Yadda dabanci da ƙwacen waya ke addabar Kano

Asalin hoton, Getty Images
Ayyukan dabanci da kwacen waya tamkar ɗanjuma ne da ɗanjummai a jihar Kano, inda yawancin masu ƙwacen wayar da ake kamawa kan kasance ƴandaba.
Haka su ma ƴandabar idan aka kama su bayan bincike akan gano suna da alaƙa da ƙwace ko kuma satar wayoyin al'umma.
A baya-bayan nan bayanai sun nuna cewa al'ummar birnin Kano ba sa iya sakin jikinsu su yi cikakkiyar mu'amila da zarar dare ya yi saboda tsoron masu ƴandaba da masu ƙwacen waya.
Ku san za a iya cewa babban kaso na ayyukan jami'an tsaro na kan masu daba da ƙwacen waya, inda su ma malaman asibiti suke kashe mafi yawancin lokutansu wajen kula da raunukan da aka samu sakamakon daba ko ƙwace waya.
'Mutum 1000 sun samu raunuka a watanni shida'

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Abdurrahman Ali, shugaban ƙungiyar likitoci ta jihar Kano ya shaida wa BBC cewa wata ƙididdiga da suka yi a sashen gaggawa na asibitin Murtala da ke birnin Kano ta nuna yadda ayyukan daba da ƙwacen waya suka jikkata mutum fiye da 1000 a watanni shidan da suka gabata.
"A watanni shida da suka gabata an sami sama da mutum 1000 da suka samu rauni sakamkon ayyukan ƴandaba ko kuma na ƙwacen waya. Za ka ga wasu wuƙa ce aka caka musu a ciki wasu kuma a baya.
Wani ma sara aka kawo masa a kansa amma zai sa hannu ya kare wani kuma a kansa za ka ga an sare shi. Sannan wani lokacin ma su kansu mutanen da ke saran jama'a su kan fuskanci matsala musamman idan jama'a suka yi musu tara-tara. Za ka an kawo su asibiti da raunuka iri-iri.
Gaskiya abu ne da ke ƙaruwa a kullum . Kuma yana ƙara nauyi a kan ayyukanmu na asibiti. Ana yawan samun mace-mace ma wani lokacin idan raunin ya wuce ƙima." In ji Dakta Abdurrahman Ali.
'Yadda suka so caka min wuƙa a ciki kan waya'
Wani bawan Allah da bai so a bayyana sunansa ba ya shaida wa BBC yadda wasu masu ƙwacen waya suka so su soka masa wuƙa a ciki domin su karbi wayar da ke hannunsa.
"Ina dawowa daga aiki da misalin ƙarfe tara na dare na yi arangama da su. Wallahi kawai sai ga wasu mutum biyu a babur ɗaya ya sauka ya sha gabana ɗaya kuma ya zare wuƙa ba tare da ya ce min komai ba kawai ya yi ƙoƙarin caka min wuƙar a cikina amma sai na yi amfani da hannuna na kare.
Hakan ne ya sa ya farke min hannu. Kuma babu abin da nake ji yana cewa sai ba ni waya ba ni waya. Nan take na sallama masa wayar kuma suka hau babur suka tafi" In ji wanda ya haɗu da ɓarayin waya a Kano.











