Ko Trump na goyon bayan Rasha ne don raba ta da China?

Goyon bayan da Trump ke bai wa Shugaba Putin na Rasha gagarumin sauyi ne a manufar ƙasashen waje ta Amurka kan Rasha

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Goyon bayan da Trump (hagu) ke bai wa Shugaba Putin na Rasha gagarumin sauyi ne a manufar ƙasashen waje ta Amurka kan Rasha
    • Marubuci, BBC World Service and BBC Global China Unit
  • Lokacin karatu: Minti 6

Shugaban Amurka Donald Trump na ƙara ɗasawa da Rasha, abin da ake gani a matsayin gagarumin sauyi game da manufar Amurka ta ƙasashen waje.

Ya goyi bayan Putin game da maganar tattaunawar zaman lafiya don kawo ƙarshen yaƙin Ukraine, kuma ya matsa wa Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky domin ya amince da buƙatun Rasha masu tsauri bayan ta auka wa ƙasarsa.

Ya kuma faɗa wa shugabannin Turai cewa kada su tsammaci cewa Amurkar za ta ci gaba da taimakawa wajen ba su tsaro.

Duk waɗannan na nuna alamun goyon baya ga Putin da kuma ɗiga ayar tambaya kan ko Amurka na ƙoƙarin aiwatar da gagarumin sauyi ne a tsarin mu'amalarta da ƙasashen waje.

Shin wani shiri ne na ƙoƙarin janye Rashar daga wajen China? Ko kuwa dai Trump ya fi saka buƙatunsa ne kawai a gaba da kuma abotarsa da Putin?

Ta yaya gwamnatin Trump ta dinga goyon bayan Rasha?

Babbar alama ta farko-farko ta zo ne ranar 12 ga watan Fabrairu, lokacin da Trump ya tattauna ta waya da Putin tsawo minti 90.

Bayan nan, ya dinga matsa wa Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky don ya amince da yarjejeniyar tsagaita wuta - yana mai shawartarsa da ya bar wa Rashar yankunan ƙasarsa da ta mamaye ba tare da ba shi wani tabbaci ba game da tsaron ƙasarsa.

Ya bayyana hirar da suka yi ta waya da Putin da cewa: "Mun amince mu yi aiki tare, kafaɗa da kafaɗa, ciki har da ziyartar ƙasashen juna."

Trump ya kuma ce Ukraine ba za ta iya shiga ƙungiyar ƙawance ta Nato ba bayan yaƙin - abin da wanda ya gada Joe Biden ya yi alƙawari, amma kuma Rasha ta nuna zazzafar adawa da hakan.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a fadar White House yayin ganawa da Shugaba Donald Trump ranar 28 ga watan Fabrairu, 2025.

Asalin hoton, Reuters

Tun daga lokacin, Trump ya kira Zelensky da "maras ƙwarewa" da kuma "mai mulkin kama-karya", kuma ya faɗa masa baki da baki cewa "bai kamata Ukraine" ta takalo yaƙin ba - kamar yadda Putin ya saba faɗa.

Trump ya ƙi ya goyi bayan dakarun ƙasashen Turai da za a tura domin kiyaye zaman lafiya bayan gama yaƙin a Ukraine. Rasha ta yi watsi da wannan yunƙurin.

AMurka ta kuma goyi bayan Rasha a ƙuri'ar da aka kaɗa a Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) da zimmar yin tir da mamayar Rasha a Ukraine.

Ko Amurka na shirin janye Rasha daga wajen China ne?

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce ba shi son ganin Rasha "ta zama ƙawar China"

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce ba shi son ganin Rasha "ta zama ƙawar China"
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wannan ɗasawar da Rasha - da kauce wa ƙawayenta ƙasashen Turai - ya sauya manufar Amurka ta ƙasashen waje ta tsawon shekara 80 - duk da cewa har yanzu babu tabbas kan ita ce sabuwar manufar.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta Breitbart ranar 25 ga watan Fabrairu cewa Shugaba Trump na da aniyar lalata alaƙa tsakanin Rasha da China.

Ya ce: "Ba na tunanin cewa yanayi irin na cewa Rasha ta zama kullum ƙaramar ƙawar China, ta dinga yin duk abin da China ke so saboda sun dogara da su - ina ganin hakan ba zai yi wa Rashar daɗi ba, ba zai yi wa Amurka da Turai kyau ba, ko ma duniya baki ɗaya."

A cewarsa, hakan zai zama abu mai haɗari ga Amurka, saboda "ana maganar ƙasashe biyu ne masu makamin nukiliya da ke adawa da Amurka".

Rubio ya ƙara da cewa Amurka za ta nemi ƙalubalantar ƙawancen kasuwanci da China ke ginawa wanda ake kira da Belt and Road Initiative a Turance.

