Hotunan aikin ceto a mahaƙar zinare ta DRC da ta rufta

..
Bayanan hoto, Aikin ceto na tafiyar hawainiya a mahaƙar zinare da ke garin Lomera na gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, sakamakon toshe hanya da ɓuraguzai da manyan duwatsu suka yi wa hanyar shiga wurin.
Lokacin karatu: Minti 2
..
Bayanan hoto, Ƴanjaridan yankin sun shaida wa BBC cewa masu aikin ceton na amfani da hannayensu da guduma da fartanya abin da ya sa suka gaza tono mutanen da suke maƙale a ɓaraguzan.
..
Bayanan hoto, Kawo yanzu dai aƙalla mutum shida ne aka ceto da ransu tun bayan ruftawar wurin a safiyar Lahadin da ta gabata.
..
Bayanan hoto, Ana samun rahotannin da ke karo da juna dangane da yawan mutanen da suka mutu.
..
Bayanan hoto, An ƙiyasta cewa akwai mutum kimanin 100 da ke aiki a ramuka aƙalla 15 lokacin da al'amarin ya faru.
Tuni ƙungiyar ta yi umarnin cewa a dakatar da ayyukan haƙar ma'adanan a wasu yankunan.
Bayanan hoto, Ƙungiyar mayaƙan M23 da ke iko da yankin sun ziyarci wurin da al'amrin ya faru amma ba su yi bayani ba dangane da yawan mutanen da suka mutu ba.