Wane ne ke ruruta wutar rikici tsakanin kasashen Gabas ta Tsakiya?

Yaƙin da ke tsakanin Isra'ila da Hamas ya kasance da rikici mafi sarƙaƙiya a tarihin rikicin Gabas ta Tsakiya.

Baya ga wannan rikici, akwai faɗa tsakanin Isra'ila da Hizbullah a Labanon da kuma rikici tsakanin kasashen yammacin Turai da 'yan tawayen Houthi a Yemen.

Hare-haren da suka kara ta'azzara rikicin su ne wadanda Iran ta kai kan wuraren da ta ke kai wa hari a Iraki da Siriya da Pakistan sai kuma hare-haren da wasu kungiyoyi masu goyon bayan Iran din suka kai kan Amurka da Isra'ila da abokansu da sauransu.

Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan sun jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin rudani. Da yawan tashe-tashen hankula a Gabas ta Tsakiya, akwai hatsarin yaƙi mai tsanani.

Baya ga wannan, ƙila abubuwa da dama su canza a cikin ikon yanki na gargajiya a can ma.

A daya bangaren kuma ana ci gaba da takun saƙa tsakanin Isra'ila da kasashen Larabawa, da kuma saɓanin addini tsakanin ƴan shi'a na Iran da ƴan sunna na Saudiyya a daya bangaren.

Wadannan batutuwa guda biyu suna da muhimmanci a yayin da ake tattaunawa kan siyasar yankin Gulf da kuma dambarwar cibiyar mulki.

Kwararru da suka zanta da BBC sun amince cewa rarrabuwar kawuna a yankin na baya-bayan nan ba ta da alaƙa da harkokin addini illa alaƙa ta siyasa da sojoji.

Alaƙar Iran da ƙungiyoyin masu ɗaukan makamai

Lokacin da Iran ta kai hari kan wuraren da ta kai hari a kasashe uku daban-daban da suka haɗa da Iraƙi da Siriya da Pakistan a cikin kwanaki uku kacal tsakanin 15 zuwa 17 ga watan Janairun bara, al'ummomin duniya sun ji wannan barazanar ta yi kamarin gaske.

Iran ta dauki kwararan matakai, kamar kai hari ga kungiyoyin masu iƙirarin jihadi da ke gaba da juna a Syria da Pakistan, wanda ya yi kama da ayyukan tattara bayanan sirri na Isra'ila a Iraki.

Masana dai na ganin dalilin da ya sa Iran ta kai wadannan hare-hare shi ne don nuna bajintar sojojinta.

Duk da cewa Iran ta sha iƙirarin cewa ba ta son kasancewa cikin wani babban rikici ko yaƙi, ta gaza jure wa iƙirarin da ta yi na cewa ba ta so ta kasance cikin tashe-tashen hankula ko yaƙi.

Ƙungiyoyi masu dauke da makamai kamar su Hezbollah ta Lebanon da ƙungiyoyin Shi'a a Iraki da Afganistan da Pakistan da Hamas da sauran kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi a yankunan Falasdinawa, da kuma 'yan tawayen Houthi a Yemen ne sakamakon rashin juri'yar Iran ta ɓangaren shiga yaƙi da tashe-tashen hakula.

Sashen Farisa na BBC ya bayyana wannan akida ta Iran a matsayin 'mai nuna kyama ga Amurka da Isra'ila.

Dukkanin wadannan kungiyoyi sun kai hare-hare kan wuraren Isra'ila ko na kawayensu kadan tun bayan barkewar yaƙin Gaza a watan Oktoba.

Haizam Amirah-Fernandez, kwararre a yankin Gabas ta Tsakiya a cibiyar Royal Elk, ya bayyana wa BBC cewa, alakar da ke tsakanin Iran da kungiyoyin masu tayar da ƙayar baya ta kasance mafi daidaito a yankin kuma wadannan kungiyoyi sun dade suna tare.

Lina Khatib, darektar cibiyar SOAS ta Gabas ta Tsakiya mai hedkwata a Landan, ta shaida wa BBC cewa, "Dangantakar Iran da wadannan kungiyoyi ya samo asali ne daga juyin juya halin Iran na 1979, kuma wata hanya ce ta inganta manufofinsu na siyasa."

A cewar masana, waɗannan ƙungiyoyi ba su gamsu da yanayin siyasar kasashensu ba wanda hakan ya kai ga wanzuwarsu. Iran tana cin moriyar hakan.

