Me ya sa samari suke fama da cutar damuwa, amma suke ɓoyewa?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Selin Girit
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 5
A cikin ƴan shekarun nan, duniya tana fama da matsalar ƙaruwar cutar damuwa, sannan abin damuwar ma shi ne yadda matsalar ke ƙamari a tsakanin yara maza da ƴan samari.
Wani bincike da aka ɗauki gomman shekaru ana gudanarwa ya nuna cewa mata sun fi maza neman taimako a lokacin da suke fama da cutar damuwa, kamar yadda binciken wanda aka yi a Amurka a 2023 ya nuna.
Haka kuma babu fayyacaccen bayani game da yadda - ko kuma yaushe - ake samun ƙaranan yara maza da samari suna neman taimako ko shawara domin magance cutar ta damuwa.
"Lamarin nan akwai ɗaga hankali," kamar yadda mujallar yara da cutar ƙwaƙwalwa ta matasa ta the European Child & Adolescent Psychiatry ta bayyana a bara, "yara maza ƙanana da samarinsu sun fi yawan kashe kansu."
Me yake jawo haka - kuma ta yaya makarantu da iyaye da hukumomi za su iya shigowa domin kawo sauyi?
Shan wahala a ɓoye
A duniya, duk ɗaya cikin ƙananan yara bakwai masu tsakanin shekara bakwai zuwa 19 suna fama da cutar damuwa, kamar yadda ƙididdigar Hukumar Lafiya ta Duniya ta nuna.

Asalin hoton, Getty Images
Binciken ya gano cewa damuwa da tashin hankali alamu ne da suka fara zama ruwan dare a tsakanin matasa, sannan kashe kai ne abu na uku da ya fi cin matasa masu shekara 15 zuwa 29.
Cibiyar cutar ƙwaƙwalwa ta The Lancet ta ce kusan kashi 75 na cutar damuwa na farawa ne kafin shekara 25. Za ka ga matashi a zahiri yana cike da lafiya, amma ƙwaƙwalwarsa na cike da damuwa, kuma adadin matasan da suke cikin wannan halin ƙaruwa suke yi, wanda hakan yake nuna akwai abin lura matuƙa a game da lafiyar ƙwaƙwalwar ta manyan gobe.
Amma yara maza da samari ba su cika zuwa neman shawara kan cutar da damuwa ba duk da cewa akwai buƙatar hakan.
"A shekara 15 zuwa 20 da suka gabata, mun samu ƙaruwar matsalar ƙwaƙwalwa a tsakanin matasa maza da maza, amma mata sun fi maza zuwa neman shawara," in ji Farfesa Patrick McGorry, masanin lafiyar ƙwalƙwalwa kuma daraktan ƙungiyar Orygen - Cibiyar kula da lafiyar ƙwaƙwalwar matasa a Australia.
Rashin zuwa neman shawarar na nufin maza ba sa neman taimako sai komai ya lalace ko kuma damuwar ta yi yawa.
Al'adu na cikin abubuwan da suke hana maza neman shawara ko taimako, kamar yadda masana suka shaida wa BBC, inda suka ƙara da cewa maza suna ganin rauni ne nuna gajiyawa a fili.
Dr John Ogrodniczuk, farfesan lafiyar ƙwaƙwalwa a Jami'ar British Columbia da ke Canada, kuma daraktan ƙungiyar HeadsUpGuys, mai kula da lafiyar ƙwaƙalwar maza ya ce maza suna lissafa neman shawara ko taimako a matsayin gazawa.
Neman shawara ta bayan fage
Binciken baya-bayan nan sun gano wasu abubuwa bayan na al'adu da fargabar nuna gazawa da suke hana maza neman shawara kan cutar ƙwaƙwalwa.
Maza da dama ba sa gane alamun cutar damuwa, ballantana su nemi taimako, kuma ba su cika samun natsuwar zuwa ganin likita ba.
Maza ƙanana da samari sun fi sha'awar neman shawara wajen abokai ko ta intanet a ɓoye ba tare an gane su ba, ko kuma cibiyoyin ba da shawara na maza da suke daidai da irin tunaninsu na mazantaka.
Wannan ya sa ba a cika ganin maza ba kasafai sun je ganin likita domin neman shawara kan cutar damuwa. A Australia misali, ƙungiyar Orygen ta kula da lafiyar ƙwaƙwalwa ta yi wani tsari na musamman domin duba matasa ta hanyar tattaunawa da su.
"Maza ƙanana ba su cika so ana ganinsu a ɗakin ganin likita ba. Sun fi so su zauna ana tattaunawa da su," in ji shugaban Orygen Patrick McGorry.
Rawar kafofin sadarwa
Kafofin sadarwa na da fuska biyu: Za su iya sada zumunta da bayar da bayanai masu muhimmanci, amma kuma suna iya ba matasan samun bayanai masu cutarwa.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Yanzu maza da dama sun fi bibiyar masu fitar da bayanai da suke da tunani irin na maza," in ji Dr Simon Rice, masanin lafiyar ƙwaƙwalwa, kuma darakta a cibiyar lafiyar ƙwaƙwalwa ta maza ta Movember Institute.
Binciken cibiyar Movember ya gano cewa matasan da suke bibiyar bayanan da suke ƙarfafa tunanin maza sun fi shiga cutar damuwa.
Amma Dr Rice ya ce ba dukkan bayanan da ake samu daga kafofin sadarwa ba ne suke cutarwa, inda ya ƙara da cewa kafofin sadarwa ma za su iya amfani wajen inganta lafiyar ƙwaƙwalwa.
Farfesa Mina Fazel, shugabar tsangayar lafiyar ƙwaƙwalwa a Jami'ar Oxford, ta aminta da hakan, inda ta ce akwai buƙatar a koyar da matasa da iyaye yadda tsarin intanet yake, inda ya yi misali da wani bincike da za a fitar nan gaba kaɗan, wanda ya nuna cewa yawanci matasan da suka cutar da kansu, a kafofin sadarwa suka koya.
Sai dai Farfesa Fazel ta ce ba laifin kafofin sadarwa kawai za a gani ba, inda ya ƙara da cewa akwai buƙatar wasu sauye-sauye a cikin al'umma.
Matsalar kaɗaici
Babbar matsalar da ke ci wa matasa tuwo a ƙwarya shi ne ƙadaici - kuma ba a cika mayar da hankali.