China ta mayar da kakkausan martani kan kalaman Rubio, inda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajenta Lin Jian ya ce: "Yunƙurin Amurka na haddasa rashin jituwa tsakanin Rasha da China ba zai yi nasara ba. China da Rasha na da tsare-tsaren cigaba da na hulɗar difilomasiyya na tsawon lokaci."

Shugaban Amurka Richard Nixon (tsakiya) ya ziyarci China a 1972, ziyarar da ake yi wa kallon babbar dabara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Amurka Richard Nixon (tsakiya) ya ziyarci China a 1972, ziyarar da ake yi wa kallon babbar dabara

Dabarar da Rubio ya bayyana - ta janye Rasha daga wajen China - za ta iya zama makwafin nasarar da Nixon ya yi wajen janye China daga Tarayyar Soviet.

Nixon ya ƙulla alaƙa ne da China, inda suka ware Rasha. Shi kuma Trump na son alaƙa da Rasha ne don ware China.

Bisa taimakon mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Henry Kissinger, Nixon ya saka hannu kan yarjejeniya da China a 1972, abin da ya kawo ƙarshen alaƙarta da Tarayyar Soviet da kuma adawar da suke yi da Amurka.

"Amurka ba ta son Rasha ta zama kamar wata abar mallakar Rasha," in ji Klaus Welle, farfesa a kwalejin London School of Economics. "Hakan na nufin Rasha na sayar wa China kayayyakin da take sarrafawa da araha, wanda hakan ke bai wa Chinar dama sosai sama da Amurka."

Sai dai kuma, Dr Dana Allin na cibiyar International Institute for Strategic Studies a Birtaniya na ganin da wuya Putin ya rungumi alaƙar hannu bibiyu.

"Trump zai iya tunanin cewa abin zai yiwu, amma dai yanzu Marco Rubio muka ji yana faɗa da kuma 'yan gargajiyar jam'iyyar Republican, waɗanda kuma ba su ne ke tafiyar da al'amura ba a Fadar White House," in ji shi.

Ko dabarar za ta yi aiki?

Amurka za ta iya fuskantar jan aikin raba China da Rasha.

Ƙasashen biyu sun ayyana "shirin da babu iyaka" a alaƙarsu jim kaɗan kafin Rasha ta mamaye Ukraine, kuma tun daga nan kasuwanci tsakaninsu ya hauhawa.

China ce kan gaba wajen sayen ɗanyen mai daga Rasha, inda ta sayi na dala biliyan 62 a 2024. A 2021, kashi biyu cikin uku kawai take saya. Bayan Rasha ta auka wa Ukraine, ƙasashen Turai sun saka wa man Rashar takunkumai, abin da ya sa China ta ƙara samun damar sayen sa.

Haka nan, China babbar mai shigar da kayayyakin fasaha ce zuwa Rasha, ciki har da kwamfuta, da kayayyakin haɗa ta (waɗansu ma ana amfani da su wajen haɗa makamai).

China ce babbar mai sayen ɗanyen man fetur na Rasha

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, China ce babbar mai sayen ɗanyen man fetur na Rasha

Farfesa Yang Cheng na Shanghai Academy of Global Governance and Area Studies ya ce da wuya Rasha da Amurka su ƙulla cikakkiyar alaƙa saboda "tarihin rashin yarda da bambancen aƙida" tsakaninsu.

"Rasha za ta ci gaba da riƙe 'yancin kanta fiye da kasancewa wata abar amfani ga manufofin harkokin wajen Amurka," a cewarsa.

"Ina ganin Putin zai karɓi tayin da Amurka ta gabatar a yanzu," in ji Dr Henrik Wachtmeister na cibiyar Swedish Institute of International Affairs, "amma ba zai yarda ya sadaukar da alaƙarsa da China ba duk irin alƙawarin da Amurka za ta yi masa."

"Rasha da China ƙawaye ne na al'ada musamman game da ma'adanai," a cewar Dr Wachtmeister. "Rasha da Amurka kuma ba haka suke ba. Masu gasa ne a tsakaninsu a kan mai da iskar gas."

Ko Trump na ɗasawa da Putin ne saboda son zuciyarsa kawai?

Trump (hagu) da Putin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Trump (hagu) da Putin

Dr Allin na ganin son zuciyar Trump ne kawai ya sa yake goyon bayan Rasha da Putin, ba manufar harkokin wajen Amurka ba.

AN zargi Rasha da yin kutse a zaɓen Amurka da ya gabata, kuma aka zargi tawagar Trump da haɗa baki da ita.

Yayin ganawarsa da Zelensky a White House, Trump ya ce: "Na san shi [Putin] tsawon lokaci. Mun yi faɗi-tashi tare da shi game da zargin hannun Rasha a zaɓenmu."

"Trump na tunanin shi da Putin ɗaya ne, mutanen da ake yi wa bi-ta-da-ƙulli," a cewar Dr Allin.