Matakai 10 da ƙasashen Larabawa da Musulmi ke so a ɗauka kan Isra'ila

Shugabannin ƙasashen Musulmi

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Daga cikin ƙudirorin da shugabannin suka cim ma har da neman a saka wa Isra'ila takunkumi da dakatar da ita daga Majalisar Ɗinkin Duniya
Lokacin karatu: Minti 5

Taron musamman na shugabannin kasashen Larabawa da Musulmi ya jaddada adawarsa ga yakin da Isra’ila ke yi da Hamas a Zirin Gaza, da kuma mamayen da take yi a Lebanon da sunan yaki da Hezbollah.

Shugabannin kasashen da suka halarci taron da aka kammala ranar Litinin bisa jagorancin Saudiyya a birnin Riyadh, sun zartar da wasu kudirori da dama da suke neman duniya ta dauka da nufin kawo karshen mamaye da hare-haren da Isra'ila ke yi kan Falasdinawa da sauran ƙasashe na yankin Gabas ta Tsakiya.

Taron ya jaddada ƙudurinsa na ganin an samar da ƙasar Falasdinu mai cin gashin kanta, da kuma gabashin Birnin Ƙudus a matsayin babban birnin Falasɗinun.

Ga wasu 10 daga cikin muhimman ƙudurorin ko matakai da taron ya cimma kamar yadda wata sanarwar bayan taro ta bayyana.

Dakatar da Isra'ila daga Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD)

Taron ya zartar da ƙudurin fara neman haɗin kan hukumomi da ƙasashen duniya kan neman a dakatar da kasancewar Isra'ila da dukkanin wasu hukumomi masu alaƙa da ita daga Majalisar Ɗinkin Duniya.

Sun ce ta saɓa wa dokokin majalisar da barazanarta ga zaman lafiya da tsaro na duniya, tare kuma da ƙin cika ƙa'idojin zamanta mamba a majalisar bisa shawarar da Kotun Duniya ta zartar ranar 19 ga watan Yuli na 2024.

Shugaba Bola Tinubu

Asalin hoton, Nigeria State House

Falasɗinu a zaman ƙasa kuma mamba a MDD

Taron ya amince ya nemi goyon baya na ƙasashen duniya don tabbatarwa da kuma amincewa da samar da ƙasar Falasɗinu mai babban birninta a gabashin Birnin Ƙudus da zama cikakkiyar mamba a Majalisar Ɗinkin Duniya.

A bisa wannan ƙuduri taron ya yaba da ƙoƙarin ƙasar Algeria kasancewarta mamba a kwamitoci biyu na Majalisar tare da neman ƙasar ta miƙa daftarin neman yarda da Falasɗinu ta zama cikakkiyar mambar Majalisar, ba ya yaba wa ƙasar ta Algeria kan goyon bayan da take bai wa Falasɗinu.

Haramta samar wa Isra'ila makamai

Taron ya zartar da ƙudurin kira ga dukkanin ƙasashen duniya da su haramta kai wa Isra'ila makamai da albarusai, inda za su nemi ƙasashe su bi sahun shawarar Turkiyya da sauran ƙasashe da ƙungiyar ƙasashen Larabawa da ta Musulmi domin rattaba hannu a kan wasiƙa ta haɗin gwiwa da za a aika zuwa ga kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, da shugaban babban taron Majalisar da kuma Babban Sakataren Majalisar, kan neman a dakatar da bai wa Isra'ila makamai, tare da gayyatar dukkanin ƙasashe mambobin Majalisar su sa hannu.

Isra'ila na aikata kisan kiyashi

Ƙasashen da suka halarci taron na Riyadh sun yi kakkausar suka tare da yin Alla-wadarai da irin miyagun laifukan da Isra'ila take aikatawa a Gaza, inda suka kira laifin da kisan kiyashi, sakamakon manyan ƙabarurruka da aka gano da kisan Falasɗinawa da take yi a fili da neman share wata al'umma daga doron ƙasa da sauran abubuwa da Isra'ilar ke aikatawa musamman a arewacin Gaza a makonnin da suka gabata.

