Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace jam'iyya ce za ta iya ja da APC da ke ƙara ƙarfi a Najeriya?
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya na ci gaba da mamaya, tana janye manyan ƴan siyasar ƙasar zuwa cikinta.
A cikin makon nan kaɗai gwamnoni biyu daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP ne suka sauya sheƙa zuwa cikin APC.
Hakan na zuwa ne yayin da babban zaɓen Najeriya na 2027 ke ƙara matsowa, kuma harkokin siyasa ke ƙara zafi.
A yanzu jam'iyyar APC mai mulki na iko da jihohi 24 daga cikin jihohi 36 na ƙasar.
A ɓangare ɗaya jam'iyyar PDP wadda a ƙarshen zaɓen 2013 ke iko da jihohi 11, ta koma a yanzu tana da gwamnoni takwas ne kacal.
Jam'iyyar LP na da jiha ɗaya, NNPP na da ɗaya sai kuma APGA, wadda ita ma take da jiha ɗaya.
A ranar Talata ne gwamnan jihar Enugu Peter Mbah ya bayyana ficewarsa daga PDP tare da bayyana komawarsa jam'iyyar APC, inda ya ce ya yi hakan ne domin ganin ana damawa da jihar a matakin tarayya.
Ƙasa da kwana ɗaya bayan hakan ne gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri shi ma ya fice daga jam'iyyar PDP.
Cikin wata sanarwar da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Daniel Alabrah ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce gwamnan ya fice daga PDP ne tare da ƴan majalisar dokokin jihar 19, ciki har da kakakin majalisar.
Tururuwar gwamnoni zuwa APC
Tun bayan zaɓen 2023, an ga yadda gwamnonin adawa, musamman na jam'iyyar PDP suka riƙa turuwar komawa APC.
A 2023 bayan rantsar da shugaban Najeriya Bola Tinubu, gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori ya buɗe fagen sauya sheƙa ga gwamnoni, inda ya ba kowa mamaki lokacin da ya koma jam'iyyar APC mai mulki, lamarin da ya kawo ƙarshen kakagidan da PDPn ta yi a jihar tun daga shekarar 1999.
Inda daga baya saura suka bi sahu.
A yanzu sauran gwamnaonin jam'iyyar adawa da suka rage a Najeriya su ne:
- Abia - Alex Otti (LP)
- Adamawa – Ahmadu Fintiri (PDP)
- Anambra - Charles Soludo (APGA)
- Bauchi – Bala Mohammed (PDP)
- Kano - Abba Kabir (NNPP)
- Plateau – Caleb Mutfwang (PDP)
- Taraba – Agbu Kefas (PDP)
- Zamfara – Dauda Lawal (PDP)
- Oyo – Seyi Makinde (PDP)
- Rivers – Siminalayi Fubara (PDP)
- Osun – Ademola Adeleke (PDP)
Komawar ƴan majalisa APC
Baya ga gwamnoni, a majalisar dokokin Najeriyar ma abin haka yake, inda ƴan majalisa na jam'iyyar adawa ke ci gaba da sauya sheƙa zuwa jam'iyar APC mai mulki.
Ko a cikin wannan mako ƴanmajalisar wakilai uku daga jihar Kaduna sun sauya sheƙa zuwa APC.
Ƴanmajalisar su ne Hussaini Ahmed daga Kaduna ta kudu da Aliyu Abdullahi daga Ikara da Kubau, sai kuma Sadiq Ango Abdullahi daga Sabon Gari.
A majalisar dattijai ma an samu Sama'ila Kaila daga Bauchi, wanda shi ma ya koma jam'iyyar ta APC daga PDP.
Gabanin haka akwai wasu manyan ƴan majalisar da suka sauya sheƙa daga jam'iyyun adawa zuwa jam'iyyar APC.
Wasu daga cikinsu su ne:
- Sanata Abdulrahaman Kawu Sumaila (Kano) - NNPP zuwa APC
- Yusuf Galambi (Jigawa) NNPP zuwa APC
- Aliyu Wadada (Nasarawa) - SDP zuwa APC Nasarawa
- Kabiru Alhassan Rurum (Kano) - NNPP zuwa APC
- Abdullahi Sani Rogo (APC) - NNPP zuwa APC
- Abdullahi Balarabe (Katsina) - PDP zuwa APC
- Abubakar Aliyu (Katsina) - PDP zuwa APC
- Yusuf Majigiri (Katsina) - PDP zuwa APC
- Abdumumin Jibril (Kano) - NNPP zuwa...
Rinjayen kashi biyu bisa uku
A halin yanzu jam'iyyar ta APC ta samu kashi biyu cikin uku na ƴan majalisar dattijan Najeriya, wani abu da ya ba ta isasshen rinjayen amincewa da kowane ƙuduri da aka gabatar a zauren majalisar, idan tana so.
Bayan komawar sanata Sama'ila Kaila daga Bauchi a ranar Talata, alƙaluma na nuna cewa APC na da ƴan majalisar dattijai 73 daga cikin 109.
Wannan ne karo na farko da jam'iyyar APC ta samu irin wannan nasara tun bayan karɓar mulki a shekara ta 2015.
A baya jam'iyyu na yin kusan raba-daidai ne na kujerun majalisa, sai dai kuma wani lokaci da aka samu rinjaye amma ba mai yawa na azo a gani ba.
A Majalisar wakilai ma jam'iyyar ta APC na gab da samun rinjayen kashi biyu bisa uku na ƴan majalisar, kasancewar a halin yanzu tana da kimanin wakilai 236 daga cikin 360.
Me ya sa ƴan siyasa ke komawa APC?
Jam'iyyun adawar Najeriya na zargin jam'iyyar APC mai mulki da amfani da barzana wajen janyo hankalin ƴan siyasa zuwa cikinta, ko kuma ta hanyar shafa musu zuma a baki.
Haka nan jam'iyyun sun zargi APC da yunƙurin mayar da ƙasar bisa tsarin jam'iyya ɗaya, sai dai jam'iyyar mai mulki ta sha musanta zarge-zargen.
A wata tattaunawa da BBC, Malam Kabiru Sufi masanin kimiyyar siyasa a Najeriya ya ce sauya sheƙar da abokan hamayya ke yi zuwa jam'iyya mai mulki ba zai rasa nasaba da yadda shugaba Tinubu ke amfani da gwamnonin jihohi na jam'iyyarsa wajen zawarcin ƴan majalisar tarayya daga jihar zuwa jam'iyyar APC.
Bugu da ƙari, ana yi wa Tinubu kallon gogaggen ɗan siyasa wanda ka iya haɗa kai da manyan ƴan siyasar jiha ko yanki domin ribato gaggan ƴan siyasar yanki da ke ɓangaren hamayya.
Ya kuma ce shugaban ƙasar na yi wa ƴan siyasa alƙawuran ayyukan da za su samar da ci gaba a yankunansu.
A wani ɓangaren kuma ana zargin gwamnatin ta APC da yi wa ƴan siyasa masu hamayya alƙawarin takara a mazaɓunsu da kuma muƙamai da ma samun damar yin walwala a zauren majalisa.