Asalin hoton, Getty Images
Dr Ogrodniczuk ya ce alƙaluman da suka samu daga HeadsUpGuys sun nuna kaɗaici da rashin tabbas na cikin abubuwan da suke damun matasa maza.
Masana sun nuna buƙatar da ke akwai ta samar da wuri na musamman da maza matasa za su riƙa zuwa suna tattauna matsalolinsu - ba dole sai wuraren ganin likita ba.
Misali su riƙa samun masu ba su shawara da da haɗakar taimakon juna ko kuma a tsara hanyoyin inganta lafiyar ƙwaƙwalwa a ajujuwa.
Rawar makarantu
"Akwai alama da ke nuna cewa matuƙar mazan sun nemi shawara, tana taimaka musu matuƙa," in ji Farfesa Mina Fazel.
"Amfanin shawarar ba shi a alaƙa da inda aka samo ta, ko dai a makaranta ko a kafofin sadarwa ko a cikin al'umma."

Asalin hoton, Getty Images
Akwai kuma alama da ke nuna cewa makarantu na taka muhimmiyar rawa "wajen lafiyar ƙwaƙwalwar matasa.
Farfesa Fazel ta yi amannar cewa makarantu na da rawar da za su taka domin inganta lafiyar ƙwaƙwalwarsu.
"Mafi yawancin ƙananan yara suna samun damar zuwa makaranta," in ji ta, "don haka ilimantar da yaran na da muhimmiyar rawar da za ta taka wajen inganta lafiyar ƙwaƙwalwarsu, ba iliminsu ba kaɗai."











