Trump ya ce Hamas za ta ɗanɗana kuɗarta

Trump

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaba Trump ya bukaci Hamas ta gaggauta sakin dukkan mutanen da take garkuwa da su a Gaza - inda ya yi barazanar cewa za ta dandana kudarta idan har ba ta saki sauran mutanen ba.

Ya kuma yi kira ga Hamas ta fice daga yankunan Falasdinawa tare da yin gargadi ga al'ummar Gaza cewa za su fuskanci mutuwa idan har ba a saki mutanen da Hamas ke tsare da su ba.

Trump ya yi gargadin ne ga Hamas a sakon da ya wallafa a kafarsa ta sada zumunta inda ya ce zai sa Isra'ila ta kammala aikin da ta soma wajen kakkabe Hamas.

Gargadin na Trump na zuwa ne yayin da Fadar White House ta tabbatar da cewa tana tattaunawa da Hamas domin sakin mutanen da kungiyar ke tsaro da su.

Ya ce Hamas za ta dandanta kudarta idan har ba ta saki sauran wadanda take tsare da su, amma ba tare da ya bayyana irin taimakon da zai ba Isra'ila ba.

An dauki lokaci dai Amurka na kaucewa tattaunawa da Hamas, musamman karkashin manufofofin kasashen waje na kasar na kaucewa tattaunawa da kungiyar da Amurka ta ayyana ta 'yanta'adda.

Trump ya yi gargadi ga shugabannin Hamas su fice Gaza, tare da gargadi ga fararen hula, inda ya ce makoma mai kyau na jiransu amma idan ba a saki wadanda aka yi garkuwa da su ba, a cewearsa za su fuskanci mutuwa.

Ba dai wannan ne karon farko da Trump ke barazana ga Hamas ba. A Disamba ya ce Kungiyar za ta dandanta kudarta idan har ba ta saki wadanda ta kama ba bayan rantsar da shi.

Kayan abinci dai sun kara tsada bayan da Isra'ila ta dakatar da shigar da kayan agaji.

Mai magana da yawun Fadar White House Karoline Leavitt ta tabbatar da cewa ana tattaunawa da Hamas domin sakin mutanen da kungiyar ke tsare da su.

Ta ce an tuntubi Isra'ila kafin soma tattaunawar.

Wata majiya ta Falasdinu ta tabbatar wa da BBC cewa an tattauna tsakanin Hamas da jami'an Amurka.

Isra'ila ta ce har yanzu akwai mutum 59 da Hamas ke tsare da su a Gaza, ana tunanin 24 na raye. Akwai Amurkawa cikin wadanda aka kama.