Me ya sa Manchester United ta kori Ruben Amorim?

Ruben Amorim

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ruben Amorim
Lokacin karatu: Minti 4

Ƙungiyar Manchester United ta kori mai horas da ƴan wasanta Ruben Amorim bayan faɗi tashin da ƙungiyar take yi a gasar Firimiyar Ingila.

A watan Nuwamban 2024 ne aka naɗa Amorim a matsayin mai horas da ƙungiyar, inda ya jagoranci ƙungiyar zuwa wasan ƙarshe na kofin Europa a watan Mayun da ya gabata, inda suka yi rashin nasara a hannun Tottenham.

Yanzu haka Manchester United ce ta shida a teburin Premier, duk da haka hukumomin ƙungiyar sun yi ta kawar da kai kan kiraye-kirayen sallamar kocin, har sai a wannan lokaci.

A cikin sanarwar da ta fitar, ƙungiyar ta ce "wannan shi ne lokaci mafi dacewa na kawo sauyi. Hakan zai bai wa ƙungiyar damar kammala kakar gasar Premier a mataki mafi dacewa.

"Ƙungiyar ta gode wa Ruben bisa ga gudumawar da ya bai wa ƙungiyar kuma tana masa fatan alheri a ayyukansa na gaba.

"Darren Fletcher ne zai ja ragamar ƙungiyar a matakin riƙo a wasanta na gaba da ƙungiyar Burnley a ranar Laraba," kamar yadda sanarwar da ƙungiyar ta tabbatar.

Ta yaya abin ya kai ga haka?

Ruben Amorim ya nace wajen amfani da salon wasa na masu tsaron baya uku da ƴan wasan gefe da gefe tun bayan zuwan shi United.

Amma kocin ya yi amfani da masu tsaron baya huɗu a wasan da ya samu nasara kan ƙungiyar Newcastle a washegarin Kirsimeti, kafin daga baya kuma ya koma tsohon salonsa.

Amorim ya bayyana cewa an samu saɓani tsakaninsa da shugabannin ƙungiyar game da sayen ƴan wasa.

Sannan ya yi kalaman da suka nuna cewa yana samun saɓani da daraktan ƙwallon ƙafa na ƙungiyar Jason Wilcox, kuma abin ya riƙa ƙazancewa tun bayan buɗe kasuwar musayar ƴan wasa ta wannan wata na Janairu.

A ganawar da ya yi da ƴan jarida ranar Lahadi, Amorim ya kira sunayen wasu manyan masu horaswa a gasar Premier, inda ya ce ba a yi musu irin katsalandan ɗin da shi ake yi masa a Manchester United.

"Na san cewa ba sunana [Thomas] Tuchel ba, ko Conte kuma ba Mourinho ba, to amma ni ne mai horas da ƴan wasan Manchester United.

"Kuma zan ci gaba har nan da wata 18 ko kuma zuwa lokacin da jagorancin ƙungiyar suka yanke hukunci."

"Ba zan ajiye aiki ba. Zan yi aikina har zuwa lokacin da za a kawo wani da zai maye gurbina."

Tarihin da Amorim ya kafa a United

Machester United na a matsayi na shida a teburin Premier bayan wasa 20, inda a ranar Lahadi suka tashi canjaras da Leed 1-1.

Wannan sakamako na nufin United ta lashe wasa ɗaya ne tal cikin wasanni biyar da ta yi a baya-bayan nan a Premier – kuma wasa uku kacal ke nan ta lashe cikin wasa 11 da ta buga a baya.

Amorim ya jagoranci United a karawa 63 jimilla, amma ya kasa yin nasara a fiye da rabin waɗannan wasanni.

Ya bar ƙungiyar bayan yin nasara a karawa 24, canjaras 18 da rashin nasara 21. Hakan na nufin ya lashe kashi 38.1% kawai na karawar United da ya jagoranta a matsayin mai horaswa.

United ta ƙare a mataki mafi muni a kan teburin Premier a matsayi na 15 a kakar da ta gabata, tun bayan da ta fadi daga gasar a kakar 1973-74, lokacin da ta je ralageshon.

Ko Fletcher zai iya?