A cikin labarin da BBC Mundo ta buga a shekarar 2020, 'yar jaridar BBC Farisa Kavian Hosseini ta ce dukkanin wadannan kungiyoyi suna samun tallafin kudi da akida daga Iran.

"Ba za a yi watsi da kusancin Iran da ƴan Shi'a da kyakkyawar alakar Saudiyya da 'yan Sunna ba," in ji Michael Kugelman, darektan Kudancin Asiya a Cibiyar Wilson. To amma a sa'i daya kuma, ya dage da cewa, gasar da ake yi tsakanin kasashen Gabas ta Tsakiya ta fi gwagwarmayar neman mulki fiye da bambancin addini.

Wannan shi ne dalilin da ya sa duk da cewa Hamas kungiya ce ta musulmai 'yan Sunni, itama Iran ke goyon bayanta.

Sau da yawa waɗannan ƙungiyoyi masu tayar da ƙayar baya na ɗaukar matsayi ko ɓangarori daban-daban.

Hamas da Hizbullah sun goyi bayan bangarori daban-daban a yaƙin Syria, amma sun haɗa kai wajen kawar da Isra'ila.

Da alama Iran ta zama saniyar ware a Gabas ta Tsakiya. In ban da gwamnatin Bashar-al-Assad na Siriya, Iran ba ta da wata alaƙa da wata kasa a yankin gabas ta tsakiya.

Masana sun ce akwai manyan dalilai guda biyu. Dalili na farko, in ji Amirah-Fernandez, shi ne, ana kallon tsarin juyin juya halin Musulunci a matsayin barazana daga dauloli masu dogaro da man fetur na kasashen Gulf da sauran kasashen yankin.

Dalili na biyu kuwa shi ne, Iran tana ganin cewa ta cancanci zama ‘yar mulkin yanki saboda tarihinta da albarkatunta da yawan al’ummarta da kuma gadon daular Farisa.” Ya kara da cewa: “Kuma wadannan buri na Iran suna cin karo da muradun wasu kasashe musamman Saudiyya."

Ƙawancen ƙasashe ƙarƙashin jagorancin Saudiyya

Kasar Saudiyya ta dauki matakai da dama a shekarun baya-bayan nan domin tabbatar da kanta a matsayin jagora a kasashen Larabawa.

Masar ta kasance kasa mafi yawan al'umma a kasashen Larabawa kuma kuma tana da tarihi sosai kan siyasa da al'adu ta yadda a shekarun da suka gabata, Masar ta kasance cibiyar kasashen Larabawa.

Amma sai mulki ya koma kasashen Gulf da yankin Larabawa. Inda aka samar da dimbin dukiya bisa dimbin albarkatun makamashi wadanda sannu a hankali ke yin tasiri a fagen siyasa.

Ƙananan kasashe irinsu Hadaddiyar Daular Larabawa ko Qatar sun taso a baya, amma tun daga lokacin, musamman da hawan Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, "Saudiyya ta canza sosai a cikin ƙasar da ma duniya baki ɗaya."

Masana sun yarda cewa Saudiyya ita ce shugaba na ƙungiyar Larabawa, ƙungiyar yanki me ƙasashe 22.

"Kowace kasa tana da burinta," in ji Khatib. "Duk da haka, Masar da Jordan su ma suna bin ka'idojin da Saudiyya ta gindaya." Kusan shekaru 40, Saudiyya da Iran sun ci gaba da yin gaba a fili a abin da wasu masana suka bayyana a matsayin "sabon yakin cacar-baki a gabas ta tsakiya."

Kuma a cikin 'yan shekarun nan, rikicin ya tsananta a sassa daban-daban na yankin.

A kasar Yemen, Saudiyya tana goyon bayan waccan gwamnatin a yaƙin da take yi da 'yan tawayen Houthi tun shekara ta 2015.

Ana zargin Iran da goyon bayan abokan hammayar Saudiyya 'yan ƙungiyar ta da ƙayar baya na Houthi.

Sai dai Iran ta musanta cewa tana aikewa da 'yan Houthi makamai.

Ana zargin 'yan ƙungiyar Houthi na amfani da makaman ne wajen kai hare-haren makamai masu linzami da jirage masu marasa matuki kan garuruwa da sansanonin Saudiyya.

Saudiyya ta kuma zargi Iran da yin katsalandan a ƙasashen Labanon da Iraki, inda 'yan bindigar Shi'a ke da gagarumin tasiri na siyasa da na soji.

