Tun da Isra'ila ta kashe Sinwar, me ya hana dakatar da buɗe wuta a Gaza?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Soha Ibrahim
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- Lokacin karatu: Minti 6
Kurarin da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi na cewa yaƙin na Gaza bai ƙare ba har sai ya kawo ƙarshen Hamas bayan kisan shugaban ƙungiyar, Yahya Sinwar, ya kawar da duk wani fata da burin ganin ƙarshen yaƙin cikin sauri.
Shugabannin ƙasashen Yamma da suka haɗa da Joe Biden na Amurka, sun sa ran mutuwar Sinwar za ta kawo ƙarshen yaƙin, amma masu lura da al'amura na ganin damar cimma yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta da zaman lafiya kaɗan ce har yanzu, kasancewar dukkanin ɓangarori biyu da ke rikicin ba wanda ke da niyyar hakan.
Ƴan sa'o'i da Isra'ila ta tabbatar da labarin kisan jagoran na Hamas, Netanyahu ya fito fili ya bayyana cewa kisan babbar nasara ce amma kuma ya lashi takobin ci gaba da yaƙin.
Yaƙin ya ƙara tsanani a makonnin nan, inda a yanzu ya zarta kai hare-hare a Gaza da Isra'ila ta yi a baya.
Isra'ila ta faɗaɗa yaƙin, inda take mamayar kudancin Lebanon, lamarin da ya ƙara tayar da hankali a yankunan da ta mamaye a Gaɓar Yamma.
A nata ɓangaren, ƙungiyar Hezbollah ta lashi takobin ci gaba da yaƙar Isra'ila. Bugu da ƙari, Iran wadda ke taimaka wa ƙungiyar ta ce kisan Sinwar zai ma ƙara musu ƙwarin gwiwa ne a Gaza.

Asalin hoton, Getty Images
Waɗanda suka shirya harin 7 ga watan Oktoba
An yi amanna Sinwar, wanda ya kasance na farko cikin shugabannin Hamas da Isra'ila ta fi nema ruwa a jallo, na cikin manyan da suka kitsa harin ranar 7 ga watan Oktoba, wanda Hamas ta kai inda ta kashe wajen mutum 1,200 tare da garkuwa da mutum 251.
Farfesa Fawaz Gerges, malami a Jami'ar nazarin tattalin arziƙi da kimiyyar siyasa ta Landan ( London School of Economics and Political Science ) - LSE - ya gaya wa BBC cewa, shi yana ganin rashin yarda da kuma burin ɓangarorin da ke yaƙin su ne manyan abubuwan da ke ƙara ruru wutar rikicin.
Farfesan, wanda masani ne a fannin hulɗar ƙasashen duniya ya ce Firaministan Isra'ila ya bayyana aniyarsa ƙarara, bayan murnar kisan Yahya Sinwar, inda ya yi alƙawarin ci gaba da yaƙin saboda burinsa bai gama cika ba na murƙushe Hamas gaba ɗaya.

Asalin hoton, EPA
'Ba ƙarshen yaƙin Gaza ba kenan'
A wani hoton bidiyo da ya sanya a shafinsa na X, Netanyahu ya ce, "Yahya Sinwar ya mutu. ''Duk da cewa wannan ba shi ne ƙarshen yaƙin ba, to amma shi ne farkon ƙarshen.“
Farfesa Gerges ya ƙara da cewa," Abin da Netanyahu yake cewa a taƙaice shi ne, za a kawo ƙarshen yaƙin ne kawai idan Hamas ta daina gwagwarmaya da makamai. Wannan ya sa ƙungiyar ta Falasɗinawa -Hamas - ba ta da wani zaɓi illa ta ci gaba da yaƙi.”

