Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da suka ja hankali a fagen siyasar Najeriya a 2025
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
Fagen siyasar Najeriya, wani katafaren fili ne da koyaushe ke cike da abubuwa na siyasa da ke ɗaukar hankali da fukantar suka daga ƴanƙasar.
Siyasar Najeriya cike take da abubuwan na cece-kuce a kodayaushe, ba sai lallai lokacin zaɓukan ƙasar ba.
A cikin shekarar ta 2025 mai ƙarewa an samu abubuwa da dama da suka ɗauki hankali a fagen siyasar ƙasar.
Wasu daga cikin abubuwan sun sauya al'amuran siyasar ƙasar da kuma samar da sabbin al'amura a siyasar ƙasar.
Cikin wannan mujƙala mun yi waiwaye na abubuwan da suka ɗauki hankali a siyasar ƙasar.
Tururuwar shiga ADC
A farkon watan Yuli ne gamayyar wasu jiga-jigan ƴansiyasar Najeriya da ke hamayya da gwamnatin jam'iyyar APC suka amince da African Democratic Congress (ADC) a matsayin jama'iyar da za su ƙulla ƙawancen haɗaka a cikinta.
An cimma ƙawancen ne a taron haɗakar da aka gudanar a babban ɗakin taro na Ƴar'adua Centre da ke birnin Abuja.
Tuni dai haɗakar ƙawancen ta zaɓi wasu ƙusoshin tafiyar sabon ƙawancen domin su jagoranci sabuwar tafiyar.
Sabuwar haɗakar ta ADC ta kuma zaɓi Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ƙasar David Mark a matsayin shugaban jam'iyyar, wadda suka amince da ita a matsayin jam'iyyar haɗaka.
Samar da haɗakar ta sauya akalar siyasar Najeriya, inda a yanzu ake ganin jam'iyyar ADC cikin manyan jam'iyyun hamayyar ƙasar.
Ficewar Atiku daga PDP
Jim kaɗan bayan da gamayyar ƴan adawar Najeriyar suka sanar da dunƙulewa wuri guda domin ''kawar da jam'iyyar APC mai mulki'' sai Atiku Abubakar da ke cikin ƙawancen ya sanar da ficewarsa daga PDP.
A fanar 16 ga watan Yuli ne madugun adawar ƙasar, Atiku Abubakar ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.
A wata sanarwa da ya fitar mai kwanan watan ranar 14 ga watan Yulin 2025, Atiku Abubakar ya ce "ina sanar da jama'a ficewata daga jam'iyyar PDP ba tare da ɓata lokaci ba."
Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar ya ce "Dole ne na raba gari da jam'iyyar a yanzu bisa la'akari da yadda PDP ta sauka daga harsashinta na asali da muka fata domin shi.''
Sai dai a cikin watan Nuwamban shekarar Atiku Abubakar ya sanar da shiga jam'iyyar ADC a hukumace bayan ya yanki katin jam'iyyar a mazaɓarsa da ke Jada.
Ficewar gwamnonin PDP huɗu zuwa APC
A cikin shekarar mai ƙarewa ce, wasu gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar.
Wannan al'amari ya sauya akalar siyasar Najeriya, inda jam'iyyar APC mai mulki ta ƙara samun ƙarfi a fagen siyasar ƙasar.
Wani abu da ya ja hankali game da sauya sheƙar shi ne yadda gwamnonin yankin kudancin ƙasar da a baya PDP ke da ƙarfi ne kan gaba a masu sauya sheƙar.
Gwamnonin PDP da suka koma APCn sun haɗa da na Akwa Ibom Umo Eno da gwamnonin Bayelsa da Enugu da kuma gwamnan jihar Taraba, Kepas Agbu.
Zaɓen sabon shugaban PDP
A ranar 16 ga watan Nuwamban shekarar ne kuma babbar jam'iyyar hamayyar ƙasar , PDP ta sanar da zaɓen sabon shugabanta na ƙasa.
Jam'iyar ta zaɓi Kabiru Tanimu Turaki SAN, a matsayin sabon shugabanta a babban taronta na ƙasa da ta gudanar a birnin Ibadan na jihar Oyo.
PDP ta ce Barista Kabiru Tanimu Turaki, ya yi nasarar ce akan sanata Lado Ɗan Marke da ƙuri'u sama da dubu ɗaya da ɗari biyar, da wakilai 3, 131 suka halarta.
Zaɓen sabon shugaban ya kawo ƙarshen shugabancin riƙo da Amb. Iliya Damagum ke yi wa jam'iyyar tun bayan sauke Iyorchia Ayu a 2023.
