya kan ɓata mata suna.
DL ta shaida wa kafar yaɗa labaran Texas cewa ta yanke shawarar kai tsohon saurayin nata ƙara ne bisa shawarar da 'yan sanda suka ba ta.
A shekarar 2016, kusan Amurkawa miliyan 10 ne aka ba da rahoton cewa tsoffin abokan soyayyarsu sun wallafa hotunan tsirancinsu a shafukan sada zumunta don ramuwar gayya.
Wata kotu a Califonia ta yanke hukuncin biyan wata mata tarar dala miliyan 6.8 kan yaɗa hotunan tsiraicinta da tsohon saurayinta ya yi a shafukan sada zumunta a 2018.
Da yawansu mata ne wadanda shekarunsu suka kama daga 18 zuwa 29, kamar yadda wani bincike daga cibiyar 'Data & Society Research' ya nuna.
Kusan duka jihohin Amurka - idan ban da Massachusetts da South Carolina - na da dokokin kare wallafa hotunan cin zarafin mutane.