Asalin hoton, EPA
‘Sauyin muradu da dama’
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mai bincike a cibiyar dabaru ta Isra'ila, (ICGS), Edy Cohen, ya bayyana ra'ayi na daban a kan babbar manufa a Gaza, inda ya ce burin Netanyahu ya nuna ƙarara cewa ba wai sakin mutanen da aka yi garkuwa da su ba ne kawai.
Firaministan na Isra'ila ya jaddada cewa ɗaya daga cikin manyan muradun shi ne , Hamas ba za ta sake mulkin Gaza ba, kuma ba wata ƙungiya da za ta sake iko da Gaza."
Cohen ya ce ya yi amanna cewa hanya ɗaya ta tabbatar da kawo ƙarshen rikicin ita ce a tabbatar ba wanda zai sake taka rawa nan gaba a Gaza - walau Hamas ko wani da zai gaji Sinwar.
Haka kuma ya jaddada muhimmancin riƙe iko da iyakar Zirin, musamman ma a tabbatar da hana satar shigar da makamai yankin.
Gerges ya ce, Netanyahu yana yaƙi ne a fage da dama, kamar yanda ake gani a Gaza da Gaɓar Yamma, da kuma kutse a Lebanon. "Haka kuma, yana neman shigo da Amurka da Birtaniya rikicin," in ji shi.
A jawabin da ya gabatar bayan isan Sinwar, Netanyahu ya ce, dama ce a garesu ta dakatar abin da ya kira matattarar miyagu, tare da samar da wata makoma ta daban - abin da yake nufi - Iran da ƙawayenta masu gwagwarmaya da makamai a faɗin Gaza da Lebanon da Syria da Iraqi da kuma Yemen.

Asalin hoton, Reuters
Abin da mutuwar Sinwar ke nufi ga waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza
Cohen ya nuna buƙatar mayar da hankali kan batun ceto waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza, inda ya ce Sinwar shi ne babbar matsalar, yarjejeniyar sakinsu.
Ya ce, "Isra'ila ba ta da wani buri a Gaza, amma muna da mutanen da aka yi garkuwa da su, da muke so a sako."
Ya bayyana ƙwarin gwiwarsa bayan kisan Sinwar, inda yake nuni da cewa mutuwarsa ka iya bayar da dama sosai a tattaunawar da za a yi nan gaba.

Asalin hoton, Getty Images
A watan Oktoba na 2023, a wata hira da aka yi da Netanyahu a tashar talabijin ta Amurka ta NBC, ya ce, “Idan ana son zaman lafiya, to dole ne a ga bayan Hamas. Idan kana son tsaro, ka kawar da Hamas. Idan kana son wanzuwar Isra'ila, da Falasɗinawa, da Gabas ta Tsakiya, to ka kawo ƙarshen Hamas.”
Netanyahu ya kafe cewa yana yin duk abin ya wajaba domin ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.
To amma duk da haka, a watan Agusta, Inbal Albini Peri - ƴar Chaim Peri, ɗaya daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su ta gaya wa BBC cewa, ko kaɗan ba ta yarda da maganar, Netanyahu ba, bayan da aka mayar da gawar mahaifinta daga Gaza.
Ta ce abin da suke son gani shi ne, gwamnati da Firaministansu su ci gaba da yarjejeniya, maimakon ci gaba da jefa rayuwar sojojinsu cikin haɗari, ana dawo musu da gawarwaki kawai.

Asalin hoton, Hostages' Families Forum
Tattaunawar dakatar da buɗe wuta a Gaza
Gerges ya ce babban burin Netanyahu shi ne sake fasalin siyasar yankin Gabas ta Tsakiya.
Ya ce wannan ne ma ya sa, kamar mutuwar Sinwar ta sa aka kawar da kai daga babban burin Netanyahu, a kan tattaunawar yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta a Gaza.
Ya ƙara da cewa wannan buri ya zarta ganin bayan Hamas, inda ya faɗaɗa har zuwa ga muradin murƙushe abokan ƙungiyar a Gaɓar Yamma, da Hezbollah, har ma dai a ƙarshe a kai ga Iran.
Yawanci ana ɗaukar Yahya Sinwar a matsayin wanda ya hana ruwa gudu a yarjejeniyar sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.
Babban mataimakin shugaban Cibiyar nazarin manufofi ta duniya (CIP), Matthew Duss, ya ce, idan dai har Sinwar shi ne babbar matsalar yarjejeniyar dakatar da buɗe wutar, to yanzu an kawar da wannan matsala.
A don haka masanin ya ce, wannan ya bai wa Amurka da ƙawayenta damar hana bazuwar rikicin zuwa gaba ɗaya yankin na Gabas ta Tsakiya.
Duss ya kuma ƙara tunda yawancin shugabannin Hamas a yanzu ba sa Gaza -suna Doha ne babban birnin Qatar, wannan zai sa a samu saukin cimma matsaya.
To amma ya yi gargaɗin cewa kafin a cimma wata yarjejeniya mai ɗorewa, dole ne a kawo ƙarshen yaƙi, amma ba buɗe wani sabon babi na hare-haren soji ba a Gaza.