Darren Fletcher

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Darren Fletcher

Yanzu an ayyana tsohon ɗan wasan tsakiya na Manchester United, Darren Fletcher a matsayin wanda zai jagorancin ƙungiyar a matsayin riƙo bayan korar Ruben Amorim.

Fletcher ya yi wasa sama da 340 a matsayin ɗan wasa a United a tsawon shekara 20.

Ɗan asalin Scotland, an kai shi United ne tun yana ɗan shekara 11, inda ya samu nasarar lashe kofin Premier biyar, da kofin League Cup biyu da na ƙalubale (FA) ɗaya da kuma gasar Zakarun nahiyar Turai ta Champions League.

Fletcher ya koma ƙungiyar West Brom da taka leda a shekarar 2015 kafin ya yi ritaya daga ƙwallon kafa a ƙungiyar Stoke City yayin da yake da shekara 34 da haihuwa.

Sai dai ya koma United a matsayin mai horas da ƴan ƙasa da shekara 16 a shekarar 2020.

Daga nan ya shiga cikin tawagar masu horas da babbar ƙungiyar har ma ya zama daraktan tsare-tsare na tsawon shekara uku.

Ya kasance mai horas da ƴan wasan ƙungiyar ƴan ƙasa da shekara 18 tun daga watan Yulin wannan shekara.

Lokuta masu muhimmanci a zaman Amorim a United

  • 1 ga Nuwamban 2024 - Manchester United ta naɗa Ruben Amorim a matsayin sabon mai horaswa.
  • 11 ga Nuwamban 2024 - Amorim ya fara aiki a hukumance bayan barin ƙungiyar Sporting.
  • 19 ga Janairun 2025 - Amorim ya bayyana tawagar United a matsayin "ƙila mafi muni" a shekara 147 na tarihin ƙungiyar
  • 17 ga Afrilun 2025 - Manchester United ta yi wani abin bajinta, na farfaɗowa daga cin 4-2 da ake yi mata, ta kuma ci ƙwallo biyu a ƙarshen wasan da ta kara da Lyon a gasar cin kofin Europa, lamarin da ya ba ta damar kai wa wasan ƙarshe na gasar bayan tashi 5-4.
  • 21 ga Mayun 2025 - Fatan United na lashe kofin na Europa ya gamu da cikas bayan da Tottenham ta lalasata a wasan na ƙarshe.
  • 25 ga Mayun 2025 - Manchester United ta ƙare gasar Premier a mataki na 15 da maki 42, matsayi mafi muni da ƙungiyar ta taɓa ƙarewa a tarihin gasar.
  • Yunin - Agustan 2025 - United ta kashe fam miliyan 200, wajen sayen sabbin ƴan wasa da suka ha ɗa da Benjamin Sesko da Bryan Mbeumo da kuma Matheus Cunha.
  • 27 ga Agustan 2025 - Ƙungiyar Grimsby, da ke buga gasar League two mai daraja ta huɗu a Ingila ta yi waje da Manchester United a gasar Carabao.
  • 8 ga Oktoban 2025 - Daya daga cikin mamallan ƙungiyar, Sir Jim Ratcliffe ya ce akwai buƙatar bai wa Amorim shekara uku domin tabbatar da cewa shi ''babban'' koci ne.
  • 24 ga Nuwamban 2025 - Ƙungiyar Everton ta yi nasara a Old Trafford duk da kasancewarsu da ƴan wasa 10, saboda bai wa Idrissa Gueye jan kati a minti 13.
  • 30 ga Disamban 2025 - Manchester United ta kasa cin Wolves wadda ke ƙasar teburin Premier, lamarin da ya bai wa Wolves makinta na uku a kakar bana.
  • 2 ga Janairun 2026 - Amorim ya ce alaƙarsa da jami'an ƙungiyar na ƙara taɓarɓarewa yayin da aka buɗe kasuwar musayar ƴanwasa.
  • 4 ga Janairun 2026 - Amorim ya bayyana cewa yana son yin aiki a matsayin managa ''ba koci ba'', kuma a shirye yake ya bar ƙungiyar idan kwantiraginsa ya ƙare cikin wata 18, bayan da ƙungiyar ta tashi kunnen doki a wasanta da Leeds United.
  • 5 ga Janairun 2026 - Amorim ya raba gari da Manchester United