Liverpool za ta tsawaita kwantiragin Gravenberch, Arsenal na sha'awar Kubo

Asalin hoton, BBC Sport
Liverpool na shirin ba wa dan wasan tsakiyar Netherlands, Ryan Gravenberch, mai shekara 23 sabon kwantiragi na dogon zango.(talkSPORT, external)
Arsenal na sha'awar sayen dan wasan gaban Japan Takefusa Kubo, mai shekara 24 daga Real Sociedad a lokacin kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu.(Fichajes - in Spanish), external
An shaida wa Liverpool cewa ba za ta iya shawo kan Crystal Palace don ta sayar mata da dan wasan tsakiyar Ingila Adam Wharton, mai shekara 21, a kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu. (Teamtalk, external)
Kungiyar Barcelona ta cimma matsaya da dan wasan tsakiya na kasar Netherlands Frenkie de Jong mai shekaru 28, wanda ya amince ya tsawaita zamansa har zuwa shekarar 2029 kan albashin da aka rage. (Mundo Deportivo - in Spanish), external
Getafe na dab da sayen tsohon dan wasan Leeds United da Chelsea Patrick Bamford, mai shekara 32, wanda ba shi da kwantiragi da wata kungiya tun barinsa Leeds a bazara bayan ya shafe shekaru bakwai yana taka leda a kulob din.(Football Espana), external
An fadawa Arsenal da Liverpool cewa babu tabbas game da makomar dan wasan Brazil Vinicius Junior mai shekara 25 a Real Madrid. (TBR Football, external)
Kocin Fulham Marco Silva ya ce dan wasan tsakiya na Wales Harry Wilson, mai shekara 28, wanda Leeds ta so ta dauko lokacin bazara, zai tattauna kan tsawaita kwantiraginsa da su. (Sky Sports), external
Leeds na neman dan wasa mai kai hari da kuma dan wasa tsakiya a kasuwar musayar 'yan wasa ta watan Janairu. (Football Insider), external











