Ko malamai za su iya haɗuwa domin magance matsalolin Musulmai?

Lokacin karatu: Minti 3

Wani abu da ke ci wa al'ummar Musulmin Najeriya tuwo a ƙwarya a wannan lokaci shi ne yadda wasu malamai ke karafkiya a soshiyal midiya, inda suke mayarwa juna martani sannan wasu lokutan daga bisani su yi kalmomin 'ɓatanci'.

Bugu da ƙari, a baya-bayan nan an samu malaman da ke sakin bakin da munana kalamai ga Annabi Muhammadu SAW da sunan kare aƙida ko kuma mayar da martani a kafafen sada zumunta.

Ana dai alaƙanta al'amarin da rashin masu faɗa wa malaman da ke irin wannan wa'azi gaskiya daga dukkan ɓangarorin Musulmai.

A ranar Laraba ne wata gamayyar ƙungiyoyin addinin Musulunci na arewacin Najeriya suka gudanar da wani taron neman haɗin kai a tsakaninsu wanda aka yi a birnin Kaduna.

Abin tambaya yanzu shi ne ko taron malaman Musuluncin zai iya warware wannan matsalar da ma sauran matsalolin da suke addabar Musulmin yankin?

BBC ta tattauna da wasu malamai a wurin taron da suka bayar da tabbacin yiwuwar al'amarin.

Sheikh Kabiru Gombe

Sheikh Kabiru Gombe wanda ɗaya ne daga cikin jagororin ƙungiyar Izala ya shaida wa BBC cewa taron na haɗin kai ne kasancewar babu wani lokaci da Musulmin Najeriya ke buƙatar junansu kamar yanzu.

"Halin da Musulmin najeriya suke ciki a wannan ƙasa, babu wani lokaci da muke buƙatar juna kamar yanzu. Duk da banbance-banbance da muke da su a fahimtar addini da aƙida to akwai wasu matsalolin rayuwa da ke tasowa al'umma da babu wata ƙungiya guda da za ta iya magance ta ita kaɗai.

Misali idan ka duba matsalar tsaro da ke faruwa a ƙasar nan za ka abin na shafar kowa ba tare da tantance ɗan Izala ko ɗarika ko wani abu mai kama da haka. Haka sauran fannonin rayuwa an bar mu a baya misali ilimi, tattalin arziƙi da kiwon lafiya da sauran su. Idan da mun haɗu wuri guda to da za mu ceci kanmu daga halin da muke ciki," in ji Kabiru Gombe.

Sheikh Ibrahim Maihula

Sheikh Ibrahim Shehu Maihula wanda yana cikin wakilai daga ɗarikar Tijjaniyya ya ce lokaci ya yi da Musulmi za su haɗa kansu.

"Babu shakka duk mai imani kuma wanda ya san matsaloloin da Musulmin Najeriya ke fuskanta zai yi murna da wannan al'amari musamman wajen samar da daidaito a tsakanin Musulmi. Sannan kuma mu yi wa kanmu iyaka ta yadda dukkan wani mai wa'azi yana da jagoran da zai iya sa shi ko kuma hana shi domin rashin hakan ya sa muka tsinci kanmu a halin da muke ciki," in ji Maihula.

Dr Bashir Aliyu Umar

Dr Bashir Aliyu Umar wanda shi ne shugaban kungiyar Majalisar Ƙoli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya ya lissafa abubuwan da taron ke son cimma a karshe.

  • Za a samu hanyoyin da za a magance wannan ta'addanci da ake yi domin samun lafiya.
  • Za kuma a lalubo hanyoyin da za a faɗakar da al'ummar Musulmi da ka da su bari a rarraba kansu da sunan kabilanci.
  • Sannan a shiryar da al'umma kan yadda za su rinka amfani da kafofin yaɗa labarai da kuma maganin masu yin wa'azin ɓatanci a soshiyal midiya.

Abu huɗu da za su kawo ƙarshen kalaman ɓatanci

Wani malami a Kano wanda muka ɓoye sunansa ya shaida wa BBC cewa batun haɗin kan malamai domin yakar al'amuran da suka shafi wa'azi da kalaman ɓatanci musamman a soshiyal midiya mai yiwuwa ne amma sai an ɗauki wasu matakai guda huɗu.

"Abin yana da sauƙin faɗi amma yana da wuyar aikatawa saboda yanzu malaman nan sun haɗu sun yi magana amma da sun koma wuraren wa'azinsu sai ka ji labari ya sauya. Wannan shi ne na farko.

Abu na biyu kuma dole ne sai mun fifita addinin Musulunci da batun haɗin kai fiye da irin muhimmancin da muka bai wa ƙungiyoyi da aƙidunmu. Mun ga yadda wasu suke ƙoƙarin kare ƴan ƙungiyarsu ko ɗarikarsu dangane da kalaman ɓatanci ko kuma na sakin baki ga annabi.

Sai kuma abu na uku dole sai gwamnati ta shigo cikin tsari ta yi dokar wa'azi bisa gaskiya da adalci ba tare da siyasa ba. Mun ga yadda wasu ƙasashen suke da irin waɗannan dokokin.

Abu na huɗu kuma shi ne ƴan an gayyaci ƙungiyoyin mabiya Shi'a da masu da'awar Qur'ani da ake kira Ƙur'aniyyun? Shin shugabannin tafiyar sun ma amince cewa su waɗannan Musulmai ne su ma? Idan har ba a saka su cikin tafiyar ba to akwai sauran rina a kaba," in ji malamin.