Uwa da 'ya na farko da suka je duniyar wata

Asalin hoton, Virgin Galactic
Keisha Schahaff da Ana Mayers sun kasance uwa da 'ya na farko da suka yi tafiya zuwa duniyar wata
Mahaifiyar da 'yar sun samu kujerun tafiyar ne a wata gasa da suka ci.
Keisha, daga tsibirin Antigua, ta yi nasarar cin gasar da ta ba ta damar zuwa yawon buɗe ido duniyar wata, a lokacin da suke tafiya a jirgin sama zuwa Birtaniya, ƙasar da 'yar ke karatu.
Tana cikin jirgin sama daga tsibirin Antigua zuwa London ne a 2021 don neman biza ga 'yarta - wadda za ta shiga Jami'ar Aberdeen daga Caribbean lokacin da ta ga wani talla na wata gasar tsere.
Bayan watanni ne sai ta fahimci cewa sun ci gasar.
Daga bisani ta ce: "Kwatsam, sai na ji tafiya a bayan gidana. Kuma sai ga Richard Branson, mai kamfanin jirgin zuwa duniyar wata mai jigilar fasinja don yawon buɗe ido. Gaba ɗaya jami'ansa suka cika gidana suna cewa 'ke ce kika yi nasara, za ki tafi duniyar wata'."
Tafiyar jirgin saman Virgin Galactic shi ne sufurin masu yawon buɗe ido don kasuwanci na farko kuma zai ɗauki fasinjansa na farko da ya sayi tikiti.
Tsohon ɗan tseren kwale-kwalen a gasar Olympic na Birtaniya, Jon Goodwin daga Newcastle zai kasance mutum na biyu mai cutar ƙyarma da zai tafi duniyar wata, kuma ɗan gasar Olympic na farko da ya yi hakan.
Ya biya $250,000 kwatankwacin naira miliyan 250 don sayen tikitinsa a shekara ta 2005.
An tsara cewa jirgin nasu zai tashi ne ranar Alhamis da safe a jihar New Mexico a Amurka. Fasinjojin jirgin za su ɗan ji wani yanayi na rashin nauyin jiki a ƙololuwar tafiyar tasu - wadda aka ƙiyasta za ta shafe tsawon kimanin minti 90.
Tafiyar jirgin na Virgin Galactic ta biyu amma ta farko ga 'yan yawon buɗe ido daga nan zai zagayo ya sauko zuwa sansanin tashar jirgin sararin samaniya ta Spaceport America.

Jiragen saman fasinja na zamani za su iya tashin da ya kai fiye da ƙafa 40,000 (kilomita 12) a sararin samaniya.
Yayin da jirgin zuwa duniyar watan yake luluƙawar da ta ninka ta jiragen sama har sau bakwai zuwa nisan ƙafa 280,000 (kilomita 85).