Zaɓen Kabiru Turaki - wanda tsohon minista ne - ya kasance mai cike ta taƙaddama, inda wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar suka nuna adawa da zaɓen.
Zaɓen nasa na ne a daidai lokacin da jam'iyyar ke tsaka da rikicin cikin gida da ruruwar ficewa mambobinta zuwa wasu jam'iyyun.
Rinjayen APC a majalisar dokoki
A ƙarshen watan Oktoban shekarar ne kuma jam'iyyar APC mai mulki ta samu rinjayen kashi 2 bisa uku na mambobin majalisar wakilan Najeriya.
Wani al'amari da zai iya bai wa jam'iyyar damar zartar da duk wani ƙudiri ko dokar da jam'iyyar ke muradi ba tare da samun tangarɗa a majalisar ba.
Jam'iyyar ta samu irin wannan nasara a majalisar dattawan ƙasar cikin tsakiyar shekarar.
Hakan na zuwa sakamakon irin sauya sheƙar da wasu mambobin majalisun biyu ke daga jam'iyyun hamayya zuwa jam'iyyar mai mulki.
Dakatar da Sanata Natasha
A farkon watan Maris ne Majalisar Dattawan Najeriya ta ɗauki matakin dakatar da ƴarmajalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga majalisar har natsawon wata shida.
Majalisar ta ɗauki matakin ne bayan shawarwarin kwamitin Ɗa'a da Ladabtarwa da Sauraron ƙorafin Jama'a na majalisar ya bayar, bayan nazari kan ƙorafin da sanata Natasha ta miƙa wa majalisar game da shugabanta Sanata Godswill Akpabio.
Sanatar ta shiga rikici da shugaban majalisar ne bayan da ta wata rigima ta shiga tsakaninsu, har ta kai ga ta zarge shi da yunƙurin cin zarafinta.
Wannan al'amari na daga cikin manyan batutuwan siyasa da suka ɗauki hankali a fagen siyasar ƙasar cikin shekarar mai ƙarewa.
Bayan dakatar da sanatar ta shigar da ƙara domin ƙalubalantar matakin, kodayake ba ta yi nasara ba.
To sai dai ƴarmajalisar ta koma zauren majalisar bayan cikar wa'adin a farkon watan Oktoban shekarar.
Dokar ta-ɓaci a jihar Rivers
A ranar 18 ga watan Maris ɗin shekarar ne kuma, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi tare da kuma da naɗa wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar na tsawon wata shida.
Tinubu ya sanar da matakin ne a wani jawabi da ya yi ta kafafen talabijin na ƙasar da yammacin ranar Talata.
A cikin jawabin nasa, Tinubu ya yi nuni da yadda aka rushe ginin majalisar dokokin jihar watanni 18 da suka gabata, wadda aka kasa sake gina ta har zuwa wannan lokaci.
Tinubu ya bayyana a lokacin cewa ya yi bakin ƙoƙarinsa wajen ganin yadda za a magance matsalar to amma ya ce duka ɓangarorin sun yi watsi da yunƙurin nasa.
Hakan na zuwa ne bayan rikicin siyasa da jihar ta shiga tsakanin gwamnan jihar Similanayi Fubara da ministan Abuja, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.
To sai dai bayan dokar ta-ɓacin ɓangarorin biyu sun sasanta da juna bayan shiga tsakani daga masu ruwa da tsaki.
A tsakiyar watan Satumba ne kuma aka mayar da Gwamna Fubara kan karagar mulkin, bayan ƙarewar wa'adin dokar.
Naɗa sabon shugaban INEC
A shekarar mai ƙarewar ne aka naɗa sabon shugaban hukumar zaɓen ƙasar, INEC, wanda ke kula da shirya manyan zaɓukan ƙasar.
A ranar Alhamis ne 23 ga watan Oktoba ne Shugaba Tinubu ya rantsar da Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar domin maye gurbin Farfesa Mahmud Yakubu - wanda wa'adinsa ya ƙare.
Sauyi a shugabancin hukumar zaɓen ƙasar abu ne da ya ɗauki hankalin ƴansiyasar ƙasar, kasancewar shi ne mutumin da zai jagoranci ɗaya daga cikin ginshiƙan hukumomi a tsarin dimokraɗkiyyar ƙasar.
Farfesa Joash Amupitan zai jagoranci hukumar zaɓen ƙasdar har na tsawon shekara biyar, bisa tanadin kundin tsarin mulkin ƙasar.