Muhimmancin kwana 10 na farkon watan Dhul Hijjah

Asalin hoton, Getty Images
Alhamis ce 1 ga watan Dhul Hijjah a kalandar Musulunci ta shekarar Hijira ta 1443 a Najeriya da Saudiyya da sauran ƙasashen Musulmi da dama.
Musulmai na kallon watan a matsayin mai alfarma, wanda ya ƙunshi babbar ibadar aikin Hajji ta hanyar ziyartar Ɗakin Allah wato Ka'aba da ke birnin Makkah na Saudiyya.
Kamar kowace shekara, Musulmai fiye da miliyan ɗaya ne ke shirin gudanar da ibadar a wannan shekara, bayan shafe shekara biyu ana taƙaita yawansu saboda annobar korona.
Hakan na nufin ranar Asabar, 9 ga watan Yuli ce Ranar Arfa, wata rana mai muhimmancin gaske ga alhazan da suka je Saudiyya don gudanar da Hajjin.
Ga wasu daga cikin muhimman abubuwa game da watan na Dhul Hijjah.
Keɓantattun abubuwa na watan Dhul Hijjah

Asalin hoton, Getty Images
Khalifa Muhammadul-Mashood, malami ne a Najeriya kuma ya bayyana watan da cewa yana da keɓantattun abubuwa da sauran watannin Musulunci ba su da shi.
Aikin Hajji
Daga cikin keɓantattun abubuwa na wannan wata akwai ibadar aikin Hajji, wadda ɗaya ce daga cikin rukunan addinin Musulunci.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A addinin Musulunci, ana kwaɗaitar da mutane ga duk wanda ya samu hali ya je ya gudanar da ibadar aƙalla sau ɗaya a rayuwarsa.
Babu inda ake yin ibadar sai a kusa da ginin Ka'aba mai tsarki, inda miliyoyin Musulmai ke zagaye shi tsawon kwanaki tare da yin salloli da addu'o'i.
Baya ga Ka'aba, wani ɓangare na aikin shi ne kai wa ƙabarin Annabi Muhammadu (SAW) ziyara a birnin Madina na Saudiyyar.
Ibadar yanka (layya)
SheikhMuhammadul-Mashood ya ce watan ya kuma keɓanta da ibadar yanka dabbobi iri biyu, da suka haɗa da layya, da hadaya, da fidiya.
"Fidiya ana yin ta ne sakamakon idan alhaji ya aikata wani abu da bai kamata ya aikata ba, kuma wanda ya yi yankan ba zai ci ba zai ci ba, sai dai ya bayar da sadakar naman," in ji Muhammadul-Mashood.
"Sai dai ita hadaya, idan mutum ya yi zai ci - kamar layya."
Arfa
"Arafa rana ce wadda a duniya babu yini mai daraja kamarsa," a cewar shehin malamin.
Dukkan maniyyata za su dumfari filin Arfa, inda za su shafe yinin rana guda suna gudanar da ibada da neman gafara ga Allah SWA.
Waɗanda suke da iko da kuma ƙoshin lafiyar hawa dutsen Arfa kan yi kokarin yin hakan don koyi da Annabi Muhammad SAW.
"Allah yana 'yanta bayi a wannan yinin, shi ya sa ma ake so duk wanda bai samu zuwa Hajji ba ya yi azumi a ranar," in ji malam. "Amma kuma ko me za ka yi a wannan rana ba zai kai na wanda ya ke filin Arfa ba."
Azumin Arfa
Duk da cewa ba dukkan Musulmi ne samun damar zuwa aikin Hajjin ba, ana kwaɗaitar da Musulmai su yi azumi a ranar Arfa.
Malamai sun ce Allah kan yafe wa bawansa laifin shekara ɗaya ta dalilin azumin.
Azumi a addinin Musulunci ana yinsa ne kafin fitowar rana zuwa faɗuwarta, inda Musulmai kan guje wa abin ci ko na sha da kuma jima'i a tsawon lokacin.
Zikirin Allah
Kazalika, malamai na yawan kwaɗaitar da mutane su dinga ambaton sunan Allah da yawa wato zikiri a cikin kwana 10 na farkon Zul Hijjah.
"Wanna ya samo asali ne daga umarnin da Allah ya bayar cewa 'ku ambaci sunan Allah a cikin wasu kwanaki ƙididdigaggu," in ji Malam Mashood.










