Burin masana na zaƙulo sirrukan sararin samaniya a 2023

MADDALONI, CASERTA, ITALY - 2022/12/30: First quarter moon of December last of 2022, seen from southern Italy. (Photo by Vincenzo Izzo/LightRocket via Getty Images)

Asalin hoton, Getty Images

Dukkan mu muna da sha’awar jin labaran sararin samaniya, ko ba haka ba? Ga masu ra’ayin haka...ku shirya jin irin wadannan labarai a 2023.

Shekarar 2022 ta kare da burin Artemis 1 – inda aka harba wani jirgi zuwa duniyar wata.

A wannan shekarar ma, akwai niyyar harba rokoki da kuma burika na zuwa sararin samaniya, wanda da yawa daga ciki kan tuna wa mutane yadda ake irin wannan tafiya zuwa sararin samaniya.

A nan, mun duba wasu manyan batutuwa da za su faru a duniyar wata.

Burin zuwa duniyar wata

Bayan nasarar zuwa duniyar wata da hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka NASA ta yi, a yanzu kuma tana shirin gwada na’urori da gudanar da binciken kimiyya a shirye-shiryen da take yi na sake zuwa duniyar wata a 2025.

Akwai shirye-shirye da dama na zuwa duniyar wata a yanzu, inda ɗaya daga ciki shi ne ƙaddamar da na’urorin aikawa da sako zuwa duniyar wata na Nova-C da kuma samar da kayan kimiyya guda biyar a duniyar ta wata.

Nova-C lunar lander

Asalin hoton, Intuitive Machines/NASA

Na’urorin na ƙunshe da fasahohi da za su taimaka wa masana kimiyya gwada kayayyakinsu a duniya a ƙoƙarin na zuwa duniyar wata.

Za kuma a gwada na’urorin daukar hoto da masu aike da sako domin ganin tasirin su wajen tattaro bayanai da kuma nadar su wadanda za su taimakawa wasu shirye-shirye na zuwa duniya wata.

Za a gwada wani makamin roka na farko mai suna Vulcan Centaur, duka a cikin shirye-shirye na zuwa sararin samaniya.

Na’urar na dauke da injina guda biyar da za su taimaka wajen saukar rokan a duniyar wata...kamar dai motar daukar kaya.

Yawon buɗe ido zuwa sararin samaniya

Wasu jirage biyu za su tashi daga tashar nazarin sararin samaniya ta kasa da kasa dauke mutane 100 zuwa sararin samaniya domin yin hutu, a wannan shekara.

Hakan zai zama kamar wani daki mai kyau.

A kan haka, wani biloniya dan ƙasar Japan, ya zabi wasu mutane takwas domin tafiya tare zuwa duniyar wata, duk da cewa masu lura a Amurka ba su amince wa jirgin mutanen zuwa duniyar watan ba a yanzu.

Shirye-shirye game da tashar sararin samaniya

ISS

Asalin hoton, NASA

A shekarun baya-bayan nan, mun ga irin nasarori da kamfanin Space X, mallakin Elon Musk, ya samu na tura mutane zuwa sararin samaniya.

Aikin kamfanin shi ne kai kayaki da mutane duniyar wata da kuma dawo da su lami lafiya.

A 2023, za mu ga tashin jiragen hukumar kula da sararin samaniya ta NASA – domin hakan ku zuba ido.

Sai dai, ba jami’an NASA kadai za mu gani ba a wannan shekara. Za mu kuma ga yadda za a kaddamar da jirgin farko na Boeing CST-100 da zai dauki ma’aikatan na NASA zuwa duniyar wata.

An tsara jirgin ne domin daukar ma’aikata zuwa babbar tashar sararin samaniya da kuma wasu wurare a nan duniya – don haka za mu ga hakan a karon farko shi ma.

Za a iya amfani da jirgin har sau goma kuma yana dauke da kwararru na fannin fasaha, hade da manyan wayoyi da kuma intanet.

Tauraro

Jupiter is HUGE!

Asalin hoton, NASA

Hukumar kula da sararin samaniya ta Turai ESA, ita ma tana shirin kaddamar da tauraron ɗan adam na zuwa Jupiter.

Burin na bukatar hakuri...zai kuma dauki tsawon shekara takwas kafin zuwa can. Shekarun ka nawa lokacin?

Idan suka samu damar zuwa can, za su fi mayar da hankali wajen zuwa duniyar ta Jupiter da watannin da ke zagaye da ita.

Duk da wannan, kafin watan Oktoba, Falcon Heavy na kamfanin Space X zai kaddamar da wani kumbo zuwa duniyar wata.

An samu jinkiri a aikin ne da aka yi niyyar yi a 2022 saboda matsala da wasu na’urori suka samu, inda a yanzu aka tsara kammala shi nan da 2029.

Muna da niyyar ba ku ƙarin bayani...sai dai akwai abubuwa da mu ma bamu sani ba.