Ya kamata kotun manyan laifuka ta duniya ta yi aikinta

Ƙasahen sun zartar da ƙudurin neman kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta gaggauta bayar da izinin kama jami'an soji da farar hula na Isra'ila da suka aikata laifukan da kotun ke da hurumin yin shari'a a kai- laifukan da aka aikata a kan Falasɗinawa.

Sanya wa Isra'ila takunkumi

Ƙasashen za su yi kira ga kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙasashen duniya su ɗauki matakan da suka wajaba da suka haɗa da sanya wa Isra'ila takunkumi da hana ta abubuwan da take yi na saɓa doka a yankunan da Isra'ilar ta mamaye a Gaɓar Yamma, da ke naƙasu ga manufar samar da ƙasashe biyu masu 'yanci -Isra'ila da Falasɗinu.

Dakatar da Isra'ila daga mamayar da take a yankuna Falasɗinawa, tare da taka mata birki a kan keta dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya da take yi da saura dokokin duniya.

Hukunta 'yan kama-wuri-zauna

Taron ya yi Alla-wadarai da abubuwan da Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna ke yi wa Falasɗinawa a garuruwan da suka mamaye da kuma kadarorin Falasɗinawan, bisa abin da suka kira da goyon baya tare da tmakaman gwamnatin Isra'ila.

A kan haka taron ya buƙaci hukunta Yahudawan a kan miyagun laifukan da suke aikatawa a kan Falasɗinawa da kadarorinsu.

Neman a ayyana yahudawa 'yan kama-wuri-zauna da ƙungiyoyinsu a matsayin'yan ta'adda

Neman a ƙaurace wa kayayyakin da Yahudawan 'yan kama-wuri-zauna ko kamfanoninsu ke sayarwa.

Tare da fitar da jerin sunayen kamfanonin da ke cin moriyar kama-wuri-zaunan a nuna su a duniya domin yi musu tofin Allah-tsine.

A yi kira ga dukkanin ƙasashen duniya su hana 'yan kama-wuri-zauna ciki har da waɗanda suke zaunea a gabashin birnin ƙudus shiga ƙasashensu.

Tallafa wa Falasɗinawa

Shugabannin sun zartar da ƙudurin bayar da dukkanin goyon baya na siyasa da diflomasiya ga Falasɗinawa, da kuma Falasɗinu domin tabbatar da haɗin kan Falasɗinawa, da kuma mayar da su kan gudanar da iko a kan dukkanin yankunan da Isra'ila ta mamaye ciki har da Gaza tare da haɗe Zirin da Gaɓar Yamma da kuma Birnin Ƙudus.

Bayan haka ma kuma da tallafa wa Falasɗinawa ta fannin tattalin arziƙi, ta hanyar ttaimakawa ayyukanta na jinƙai da sake gina Gaza da bayar da gudummawa ga kasafin kuɗin Falasɗinun da tilasat wa Isra'ila ta saki kuɗaɗen haraji na Falasɗinu.

Dakatar da kutse a Gaza da Lebanon

Taron ya ɗora wa kwamitinsa bisa jagorancin Saudiyya ya ci gaba da aikinsa tare da matsa lamba da faɗaɗa aikinsa domin kawo ƙarshen kutsen Isra'ila a Lebanon da dukkanin yankunan Falasɗinu, da yadda hare-haren na Isra'ila ke barazana da keta 'yancin ƙasashen Syria da Iran da Iraq.

Yaba wa Tarayyar Afirka

Taron ya yaba da sanya hannu tare da amincewa da aka yi da ƙudurin taimaka wa dukkanin buri da manufofi da harkokin Falasɗinawa, wanda ƙungiyar asashen Larabawa da ƙungiyar haɗin kan musulmi da kuma ƙungiyar ƙasashen Afirka (AU) suka samar, tare da yaba wa ƙungiyar ta ƙasashen Afirka a kan cikakken matsayin da ta ɗauka kan goyon bayan Falasɗinawa a taron na Riyadh.

Manyan sakatarorin ƙungiyoyin biyu - Kungiyar kasashen Larabawa da kuma ƙungiyar haɗin kan Musulmi za su ci gaba da sa ido wajen ganin ana aiwatar da ƙudurorin da taron na Riyadh ya zartar, da kuma bayar da rahoto akai-akai ga shugabannin ƙasashen.