Wane ne Malam Yahaya Masussuka kuma me ya sa ake cece-kuce a kansa?

Lokacin karatu: Minti 5

A yanzu haka kusan za a iya cewa Malam Yahaya Masussuka na ɗaya daga cikin malamai da ke tayar da ƙura da kuma aka fi jin amonsu a kafafen sada zumunta a arewacin Najeriya, sakamakon irin wa'azinsa dangane da irin fahimtar da ya yi wa addini wadda wasu ke yi wa kallon ba daidai ba.

Wannan saɓanin fahimtar da yake da ita ce dai masu fashin baƙi ke ganin ita ce ta sa wasu malaman arewacin Najeriya da ke da bambancin fahimta da shi ke yawan janyo saka ƙafar wando ɗaya da su.

A ranar Talatar nan ne gwamnatin jihar Katsina ta gayyaci Malam Yahaya Masussuka da ya bayyana a gaban wani kwamiti domin kare kansa daga zarge-zarge da malaman jihar Katsina ke yi masa na "cin zarafin malamai da ɓatanci ga hadisan annabi Muhammad SAW."

Masussuka zai bayyana gaban malamai

Gwamnatin jihar Katsinar ta sanar da shirya zama tsakanin malamin da kwamitinin malaman jihar domin ya kare kansa.

Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta ce ta buƙaci malamin ya bayyana a gaban kwamitin malaman jihar domin kare kansa daga wasu fatawowi da yake bayarwa a lokutan karatunsa.

Tun da farko wasu malamai a jihar ne suka shigar da ƙorafinsu ga gwamnatin jihar saboda zarginsa da wuce gona da iri a karatuttukansa.

Bayan ƙorafin malaman ne kuma sai wasu malaman da ke goyon bayansa suka shigar da ƙorafinsu gaban gwamnati cewa wasu na yi wa Sheikh Masussuka barazana da cin mutuncinsa, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

Sanarwar ta ce za kuma a samar da wasu ƙa'idojin wa'azi a jihar bayan zaman da za a yi tsakanin malamin da kwamitin malaman.

Gwamnatin ta kuma ce za ta tabbatar ana bin duka ƙa'idojin da aka cimma tare da hukunta duk wanda ya kauce musu.

Sanawar dai ba ta sanar da ranar da Malamin zai bayyana a gaban kwamitin malam ba.

Tuhume-tuhumen da ake yi wa Masussuka

Wani kwamitin ilimi da ilimantarwa na Dr Muhammad Hussamatu Abbas ne ya gabatar da ƙorafi ga gwamnatin jihar Katsina a kan irin koyarwar Sheikh Yahaya Masussuka, inda kwamitin ya zargi malamin da ɓatanci ga hadisan Manzon ALLAH (SAW).

Ƙwamitin ya buƙaci gwamnati ta shirya zama na musamman don gabatar da hujjoji daga ko wane ɓangare don tabbatar da gaskiyar kowa.

Sheikh Masussuka ya sha musanta cewa yana ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW.

Fahimtar Masussuka

Kamar yadda ba ya ɓoye fahimtarsa, Sheikh Masussuka mutum ne mabiyin fahimtar Ƙur'ani zalla, wani abu da ya sa yake yawan sukar hadisai da ya ce "suna taɓa ƙimar Annabi Muhammad SAW."

A baya-bayan nan ya yi suna da wata sara da yake kira da "Ritaya Dole", da ya ce ya ƙudiri aniyyar sanya wa koyarwar mabiya fahimtar "Salaf" ko kuma da ake kira Ahlussunnah, ko kuma ƴan ƙungiyar Izala, burki.

Wannan al'amari ne ake ganin ya ƙara rashin jituwar da ke tsakanin malamin da mabiya fahimtar Salaf ɗin inda suka yi ta musayar yawu a wa'azozinsu da soshiyal midiya.

Sheikh Masussuka na da gidan rediyo da talbijin da kuma makarantu a garin Dutsen-Ma na jihar Katsina, inda ya ce ya kafa su ne da manufar yaɗa koyarwar Alƙur'ani.

Ziyarar neman haɗin kai

A watan da ya gabata ne, Sheikh Yahaya Masussuka ya fara wata ziyarar da ya kira ta haɗin kai ga malaman ɗarika a birnin Kano da Bauchi da sauran sassan Najeriya.

Malamin ya ziyarci Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda jagora ne na ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya.

Ya kuma gana da wani ɓangare na jagorancin Ƙadiriyya a birnin Kano. Sannan kuma an gano malamin a wani taron Mauludi da aka yi a watan da ya gabata a birnin na Kano.

A ƙarshen makon da ya gabata ne kuma Malam Yahaya Masussuka ya shiga birnin tarayya, Abuja inda ya gabatar da wata lacca mai taken "Yadda kuka mangare wasu to kuma dole ne a mangare ku".

Ana ƙoƙarin rufe bakin Masussuka - Amnesty

Kungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Amnesty International reshen Najeriya ta nuna damuwarta da abin da ta bayyana da ƙoƙarin rufe bakin Sheikh Yahaya Masussuka.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata, Amnesty ta ce "dole ne a dakatar da duk wani ƙoƙarin yin amfani da gwamnati wajen rufe bakin Malam Masussuka tare da rufe makarantunsa duk kuwa da cewa babu wasu shaidu da ke nuna cewa ya saɓa doka."

Sanarwar ta ƙara da cewa "akwai taron dangi a ƙoƙarin hukunta Malam Masussuka kawai saboda yana wa'azinsa cikin lumana. Malamin ya yi suna wajen yin wa'azi domin gujewa tsauraran aƙidu da wuce gona da iri sannan kuma yana ƙwarara gwiwar zama a tattauna."

Daga ƙarshe Amnesty International ta ce kundin dokokin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowa ƴancin addini da tunani "saboda haka ya zama wajibi ga hukumomin Najeriya su bai wa Malam Yahaya Masussuka kariya kamar yadda dokokin ƴancin ɗan adama suka tanada."