Bugu da kari, ana zargin wasu daga cikin wadannan kungiyoyin da kai hare-hare a kan cibiyoyin Saudiyya.

A cikin Maris din 2023, dangantakar Saudiyya da Iran ta dauki wani sabon salo.

A shawarwarin da ƙasar China ta shirya, ƙasashen biyu sun sake raya huldar diplomasiyya, da farfado da yarjejeniyoyin da suka shafi tsaro da cinikayya da tattalin arziki da kuma zuba jari.

Masana sun gargadi BBC Mundo da cewa dangantaka a Gabas ta Tsakiya tana da sarkakiya kuma tana canzawa koyaushe,

Masu shiga tsakani

Khatib da Amirah-Fernandez sun sanya Qatar cikin kungiyar da Saudiyya ke jagoranta.

Yana ganin rawar da Qatar ke takawa a matsayin wani muhimmin al'amari na kokarin samar da daidaito a yankin.

A halin yanzu, masu shiga tsakani na Qatar ma suna shiga tsakani tsakanin Isra'ila da Hamas.

Tsawon shekaru, attajirin nan na al'umman Gulf ta yi sulhu tsakanin abokan gaba irin su Isra'ila ko Iran, da sauran makwabtanta wadanda galibinsu kungiyoyin masu ikirarin jihadi ne kamar Hamas ko Saudiyya.

Tsarin da maƙwabta ba su yi maraba da shi ba

"A shekarar 2017, Saudiyya da Bahrain da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Yemen da Libya sun tare Qatar, saboda suna kallonta a matsayin barazana saboda burinta na siyasa," in ji Khatib.

Qatar kasa ce mai matuƙar arziki amma ƙarama. Kamar yadda masanin kimiyyar siyasa Mehran Kamarawa ya bayyana a cikin littafinsa Qatar: Small State, Big Politics, "Qatar na neman ƙawance da yawa a matsayin wata hanya ta tabbatar da tsaronta da kuma ƙara girman matsayinta na diflomasiyya."

A shekarar 2021 ne dai aka ɗage takunkumin da aka sanyawa Qatar, kuma dangantakar da ke tsakaninta da kasashen da ke makwabtaka da ita, musamman Saudiyya na fuskantar wani yanayi na sada zumunci.

Tabbas, Khatib ya sake nanata, Qatar har yanzu tana son "kafa kanta a matsayin ƙasa mai sassaucin ra'ayi da sasantawa a cikin dabarun siyasarta."

Matsayin Isra'ila

Amirah-Fernandez ta kira Isra'ila a matsayin misali mai ban mamaki, kuma Khatib ya nuna cewa Isra'ila kasa ce mai cin gashin kanta ba tare da shiga wani kawance ba.

Ta dade tana yaƙi da Iran da dakarun sa-kai da take marawa baya ba tare da an bayyana shi ba, inda ake ɗan gwabza fada amma babu cikakken fadace-fadace. Dangantaka da makwabtan Larabawa ma ba ta da sauki.

Isra'ila da Turkiyya, da Iran ƙasashe ne waɗanda ba na Larabawa ba ne a Gabas ta Tsakiya waɗanda ke da ƙarancin amincewa a matsayin ƙasashe.

Daga cikin ƙasashen Larabawa kuma, Masar tun 1979 da Jordan tun 1994, da Hadaddiyar Daular Larabawa tun 2020 da Bahrain da Morocco da kuma Sudan sun amince da ƙasar Isra'ila.

A cewar Amirah-Fernandez, hakan na faruwa ne saboda, “Kasashen Larabawa na kallon Isra’ila a matsayin mai wuce gona da iri, kuma ‘yar mamaya ce, kuma wannan yaƙi da Gaza ya ƙara ta’azzara lamarin.

Jim kaɗan kafin a fara yaƙi da Hamas a ranar 7 ga Oktoba, 2023, Isra’ila ta kasance tana tattaunawa don daidaita dangantakarta da ƙasar Larabawa, wanda da zai kasance babban ci gaba ga kasar Yahudawan.

Sai dai bayan kai harin, an bayyana cewa mahukuntan Saudiyya sun bukaci Amurka da ta dakatar da wannan tattaunawa ta hanyoyi uku.

Saboda haka, har sai an sami hanyar warware rikicin Falasdinawa kafin za a iya shawo kan lamarin.