Mece ce makomar alaƙar Zelensky da Trump da Tarayyar Turai?

Zelensky ya fice daga White House bayan ɓaɓatu da Trump a White House

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Zelensky ya fice daga White House bayan ɓaɓatu da Trump a White House
    • Marubuci, Laura Gozzi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Europe reporter
    • Marubuci, Thomas Mackintosh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, London
  • Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya koma gida Kyiv bayan balaguron da ya yi na kwana uku, inda a ciki aka ba shi umarnin ficewa daga Fadar White House ta Amurka ranar Juma'a bayan ɓaɓatun da suka yi da Donald Trump da mataimakinsa JD Vance.

Ya fi samun kyakkyawar tarɓa a birnin Landan a ƙarshen mako, inda Firaminista Keir Starmer ya tarɓe, ya kai wa SArki Chales ziyara kuma aka nuna masa babbar kara daga shugabannin Tarayyar Turai yayin taronsu na ranar Lahadi.

Wannan ya sha bamban sosai da abin da ya faru a fadar ta White House.

Bayan taron na Landan, Mista Starmer ya ba da shawarar shugabannin Turai su kafa "wata tawaga" domin kare Ukraine - amma dai babu cikakken bayani kan yadda za a gudanar da hakan.

Ga bayanai na baya-bayan nan game da alaƙar Zelensky da Trump, da kuma shirin Turawan na kare Ukraine.

Ina matsayin alaƙar Zelensky da Trump a yanzu?

Shugaban Ukrain Volodymyr Zelenskiy yake sauraron tambayoyi yayin wata ganawa da 'yanjarida

Asalin hoton, Reuters

Cikin wani jerin saƙonni a dandalin X a safiyar Asabar, Shugaba Zelensky ya ce akwai Ukraine da Amurka su "zama masu faɗa wa juna gaskiya" domin fahimtar inda suka sa gaba - kuma yana son Amurka ta "tsaya da kyau" wajen goyon bayansu.

Da yake magana da gidan talabijin na Fox News jim kaɗan bayan ɓaɓtun, Zelensky ya ce sa'insar da suka yi abu ne "mai wuya", sannan ya gode wa Amurkawa da Trump.

Sai dai bai nemi afuwa ba duk da yadda wasu 'yanmajalisar Amurka suke kiraye-kirayen ya yi hakan.

Fadar ta White House ba ta ce komai ba kai-tsaye game da lamarin, inda akasarin 'yanmajalisar jam'iyyar Republican suka goya wa Trump da Vance baya.

Ta yaya shugabannin Turai suka mayar da martani?

Saƙonnin nuna goyon baya ga Zelensky sun yi ta ɓulla bayan ya fita daga White House a yammacin Juma'a.

Waɗanda ba a ji muryarsu wajen yaba wa Zelensky ba akwai Firaministar Italiya Giorgia Meloni, wadda ba ta son lalata alaƙarta da Trump, da kuma na Hungary Victor Orban, wanda ya yaba wa Trump ɗin game da "tsayawa da kyau wajen neman zaman lafiya".

Zuwa lokacin da aka fara taron Landan ranar Lahadi, an ga yadda shugabannin Turan ke nuna ya kamata a aikata abin da ake faɗa ba tare da sun ɗaukaka batun cewa suna buƙatar sa hannun Amurka ba.

A ƙarshen taron, Starmer ya zayyana wani yunƙuri mai matakai huɗu na neman zaman lafiya wanda ya ƙunshi cigaba da aika wa Ukraine makamai, kasancewar Ukraine a wurin tattauna zaman lafiya, ƙarfafa tsaron Ukraine, da kuma kafa tawagar ƙawance da za ta tura dakaru Ukraine.

Yaya batun tabbacin tsaro daga Tarayyar Turai?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Starmer ya ce hikimar tura dakaru Ukraine - da za ta ƙunshi sojan ƙasa da na sama - ta samu goyon bayan ɓangarori da yawa, amma ya bar wa ƙasashen su tattauna kan batun a cikin gida.

Ƙasashen Scandinavia sun nuna cewa akwai yiwuwar su goyi bayan yunƙurin.

Firaministan Denmark Mette Frederiksen ta ce "tunaninta a buɗe yake" kan batun, yayin da na Sweden Ulf Kristersson ya ce ƙasarsa a shirye take ta bai wa Ukraine tabbacin tsaro - idan Amurka ta yarda da tsarin.

Firaministar Italiya Giorgia Meloni ta fi son a sake zaman tattaunawa da zai ƙunshi Amurka, ba na Turawan kawai ba, abin da ta ce ya ba ta "mamaki".

Sai dai kuma Poland - wadda ta daɗe tana goyon bayan Ukraine - tuni ta ce ba za ta tura dakaru ba, duk da cewa ba ta ƙin bai wa Ukraine ɗin tallafin kayayyaki da makamai.

Yanzu shugabannin Turai na da 'yan kwanaki na yin tunani game da abin da ke faruwa kafin su sake haɗuwa a binrin Brussels ranar Alhamis don ganawa kan tsaro, inda shugabar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen za ta gabatar da abin da ta kira "babban tsarin dawo da martabar Turai".

Daftarin yarjejeniyar zaman lafiya na Macron

Emmanuel Macron, da Keir Starmer, da Volodymyr Zelenskiy sun halarci taro a binrin Landan ranar Lahadi

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Emmanuel Macron, da Keir Starmer, da Volodymyr Zelenskiy sun halarci taro a binrin Landan ranar Lahadi

A ranar Lahadi da dare jaridar Le Figaro ta ruwaito cewa Shugaban Faransa Emmanuel Macron da na Birtaniya Keir Starmer sun gabatar da ƙudirin zaman lafiya na wata ɗaya tsakanin Rasha da Ukraine "ta ruwa da ta sama".

Duk da dai babu cikakken bayani, ɓangarorin za su ƙulla yarjejeniyar mako huɗu a sararin samaniya, da ta ruwa da kuma kan tashoshin makamashi. Amma Macron ya ce ban da faɗa ta ƙasa saboda zai yi wuya a iya sa ido kan dakaru.

Amma a ranar Litinin, babban jami'in sojan Birtaniya ya ce "ba a cimma kowace irin yarjejeniya ba game da yadda za a cimma hakan".

Duk wata yarjejeniya dole ne ta samu amincewar Rasha kuma zuwa yanzu babu wata alama da ke nuna za su yi hakan.

Me Rashan ta ce?

Maria Zakharova

Asalin hoton, Getty Images

Duk da cewa Vladimir Putin bai ce komai ba a hukumance game da abin da ya faru a White House, mai magana da yawun Fadar Kremlin Maria Zakarova ta ce "cikakkiyar rashin nasara ce ga Ukraine a fannin difilomasiyya".

A ranar Litinin da safe, wani mai magana da yawun fadar, Dmitry Peskov, ya soki taron na birnin Landan.

"An yi ta fitar da sanarwa a wurin game da ƙara yawan kuɗin da ake bai wa Ukraine cikin gaggawa. Tabbas wannan ba shi cikin shirin zaman lafiya, shirin cigaba da faɗa ne," in ji Peskov.

"Sauran ya danganta ga irin yarjejeniyar da tsara kuma aka gabatar domin tattaunawa. Za mu goyi bayan duk wani yunƙuri a kan wannan."