Trump ya ce 'Ukraine ta fi wuyar sha'ani fiye da Rasha'

Donald Trump
Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana ganin Rasha ta fi saukin hulda fiye da Ukraine a yunkurin samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.

Ya ce Amurka na samun kyakkyawar fahimta tsakaninta da Rasha, kuma mu'amula a ganinsa mu'amula ta fi sauki da Moscow fiye da Kyiv.

Wannan na zuwa mako guda bayan da musayar yawun da aka yi a Fadar White House, inda Trump ya caccaki shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky kan abin da ya kira rashin "mutunta Amurka"

Yanzu alamu ya nuna manufofin Trump na kasashen ketare a yan kwanakin nan sun fi karkata kan sasanta rikicin Ukraine, bayan da Amurka ta dakatar da ba kasar tallafin soji da kuma bayanan sirri.

Amurka dai na son shugaba Zelensky ya amince da yarjejeniyar da za ta ba kasar damar kula da ma'adinan Ukraine da kuma gaggauta amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta da Rasha.

Shugaba Trump ya ce nan gaba ne za a tattauna wannan kuma abu ne mai sauki.

Rasha ta kai hare-haren makamai masu linzami da na jirage marar matuka a cibiyoyin makamshi na Ukraine a ranar Alhamis

A yanzu shugaban ya dawo yana cewa zai kakaba sabbin takunkumi kan Rasha kan luguden wutar da take ci gaba da yi a Ukraine.

Amma Mr Trump ya ce Ukraine na ba shi ciwon kai tare da cewa bai san ko yan Ukraine na son a kawo karshen yakin ba.

Ya ce ya yi imanin Putin na son kawo ƙarshen yakin amma ba ya da tabbas kan Ukraine.

"Ban sani ba ko Ukraine na son sasanci," a cewar Trump bayan da aka tambaye shi dalilin dakatar da ba Ukraine da tallafi.

Hulɗar Trump da Putin dai na zama barazana ga aminan Amurka na Nato, saboda ƙasashen yammaci sun yanke alaƙa da RAsha tun Fabrairun 2022 da ta ƙaddamar da mamayar Ukraine.

A makon gobe ne jami'an Amurka za su tafi Saudiyya domin haduwa da Mr Zelensky wanda ke fuskantar matsin lamba daga Trump ya amince da bukatunsa.